nu da zuwa ya dubi Mommy tana zaune a tsakiyar su Khadeeja yace ‘Gulmar wa kuke yi suka saka ki a tsakiya haka.’
Itama dariyar tayi tace ‘Ba dai gulmarka muke yi ba.’
Yaya Mama tayi musu sallama ta fice yayinda Khadeeja ta mike ta nufi dakin Mommy ba tare da tace komai ba.
Baffa ya bi bayanta da kallo sannan yayi dariya ya dubi Mommy yace ‘Wannan iya rigimar karata ta kawo ko?’
Ta harareshi tace ‘Ashe ka san kayi mata laifi?’
Yayi dariya yace ‘Rabu da ita da-Allah, ya za ayi ace mutum yana da mata biyu ace daya ba zata karbi daya aiki ba idan bata da lafiya? Ai itama bata so a zauna lafiya ba.’
Nan ta kara yi masa bayanin yanda zaman nasu yake, sai dai ta kasa gaya masa cewa Mustaphan yana bawa Naja kwanan Khadeeja saboda Khadeejan bata yarda taje dakinsa. Yanda ta san shi ta san tabbas ba zai dauki wanna ba, tunda shima tashi uwar har ta koma ga Allah turaka take zuwa ranar kwananta.
………
Haka dole Khadeeja ta hakura ta cigaba da hidimar gida da ta yara.
Shima Mustapha da ya gama zagaye-zagayen haka ya sameta a dakinta yana nuna mata jin dadinsa ganin yanda take kula da yaran sai dai baya jin dadin yanda idan ta jera abinci take komawa daki ta barsu shi da ‘yayansa.
PAGE 187
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Duk yanda ya so ta bashi hadin kai su tattauna maganar ta ki, da ya dameta da zance ma sai tace ‘Don Allah ka bari! Kai dai ba so kake na cigaba da hidimar gidanka da yaranka ba amaryarka tana hutawa? To ai ina yi ko? Ina ga duk a inda na zauna naci abinci ma wannan bai kamata ya zama damuwa ba tunda dai ku kun ci naku.’
Kafin ya bata amsa ta fice ta bar masa dakin. Dole ya hakura ya zuba mata ido tunda dai tana yin abinda yake so kuma duk ranar da ya kai mata kwananta bata hanashi bukatarsa.
000000
Da fari lokacin da Mustapha ya kara aure Khadeeja taga ‘yan uwansa basa wani damunta tayi zaton tunda an mata kishiya sun fita harkarta. Sai dai tunda suka ji labarin Naja tana da ciki sai suka kama zarya gidan; babu yanda za ayi Yaya Jidda tayi sati bata zo gidan ba. Haka zata taho da girki a flask wai Hajia ce tace a kawowa Naja saboda kwadayin mai ciki. Gashi idan ta zo a wajen Najan zata sauka, sai dai idan Khadeejan tana nan ta shiga su gaisa sai ta koma wajen Najan. Sai kuma tayi ta aiko yara; a bata abinci. Idan ta cinye kuma tace a bata wani dan abun tabawa. Ranar da bata zo ba kuma sai a turo yaranta da abincin; haka zasu zo ta wuni surutu da hidima da su bata taba jin wani yace Hajia tana gaishwta ba. Kuma shima Mustaphan kuma yana kallo ana yi amma bai taba cewa komai ba; sai dai yawan godiya da zata ji shi yana yiwa mutan gidan nasu.
Haka ta kawar da kai ta cigaba da duk wannan hidimar tana ganin rawar kai kala-kala.
Haka ta cigaba da dagewa har Allah ya sauki Naja lafiya, aka sami yarinya mace wadda tun ranar da aka haihu Mustapha yayi mata huduba da suna Rukayya.
Basu tsara zata tafi gida ba don haka sai aka kawo kanwar mahaifiyarta Alawiyya waddad suke kira da Anti Wiyya ta zo yi mata zaman dabaro.
Tun Khadeeja tana saka ran zata ji Mustapha yace zai hade mata kwanan saboda Naja tana jego har dai ta fitar da rai.
Ranar da aka kwana takwas da haihuwa ranar ta kama kwanan khadeeja ne sai dai a daren ranar zata fita daga girki.
PAGE 188
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Da yake a dakinta suka kwana a nan yake shirin fita office; musamman tunda bandakin dakinsa ya kwana biyu rabon da a wanke saboda Naja ba zata iya wankewa ba kuma Khadeeja ta ki ma shiga dakin; gashi kuma yana kyashin ya saka Afaf ta wanke tunda baya son damuwarta.
Yana zaune a gaban mudubinta yana shafa mai ta fito daga wanka, ta dauki kayan shafawarta ta koma gefen gado, suna yi suna taba hira.
Jimawa kadan tace ‘Yauwa, tazarce zamu yi ko? Sai na hade kwanakin tunda Naja tana jego har zuwa tayi arba’in ko?’
Ya dan yi dum, alamar maganar ta shammaceshi; tun ranar da Naja ta haihu ta gaya masa ba zata bayar da kwanata ba saboda ko ba zata iya biya masa bukatarsa ba tana so ya kwana da su ita da Baby, in ya so kwana biyu sai su hakura. Ya riga ya amsa mata hakan domin shi ma hakan yayi masa; duk da dai shi ba mutum ne mai son jarirai ba domin ko daukan yaro baya son yi har sai yaro ya iya zama sosai. To amma dai tunda ta nuna tana so shima sai ya ji hakan yayi masa ko hira ce sa yi, musamman da yake bai taba tsammanin Khadeeja zata nemi wani karin kwana ba duk da ita ta bada nata kwanan an bawa Najan.
‘Um, no ina ga ba haka za ayi ba. Na riga nayi magana da ita amma bata bada kwanan nata ba, tunda kin ga kema tambayarki nayi kika bayar ba tare da nayi miki dole ba. To ita bata bayar ba, don haka sai a cigaba da kwana bibbiyun kawai.’ Ya fada cikin in-ina yana satar kallon Khadeejan ta cikin mudubi.
Sai da tayi da gaske sannan ta hadiya malolon da ya tokare mata makogoro; duk da dama hakan ta sa rai zai fada amma sai da abun yayi mata ciwo. Ita bata ma yarda Naja