fice, tace ‘Idan na tsahi daga aiki zan je gidan Mommy.’
Ya dan tsaya yana kallonta yana kokarin su hada ido ko zai karanto wani abu a fuskarta, sai dai bata bashi damar ba. Daga tsayen yace ‘Ki gaishe min da mutanen gidan.’
Ya fice ita kuma ta cigaba da cin abincinta ba tare da ko da ta kalli inda ya wuce ba; gaba daya ma a halin yanzu ko son kallonsa bata son yi.
……….
Tun wajen 12pm ta nemi izini a wajen aikin nata ta fice, kai tsaye gidansu ta nufa. Ta ci sa’a ta sami Mommy da Yaya Mama suna zaune a parlor suna hirarrakinsu. Bayan sun gaisa Khadeeja ta dubi Yaya Mama tace ‘A nan kika kwana Yaya.’
Tayi dariya tace ‘Ga jakata a kusa dani kina kallo amma kike min wannan tambayar, to ni yanzu ma zan tashi saboda 2pm zan dauko yara a makaranta sannan mu wuce gidan.’
Itama tayi dariyyar, ta umurci Hafsa da ta shida dakin Nabila ko taje kitchen wajen masu aikin gidan ta zauna.
Tun kafin tace wani abu Mommy ta dubeta tace ‘Lafiya dai na ganki kamar a fusace, sarkin rigima.’
Ta zumbura baki ta sunkyar da kai tana kallon hannunta kamar me kunkuni, sai da ta gama zumbura bakin sannan cike da takaici tana kokarin danne hawayen da ya taso mata tace ‘Mommy ni Mustapha zai mayar ‘yar aiki, kuma Baffa ya goya masa baya.’
Mommy ta gyara zama ta fuskanceta sosai tana kallon fuskarta da mamaki sannan tace ‘Ban gane ba, kuma me kawo Baffanki a cikin mayar dake ‘yar aiki? Shi Mustaphan me yayi miki?’
Tana bude baki zata yi magana hawaye ya kwace mata, ta sa bayan hannunta ta goge sannan ta labartawa Mommy abinda ya faru. Zuwa lokacin hawayenta ya gama kwacewa yana zuba kamar ana zubar da ruwan famfo, Mommy ce ma take kokarin goge mata. Tace ‘Mommy yanzu shikenan haka zan yi wata tara ina mata hidimar gida tana kwana da miji, bayan ni haka nayi nawa laulayin ko tausayina baya ji. Ko haihuwar Hammad fa ana gama suna dole na mike na koma hidimar gidan saboda ban ma ga fuskar cewa ba zan iya ba. Amma yanzu saboda ya auro ‘yar gwal shine zan karbar mata aiki ita kuma tayi laulayi.’
PAGE 185
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Yaya Mama tace ‘Nifa gaba daya ban gane. To ke me yasa bakya zuwa dakin kike barinta taje, ai da sai kije ki yi wanciyarki a can kiga ta inda marasa kunya zasu kwana tare.’
Kafin tayi magana Mommy tace ‘Gaskiya nima dai ban gane dabarar yin hakan ba, ai dakin ya kamata ki gyara ki tare har sai kin gama kwananki.’
Ta sa bayan hannunta ta goge hawayenta sannan tace ‘Mommy ba zan iya ba, ya kwana da wata matar a kan gadon sannan nima ya kwana dani a kan wannan gadon. Watakila ma da yayi aurensa ba tare da ya ci min mutunci ba abubuwa da dama zau zo min da sauki, ama gaskiya ba zan iya ba. Tunda ko bayan ta tare ranar da zan karbi girki bayan da ta gama kwana takwas dinta na shirya tsaf zan shiga dakin, amma har magriba bata fito daga ciki ba. Lokacin shi kuma ya riga ya fita. Don haka na kyaleta na shirya masa abincin dare tunda na gama kintsawa. Amma yana dawowa ko kallon abincin bai yi ba ya sameni wai tunda ina jego na bashi kwanakin ya kaiwa amaryarsa in ya so idan nayi arba’in sai a fara rabon kwanan. Kinga kenan ita ta riga ta san ba zai bani kwnan ba shi yasa ta ki fita ma daga dakinsa. Daga wannan lokacin dakin da me dakin suka karasa fice min daga rai gaskiya. Idan yana bukatata ya sameni a dakina, kuma yana zuwa din.’
Mommy wadda take binta da kallo tana jijjiga kai tace ‘Lallai Mustapha, ni na rasa ma me zan ce. Ni fa mamakin da nake Baffanki ko gaya min bai yi zai je ba balle da ya dawo ya gaya min, watakila jiya bayan ya fita da magriba Mustaphan yayi sa’a ya sameshi a gate suka gama magana.’
Yaya Mama tace ‘Hmm! Ai komai dadinki da miji idan dai wata macen ta gifta to sai abinda kika gani. Watan hakurinki ne ya kama har ya gama yayinta.’
Mommy tace ‘To yanzu ya za a yi? Kinga Baffanki ya riga ya sa baki a maganar ba tare da kin gaya masa ainahin abinda yake faruwa ba..’
‘To Mommy ya za ayi nayi masa duk wannan bayanin ya gane, ai ban ga alamar zai ma gane ba tunda ko a lokacin ma yace amfanin mta biyu kenan daya ta taimakwa daya. Kuma ya za ayi na zauna ina gaya masa Mustapha yana satar min kwana saboda na ki zuwa dakinsa?’
PAGE 186
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
‘Umm, hakane kuma. To Allah ya kyauta. Yanzu kam sai dai kiyi hakuri a ga abinda hali zai yi tunda dai babu wanda zai je ya kwance maganar baffanki. Ina ga kula dayarn wanda kika yi a baya bai kashe ki ba bana jin na wata tara nan gaba zai dameki.’
Haka suka zauna suka yi ta bata hakuri; sai daga karshe Yaya Mama tace ‘Kuma kema idan kin gaji kawai kiyi pretending ki kwanta masa, wallahi da kaina zan zo na taho dake na kawowa Mommy tayi jinyarki idan kin huta kya koma.’
Mommy ta kai mata duka tana cewa ‘Allah ya shiryeki yayar kwabo.’
Suna nan zaune wajen 1:30pm Baffa ya shigo gidan da sallama, bayan ya amsa gaisuwarsu da san