NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 81 of 105

shi yayi ta faman yi musu fada har ya samu su gama shiryawa a hankali. Afaf ce ita kadai a parlor din Naja tana kallo saboda TV din parlor dinsu Startimes ce ita kuma ta fi son DSTV wadda take parlor din Naja; yayinda Anti Wiyya take ta kaiwa da kawowa tana kokarin dora a bincin rana. Ta wuce Afaf a parlor ta shige dakin Naja inda ta sameta a kwance a gefen gado; bayan ta amsa sallamarta ta karasa ta zauna a gefen karata kamar a fusace. Tace ‘Sannu Anti, kina ta hidima. Lallabata nakeyi idan ta koshi goyata zan yi na fito na tayaki. Salaman ma ina jin yau ba zata zo ba; ko wa take so yayi mana wanke-wanke da sharar oho ga girki.’ Tayi tsaki ta kawar da kai tace ‘Kin ganni a cike nake da haushinta, gashi kamar ta shirya wulakanci tunda yau wanke-wanken ya fi na kullum yawa sannan taki zuwa.’ ‘Hmm! Ai sai hakuri masu aikin zuwa da dawowa basu da kirki, nima da na gama jegon nan me kwanan zan dauka.’ PAGE 192 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Suka yi shiru na dan lokaci, jimawa kadan Anti Wiyya tace ‘Ita kuma wannan ‘yar taki wallahi itama bata da mutunci; yaushe za ace budurwa kamarta ba zata yi aiki ba komai kankantarsa? Sai ai ta dinga bin mutane da kallo suna mata aiki sai kace ubanta sayenmu yayi. Gaskiya ku sake zama a gidan nan, haba! Idan banda ma rashin mutunci ya za ace mace tana jego kuma a barta da kula da gida da yara bayan tana da kishiya? Ai kamata yayi ta karbar miki aikin. Ko da yake wannan ‘yar mulkin kishiyar taki na kula daga ke har maigidan tsoronta kuke yi.’ Ta tashi zaune ta kwantar da Rukayya wadda ta riga ta yi bacci, ta kama haba ta dubi Antin tata tace ‘A’a shi dai yake tsoron matarsa, duk abinda ta ga dama tace ba zata yi ba haka zai yi ta kame-kame saboda ita ba a iya yi mata dole.’ Ta kalleta shekeke tana cewa ‘Kece karkatacciyar kukarsa mai dadin hawa ko? Shi yasa kina jego amma aka lafta miki aiki? Ita ko kunya bata ji? Sai ta sauko ta ishi mutane da gaishe-gaishe kamar wata musulmar ta kwarai.’ Cikin damuwa tace ‘Haka take fa, da an hadu tayi ta haba-haba da mutum amma mugun halinta yana nan fal cikinta sai mu da muke zaune da ita muka san halinta.’ Anti Wiyya ta dan yi kasa da muryarta tace ‘To gaskiya dai dole ayi aiki a kan wannan matar, yanda ta kama maigidan nan tana juya shi ai ba fin mu iyawa tayi ba. Kema idan kika zo yawon arba’in da kaina zan kai ki inda za a taimaka miki a kwato miki daraja. Wannan kwarjinin da take dashi take yiwa kowa har maigidan kema a samo miki shi. Taimako ne da ayar Allah ina da malamina a hannu kudi kawai zaki bayar. Har yaran ma don ubansu ko su biki su zauna lafiya ko kuma su koma ‘yan kallo.’ Tana ta jijjiga kai saboda gamsuwa tana cewa ‘Babu komai Anti, in sha Allahu zamu je. Don nima wallahi zaman haka ya isheni. Kuma dama Yaya ma tace zamu je ban san me ya dauki hankalinta ba.’ Nan suka zauna suka gama kulla yanda za ayi sannan suka fito suka kama hidimar gidan. PAGE 193 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Haka suka cigaba da yi har Naja tayi arba’in; duk wata kalma da Mustapha zai yi amfani da ita ya sa Khadeeja ta karbi hidimar nan bata yi amfani ba har ya gaji ya sakawa sarautar Allah ido. Sai da Naja tayi arba’in sanna suka cigaba da rabon kwana. idan Khadeeja ce da kwana sai Mustaphan yaje dakinta yayinda ita kuma Naja take zuwa dakinsa. Kwanci tashi har ya zama ta mayar da saman nasa kamar nata, ya zama kullum tana ciki ko parlor dinsa ko dakinsa. Bata dade da yin arba’in din ba kuma Khadeeja ta gama bautar kasa; sai dai duk yanda ita da Baffanta suke kokarin samar mata aiki bai samu ba. Inda tayi bautar kasar ma ta so su riketa amma suka nuna mata basa bukatar ma’aikata. Bata son zaman gidanta, domin ta san in dai ya zama Naja zata tafi aiki ta barta a gidan da yara to dole Mustapha zai yi duk yanda zai yi ya tursasa ta ta dinga kula da yara. Ya zama shi da matarsa sun yawon neman kudi ita tana musu hidimar gida da ta yara. Don haka ta sanar da manager zata dinga zuwa litinin zuwa juma’a tana yi musu aiki kyauta. Da yaji haka sai ya sa aka dorata a kan tsarin internship da suke da shi; inda duk wata za a dinga bata naira dubu goma sha biyar har zuwa lokacin da za a sami wani gurbi a gidan rediyon kawai sai a dauketa. Sosai hakan yayi mata dadi, kuma ba tare da wata fargaba ba ta sanarwa Mustapha sun riketa aiki, ta cigaba da zuwa. Kusan wata takwas kenan da haihuwar da naja tayi; kuma kamar yanda suka tsara an kaita wajen malami. Bayan malamin ya ji bayaninsu ya bata wani abu mai kama da gishiri yace tayi sati tana zuba musu a abnci duk gidan kowa yaci har Khadeeja. Haka ta dage tayi amfani da abun nan sai dai bata da tabbcin Khadeeja ta ci abun marmarin da take girkawa tana aika mata, shima Habib bata da tabbacin cinsa domin ya fi cin abinci a wajen Khadeeja. A hankali ta fara ganin sauyi, kamar dai duk yaran da Mustaphan suna saurararta; tunda wasu lokutan idan ta s
🏠