NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 75 of 105

n ta taso ta bude masa kofar, ko a fuska bata nuna masa ta san tayi laifi. Ya shige cikin daki ya kalli abincin da take ci a gefen dadduma yace ‘Ya zaki taho nan ki kama cin abinci ki bar mutane? Kuma kina ji nace ki bata abincin itama.’ Duk yanda ta so abi maganar a hankali bai samu ba, domin yanda yayi mata wannan tambayar da isa da gadara take taji duk wata kara da zata iya yi masa ta bushe. Ta kalleshi ta kawar da kai sanna ta wuceshi ta koma ta zauna a gaban abincinta inda ta taso sannan tace ‘Gani nayi kun cike table din, abincin kuma babu tunda ni ban soya dankali da ita ba. Me kake so na bata?’ ‘Ai tun jiya nace ki dinga saka abincin a can don kowa ya ci kuma kika amsa ko? Me yasa ne kike so ki dinga raina ni a gaban mutane? Saboda me nace ki bata abinci ba zaki bata ba zaki shigo nan ki bar mutane?’ Ta kula dai duk wani zille-zille ba zai yi mata ba, ta kalleshi suka hada ido tayi murmushin yake mai dauke da takaici sannan tace ‘Kwana kusan talatin tayi a gidan nan tana girki bata taba bani ba, kuma tare kuke cin abinci kai da ita da yara baka taba cewa a kirawoni naci abinci ba; ko da yake ko ka kirawoni ma ba ci zan yiba tunda nima na iya girkawa. Kayi hakuri ba zan hada girki da matarka ba itama kar ta hada dani, duk wanda ya girka yaci shi da maigida da yara kawai.’ PAGE 177 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ta mika hannunta ta dauki fork a kan plate din da yake gabanta ta fara wasa da shi tana kokarin tokare takaicin da yake taso mata yana neman ya sakata kuka. ‘Wai ke me yasa ban isa na gaya miki magana kiji bane Khadija? Ko..’ ‘Ita da ka gaya mata ai ta ji har ta bani abincin, ko da yake ita ka dauka mutum shi yasa kake nema mata abinda zata ci. Ni da babu wanda ya damu da rayuwata ina nan kake fita ka siyo muku abinci ka sakata a gaba ita da yaranka ku cinye ba tare da ko rabona an bani ba. Ban yi magana ba, shine kuma yanzu za ace ni zan bata abinci; to ta cigaba da jirana taga idan zata ci abinci.’ Ta gyara zama ta jingina da bango ta kawar da kai. Ya rasa abinda zai gaya mata saboda tabbas ya san duk abinda ta fada gaskiya ne, sai dai a wancan lokacin ai laifi tayi masa na kin amincewa ta kula da yara don haka bai ga dalilin da zai sa ya bata abincin da ya siyo ba bayan taki ta girka. Ba tare ya ce mata komai ba ya fice daga dakin don a yanda ya san Khadija da taurin kai sai dai ya datse igiyar auren nan amma ba zata yi abinda yake so ba. Sai dai tabbas idan ta cigaba da gwada masa taurin kai irin wannan zai datse igiyar auren ya huta, taje can gidansu ta cigaba da taurin kan. ……….. Haka ya karasa shiryawa zuciyarsa babu dadi, don ko dakin Najan ma bai shiga ba suka fice tare da Habib suka tafi daurin aure. Yana ficewa itama ta gama shiryawa, ta kulle dakinta da parlor dinta gaba daya. Ta hada mukullanta da wanda ta cire daga jikin nashi keys din duka ta jefa a jaka don bata so ko shi ya bude mata waje idan bata nan. Ta goya Hammad ta tasa Hafsa a gaba, suna saukowa kasa ta shiga parlor din Naja inda ta jiyo hayaniyar yaran, ta dubeta da fara’a tace ‘To Anti ni na fita, zan je gidanmu ne in sha Allahu zan kwana biyu. Sai ranar litnin zan dawo.’ Ta juyo ta yi mata wani kallo na raina sanna tace ‘A dawo lafiya.’ Shukra ta tashi da gudu ta kama hannunta tace ‘Anti gidan Mommy zaki je?’ Ta shafa kanta ‘Can zan je Shukra, sai ranar Monday zan dawo.’ Ta langabe kai tana cewa ‘Kai Anti ina son zuwa fa, kwana biyu ban je wajen Anti nabila ba fa.’ PAGE 178 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) ‘Ai kin ga Monday akwai school ko? Shi yasa ba zan tafi dake ba. Amma idan zan koma ranar da babu makaranta zan tafi dake kin ji.’ Haka ta tsaya ta lallabata sannan ta wuce. 000000 Haka rayuwarsu ta cigaba; duk yanda ya so Khadeeja ta dinga binshi dakinsa gaba daya taki. Don haka bashi da zabi duk daren da yake bukatarta sai dai ya bita dakinta su kwana, idan bai je ba sai dai kawai ta leka dakin nasa tace masa sai da safe. Sau da dama ya sha kyaleta yaga ko zata biyo shi amma da zarar ta shiga dakin tace masa sai da safe sai tayi ficewarta. Da farko duk ranar kwananta idan bai ya bukatarta yayi kwanciyarsa a dakinsa haka yake kwana shi kadai, amma tunda Naja ta gane sai ta dinga bibiya; idan ta sameshi shi kadai sai tayi kwanciyarta a nan da uzirin laulayi. A zatonsu Khadeeja bata sani ba; sai dai ita din ta zabi tayi shirune tunda ta san yana yin hakan ne don ta hakura ta koma kwana dakinsa. Ita kuma har ga Allah gani take yi babu yanda za ayi ko wa take aure ta kwana gadon da yake kwana da wata matar; musamman Naja wadda bata tsanar wata mace kamar ita ba. …….. Tunda Khadeeja ta dawo daga gida kuma sai laulayi ya saka Naja a gaba. Haka zata wuni jikinta babu kwari, abinci kuwa to idan dai itace ta dafa ba zata iya ci ba dole sai dai ya siyo mata wanda zata ci. Yau Khadeeja take fita daga girki don haka a wajenta shi da yara suka ci
🏠