a Afaf aiki haka zata tashi tayi ko bata so kuma Mustaphan ya daina hanata.
PAGE 194
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Sun gama magana da ita a kan zai siya mata mota, amma gashi lokaci yana ta kurewa yanzu ya ma ce mata shi ba alkawari yayi mata ba; shi kawai ce mata yayi zai yi tunani.
Cikin damuwa suke waya ta sanar da Anti Wiyya halin da ake ciki; tace ‘Wallahi Anti nema yake ya canza maganar. Kuma dama na gaya miki aikin malamin nan ba kullum yake ci ba, tunda ko Mustaphan ya fara saurarar maganata da an kwana biyu sai ya sake komawa kamar da. Gani ma nake kamar duk lokacin da matarsa ta karbi kwana sai ta warware min aiki, shi yasa nake ta fama da shi.’
Daga daya bangaren Anti Wiyya tace ‘Au haka ne? To barni da su, ai ba mu za a yiwa bariki ba. Akwai wani malamin aikinsa yana da zafi sosai, in kin sami lokaci kiyi min waya sai muje wajensa. Ke kanki sai kin yi mamakin aikinsa.’
Suka karasa hirarrakinsu sukayi sallama. Ta jefa wayarta a kan gadonta cike da kwarin gwiwa; ta san Mustapha yana kokari wajen kyautata mata amma ita gani take kamar tsoron khadeeja yake yi. Kuma ma ita so take ya zama gaba daya gidan sai abinda ta fada za ayi. Tana ganin yanda maza suke yiwa matansu kyauta ta burgewa, itama haka take so ya dinga yi mata, duk abinda ta nema ya bata kawai tunda ta san yana da kudin. Idan ma ta sami yanda take so to ko ganin Mustapha yaran basu isa suyi ba sai da izininta, domin ta kula da yanda yake saurararsu yana bin ra’ayinsu kamar su suka haifeshi. Sai an yi magana yace su marayu ne. Tabbas dole gidan nan gaba daya ya dawo tafin kafarta don ta gaji da wannan mulkin da ake mata ana kasa mata hankalin miji tsakanin uwargidansa da yaransa.
………
Kwanci tashi sai da Khadeeja ta kwashe shekaru biyu tana aiki a gidan rediyon nan a matakin internship sannan aka sami gurbi aka dauketa cikakken aiki, aka saka mata albashinta Naira dubu saba’in.
Ba karamin dadi ta ji ba da samun wannan ci gaban domin tun da ta fara service ya zama wasu hidimomin nata ita take yiwa kanta kamar kayan shafe-shafe, turare wani lokacin ma har da sutura. Bata sani ba ko haka yake yiwa Najan ma tunda itama tana da albashi ko kuma ita kadai yake yiwa hakan.
PAGE 195
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Sai dai bata da lokacin da zata bincika ko kuma ta tambaya don haka take rayuwarta yanda taga zata iya.
Afaf ta shiga Jami’ar Bayero ta Kano inda take karantar Computer Science yayinda Habib yake SS3 yayinda Nasreen take JSS3 ita kuma Shukra tana primary 5.
Zuwa yanzu duk bakon da yayi kwana daya a gidan zai gane cewa gidan ya kasu kashi biyu; Shukra da Halifa wadanda su ‘yan dakin Khadeeja ne da kuma Afaf da Nasreen wadanda su ‘yan dakin Naja ne. ko a wajen tarbiyya ‘yayan dakin Khadeeja sun fita da ban da ‘yayan dakin Naja. Domin ita Khadeeja tarbiyyar take basu da kulawa saboda Allah kamar yanda take yiwa Hammad, ita kuma Naja hankalinta yana kan yanda zata kwace gida ta mallake maigidan don haka duk abinda zai saka shi farin ciki shi da yaransa shi take yi; ko da kuwa abun ba daidai bane.
Lokuta da dama idan taje wajen malamanta tana samu ta fara juya Mustapha, sai dai abun bai fiya dadewa ba. Da zarar ta fara samun yanda take so sai kuma ta sake rasa kan maigidan nata. Tayi iya bakin kokarinta ganin ta inda zata samu ta hadashi fada da Afafa amma ta gagara; saboda son da yake yiwa Afaf ba kadan bane. Kuma kusan duk wani abu da zai yi to da Afaf yake shawara. Haka aka yi a farkon shekarar nan da zai canza mota; da kansa yake fada Afaf ce ta zabar masa motar bayan ita bata ma san zai canza motar ba sai da aka kawo motar gidan. Haka kuma aka yi da zai canza fentin gidan; Afaf ce ta zabi wanda take so aka yi, sai daga baya matan gidan suka ji labari.
Lokuta da dama Naja ta so su hade kai da Khadeeja ko da su samu su kwaci Mustapha daga hannun ‘yayan ne, amma bata sami hadin kai ba. Domin har yanzu zaman nasu dai babu yabo babu fallasa. Shi yasa ma Najan takewa Khadeeja kallon bata san me take yi ba saboda yanda ta bari yara suke controlling miji.
Ita kuwa Khadeeja bata taba daukan alakarsa da yaransa a matsayin matsalarta ba, matsalarta daya da shi rashin adalcin da yake nuna mata tsakaninta da Naja. Idan dai abun a nuna kulawa ne da kauna to Naja yake nunawa, amma idan abu ne wnda za ayi masa hidima shi da yaransa to sai yace a kaiwa Khadeeja.
PAGE 196
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Duk wani kokari da zata yi ta ga ya nuna mata so da kauna tayi amma abun ya ci tura; har ta gaji ta zuba masa ido. Lokuta da dama idan tayi magana sai dai ya dinga kokarin nuna mata cewa ya fi sonta kuma ya fi trusting dinta shi yasa yake saka ta hidimarsa da ta yaransa. Ta gaji da jin wannan tatsuniyar shi yasa ma ta hakura ta daina korafi; kawai dai duk abinda zata yi zata yi, abinda ba zata yi ba kuma haka zata zuba masa ido ya karaci barazanarsa amma bata yi.
Haka rayuwarsu ta c