abincin rana. Ragowar abincin ranan shi ta diba ta zuba a flask ta ajiye musu ita da Hafsa saboda ta huta shiga kitchen da daddare.
Tana zaune a parlor tana bawa Hammad nono ya shigo parlor din, bayan ta amsa sallamarsa ya zauna kusa da ita. Sai da ya gama kame-kamensa yace ‘Da-Allah kiyi abincin dare gaba daya saboda Naja bata da lafiya, kin san na gaya miki ciki ne da ita kuma yana bata wahala.’
Ko da dai bata zata abinda ya zo fada kenan ba amma tana jiran wannan din ma domin tu tuni yara suka gaya mata Najan bata da lafiya kuma ta fahimci menene ciwon. Ta cire Hammad daga nono ta saka shi a kafada tana cewa ‘Ai kuwa ka ga yau ba girki zan yi ba ga ragowar abincin rana can shi na ajiye zamu ci da daddare. Allah ya bata lafiya.’
PAGE 179
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Ya sake bata rai ‘Khadeeja, da-Allah ki bari. Yarinyar nan bata da lafiya ko abincin ma ita bata iya ci, kuma ba ita nace ki yiwa girki ba. Ni da yara zaki girkawa, idan ta sami lafiya zata karbi girkinta.’
Ta kwantar da Hammad a gefenta sannan ta fuskanceshi gaba daya don bata cikin yanayi na son zance, tace ‘To ai cikin ba wani abu bane, ko ka manta ne? haka na dinga hadawa da cikin da komai duka da karancin shekaruna ga rashin mataimaki. Ita kuwa yanzu ka ga tana ma da mai aiki; ai babu wani abu da zai gagareta. Idan dai kwana ya zagayo kaina in sha Allahu zan yi kamar yanda muka saba.’
A fusace ya kalleta na dan lokaci sannan yace ‘Yanzu kenan ke babu halin ace kiyi wani abu sai ki tuno abinda ya faru shekarun da suka wuce? Kuna zaune tare a gidan kina kallon bata da lafiya nace kiyi girkinta amma kina nema kice ba zaki yi ba? Wai ke me kike son zama ne? babu wanda ya isa ya tankwaraki kenan saboda zaman kanki kike yi ko me?’
Ta sunkuyar da kai murya kasa-kasa tace ‘Ba haka bane, kawai dai nima mutum ce, yanda aka yi min na zata haka ake yiwa mutanen da ake so shi yasa nake so ko yaya ne ayi adalci.’
Bata saurari abinda zai fada ba ta mike ta dauki Hammad a hankali saboda bata son ta tasheshi ya fara bacci, ta wuce dakinta ta barshi a nan.
Yanda tayi wannan tafiyar ya tabbatar ko me zai yi ba zata saurareshi ba; wanda hakan yake nufin shi da yaransa zasu shiga halin rashin samun kulawa na tsawon wata takwas har Naja ta haihu, sai dai su sami kulawa kwana biyu kwana biyu kuma a barsu a gantale. Babu yanda za ayi ace ya dauki wannan kuma a halin yana da mata biyu. A yanda cikin nan yake wahalar da Naja kuma dole Khadeeja ce zata dauki wannan hidimar har zuwa lokacin da zata haihu.
Sai da ya gama lissafinsa sannan ya mike ya fice, kai tsaye dakinsa ya wuce ya dauki mukullan motarsa. Bai zame ko ina ba sai gidansu Khadeeja; baya son kai kara don ya kulaita ko ya kai kararta ma goya mata baya zasuyi, sai dai yanzu bashi da wani zabi da ya wuce hakan.
Ya ci sa a yana shiga gidan Baffa yana shirin fita, a nan bakin gate ya tsaya yayi masa bayanin halin da ake ciki.
PAGE 180
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Cike da kulawa Baffa ya jijjiga kai yace ‘Subhanallahi, to Allah ya bata lafiya. Yanzu ka ga fita zanyi amma in sha Allahu idan na gama abinda nake zan zo har gidan na sami Khadeejan. Kada ma kace mata zan zo, ka kyaleni da ita zan zo na sameta ka ji. Ai daya daga cikin amfanin karin auren kenan daya ta taimakawa daya a irin wannan yanayin.’
Suka yi sallama kowa ya nufi inda zai je.
PAGE 181
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Ba shi da tabbacin abinda Baffa zai yi a kan wannan matsalar amma dai yana saka ran Baffan zai fahimceshi ya saka Khadeeja ta dinga taimakawa Naja, a kalla a lokutan da bata da lafiya; idan ba haka ba menene ribar mata biyun ga namiji.
Bata samu tayi sallar isha’i a kan lokaci ba don haka har wajen 8:30pm tana zaune a kan dadduma, Hammad yana wajen Habib wanda yake zaune a parlor dinta yana kallon TV. Ta so ta jiyo muryar Baffanta suna gaisawa da Mustapha a tsakar gida, amma da yake bata sa rai da zuwan Baffan ba sai kawai ta zata kunnenta ne ya jiye mata ba daidai ba.
Tana nan zaune Mustapha ya turo kofar dakin ya shigo da sallama, bayan ta amsa sallamarsa yace ‘Baffan Mommy ne yazo, gashi nan a parlor na.’
Da mamaki ta kalli Mustaphan da alamomin tambaya a fuskarta, tace ‘Baffana?’
Yayi ‘yar dariya saboda yanda ta tambaya sannan yace ‘Baffan Nabeela dai.’
Itama sai ta dan yi dariya tare da mikewa tsaye; kwata-kwata bata yi zaton kararta Mustapha ya kai wajen Baffa ba. Ta yi zaton zuwa yayi ya ga sabon gidansu kamar yanda take ta faman rokonsa tunda suka tare yazo ya ga gidan. Nan da nan ta tashi ta fice don zuwa ta taryi Baffan nata. Sai da ta shiga kitchen ta jera ruwa da lemo a faranti sanna ta fito, ta dubi Habib wanda yake zaune a parlor din yana rike da Hammad tace ‘Yaya ku taso ku gaida Baffa gashi nan a parlor din Abbanku.’
Tana shiga parlor din ta sameshi da Shukra da Nasreen yayin da Abban nasu yake zaune da