ce ba zata bada kwananta ba, ta fi yarda shine di ba zai iya bata kwana arba’in ba ba tare da ya ji dumin rabin ransa ba. Ta daure tayi murmushin yake sannan tace ‘Allah sarki hakane kam, to babu damuwa Allah ya raya mana Rukayya ita kuma mai jego Allah ya kara mata lafiya. Shikenan ai tunda ta haihu lafiya idan ta karbi kwana yau to ta hada da sauran hidimar gida da yara da nakeyi nima na samu na huta.’
PAGE 189
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Yayi shiru da bakinsa a bude yana kallon Khadeejan ta cikin mudubi; to a gaban Antin tata zai sakar mata aikin gida da na yara bayan ga danyen jego sannan kuma ga Khadeejan tana kallo? Kuma ace ita ce zata tashi ta shirya masa yara, duk da dai kusan sun iya shirya kansu amma dai idan ba a tsaya a kansu ba haka zasuyi ta shiririta har su makara. Gashi Afaf ta shiga SS 3 yanzu tun 7:15 am ake tare su makara. Ya san idan dai ba a tsaya a kansu ba to kullum sai dai ya dawo da Afaf. Ya rasa ma me zai ce mata, domin ya san kusan ko me yace tana da amsar bashi kuma ya tabbatar fitnar da bata yi bace a lokacin da Baffanta yace ta dinga taya Naja aiki take shirin biyan bashinta yanzu.
Ta mike ta kwashi mayukanta da ta gama shafawa ta karasa gaban mudubin ta ajiye. Ta dan tsaya daga gefensa tana kallonshi fuskarta cike da walwala kamar ba yanzu ta hadiye bacin rai ba, tace ‘Kuma ni na yafe nawa kwanan ka hada mata, idan kuka yi arba’in sai mu cigaba da rabon. Ka ga ita da Baby suna bukatar lokacinka da kulawarka sosai a wadannan kwanakin.’
Ta wuce ta nufi gaban wardrobe domin saka kaya.
PAGE 190
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Yana nan zaune a gaban mudubin ta shirya ta fice ta barshi a dakin; nan da nan ta hada masa breakfast ta jera a kan table sannan ta dawo dakin ta sameshi ya riga ya gama saka kaya. Tana tsaye daga bakin kofa tace ‘Na yi serving breakfast.’
‘Ok.’ Ya amsa.
Ta juya ta fice ya biyo bayanta.
Suka zauna tare suna cin abincin. Har suka ci kusan rabin abincin babu wanda yace wani abu; kowa da abinda yake ransa. Ya ajiye kofin shayinsa bayan da ya kurba sannan ya dauki fork dinsa ya tsikari dankalin baturen da yake gabansa, ya dan ajiye fork din ya kirawo sunanta a hankali kamar ma baya so ta ji kiran. Ta daga kanta daga kallon kwanon abincinta ta amsa tana kallonsa. Yayi gyaran murya sannan yace ‘Um, da-Allah kiyi hakuri ki cigaba da girki akalla har zuwa lokacin da Antin Naja zata gama yi mata wanka ta tafi, tunda kinga ga Hafsa nan tana taimaka miki kuma na san Afaf din ma yanzu duk abinda kika gwada mata zata iya tayaki da shi.’
Saura kadan dariya ta kwace mata; wato yanzu Afaf ta kai ta taimaka wajen girki kenan tunda ya auro matar so? Ashe ma ya san kunya tunda ga shi baya so yaji kunyar iyayen Naja. Ta ajiye cokalinta ta kurbi shayinta sannan tace ‘Don Allah Abban Afaf mu bar wannan maganar, hidimar gidannan ta wata takwas na karbar mata. Ai nayi ko? Yanzu sai ta cigaba daga inda ta tsaya. Kwanan kuma da nace na bata da gaske nake, kuje kuyi jegonku na masoya kwana arba’in; watakila dai a kwankin da suka kama nawane na yi aikin gidan idan ina nan in ya so ita sai ta kwana da angonta.’
Cike da jin zafin abinda ta fada yace ‘Khadeeja ni kike gayawa wannan maganar?’
A cikin abinda ta fada bata san menene ya bata masa rai haka ba tunda ita dai a iya saninta ba rashin kunya tayi masa ba, amma ta ga ya fusata yana faman yi mata muzurai. Ita da ya kamata ace itace ranta ya baci haka saboda nauye-nauyen da yake nema ya dora mata wadanda karara suke nuna rashin adalci.
Ta kalleshi ta kawar da kai tace ‘Allah ya baka hakuri.’
Ta kurbe ragowar shayinta ta mike da kofin da kwanonta ta wuce kitchen.
PAGE 191
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Tana ajiye kwanukan ta fito ta wuce dakinta, tana turo kofar dakin hawayen da take rikewa suka kwace mata, ta karasa ta zauna a kan kujerar gaban mudubi. Ta zubawa mudubin ido tana kallon yanda hawaye suke fita daga idanuwanta suna gangarewa ta kan kumatunta. Wai me Mustapha ya dauketa ne? mai aikin Naja? To da me yasa ya aureta ne? ko dama haka ake soyayya?
Bata sami amsar tambayoyinta ba karar fitar motarsa daga gidan ta katse mta tunani, ta tuna itama aiki zata tafi. Don haka ta mike ta wanke fuskarta ta karasa shiryawa ta fice daga gidan zuciyarta cike da damuwa.
……..
Kamar yanda Khadeeja ta fada bata sake kula hidimar yaran a ranar da ba itace da kwana ba, sai dai ranar kwanata tana fitowa ta sallami kowa sanna ta cigaba da harkarta. Idan kuma dare yayi ta shiga dakinta tayi kwanciyarta don ta tabbatarwa Mustapha cewa ta bashi kwanan.
……..
Ranar asabar ce don haka yara babu makaranta duk suna gida, kamar yanda suka saba tunda Khadeeja taki hidimar yaran to duk ranar girkin Naja Anti Wiyya ce take abinci har yaran. Ita kuma Najan itace zata tsaya a kansu suyi wanka su shirya, sai dai ranar da bata tashi ba dole haka Mustaphan yake ta