NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 74 of 105

ranar litinin sai na dawo.’ PAGE 174 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ya dan bata fuska ‘Kuma shine har kwana biyu? Ai na zata a gidan bikin zaki ga duk wani wanda ya kamata kije masa yawon.’ Tayi ‘yar dariya sanna tace ‘Kada fa ka manta bikin na dangin Baffa ne, ‘yan uwan Mommy su kuma ai sai dai naje musu gida yawon arba’n din ko? Hajiya Nana dama ban kai mata baby ba ga su Anti Halima da Baba Usman. Ka ga yau a gidan biki zan wuni, gobe kuma tun safe zamu fara da Nabila; dama zamu kai musu katin bikinta tunda ka ga an fara rabo duk da dai bikin saura sati uku.’ ‘Uhm, sai kun dawo.’ ‘Mun dawo kuma? Ni kadai fa zan tafi, Hafsa kawai zan dauka saboda Hammad.’ Ya tashi zaune yana fuskantarta ‘Na zata ke da yara zaki tafi kamar yanda kuka saba.’ Ta jijjiga kai tana dariya ‘Haba dai, yawon arba’in din na kwashi yara har hudu? Dama saboda babu mai kula da su ne yanzu kuma ka ga Antinsu tana nan. Ni kadai zan tafi.’ Duk yanda ya so ta tafi da yaran nan haka ya hakura ya kyaleta domin ta ci alwashin ba zata sake tafiya da su danginta ba tunda yanzu suna da uwar dakin da zasu dinga kawowa gulma. A kan lokaci ta gama abincin safe, sai dai da yake yana nan babu yanda ta iya haka ta jera a dining table din parlor dinsa. Dankalin bature ta soya da ragowar sauce din jiya da aka ci abincin dare sannan kuma da soyayyen kwai. Kowa a plate dinsa ta zuba masa har shi Mustaphan ta saka sauce a gefe da kuma soyayyen kwai. Nashi ta fara ajiye masa tare da na Shukra sannan ta juya ta koma kitchen din. Tana shigewa kitchen din ya dubi Afaf yace ‘Jeki kasa ki kirwo Antinki ta zo muyi breakfast.’ Nan da na ta mike ta fice, ya dubi Habib ya mike yana shirin ya bi Khadeeja kitchen ya karbo nashi abincin yace ‘Shiga parlor din Anti ka daukowa kujerar dinin guda daya a kara.’ Don haka yabi bayan Khadeejan. A hanya ta hadu da shi ta riko plate biyu, tana kokarin mika masa yace ‘Abba ne yace na daukowa Anti Naja kujera tare za ayi breakfast din da ita.’ PAGE 175 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Kafin ta gama fahimtar abinda ya fada ya wuceta ya nufi dining; tana karasowa ta ajiye farantan hannunta daya a gaban Nasreen ta zagayo da dayan zata ajiye a kujerar da take kusa da Mustaphan a daidai lokacin da Afaf ta shigo tare da Naja suna tafe suna hira. Kafin tayi magana ta zauna a kujerar da take kusa da Mustapha daga damansa a daidai lokacin da Khadeejan take shirin ajiye nata abincin a wajen. Tayi cak ta dauke farantin da take niyyar ajiyewa ta dubi Habib tace ‘Yaya kaje kitchen ka dauko naka abincin ke kuma Afaf ungo wannan ni sai na dauko wani.’ Cike da fara’a Naja tace ‘Ina kwana Umman Hammad.’ Itama nan da nan ta saki fara’a ‘Lafiya kalau amarya ba kya laifi, ya gajiya.’ ‘Alhamdulillah. Sannu da aiki.’ ‘Yauwa.’ Har cikin ransa yaji dadin yanda suka gaisa, haka yake son iyalansa ko da dai idan baya nan ba zasu hadu suyi hira ba to idan yana nan a zauna duka kamar haka a ci abinci tare; ya dubi Khadeeja yace ‘Yauwa itama ki taho mata da abincin ko?’ ‘Ok.’ Ta amsa a gajarce sanna ta juya ta nufi kitchen dinta. Kafn ta karasa kitchen din zuciyarta ta gama tunzura; Mustapha so yake yayi mata dole kenan? Ta gaya masa ba zata yi abinci da matarsa ba amma shine zai saka a kirawota harda zama a kujerarta. Lokacin da ita Najan take girki ai bai taba kiran Khadeejan yace tazo suci abinci ba shine sai yanzu don ya tabbatar mata Naja itace matar da yake kauna shine zai ce ta bata abinci. Nan take ta juye ragowar dankalin wanda dama ba yawa ne da shi ba ta ajiye ne saboda Shukra, ta hada da wanda da ta zubawa Afaf ta zuba sauce da kwai. Ta hada shayinta mai kauri ta dauka ta wuce dakinta ta bar Hafsa a kitchen tana cin nata abincin. Shiru Khadeeja bata fito ba, kowa yana ta cin abinci yayinda Naja take shan shayinta wanda ta hada. Shirun yayi yawa ya dubi Habib yace ‘Je ka dubo ko Antinka dankalin ta tsaya soyawa?’ Bai dade da shiga ba ya dawo yace ‘Abba bata kitchen din, tana dakinta kuma ta kulle kofar.’ Ya zauna ya cigaba da cin abincinsa ba tare da wata damuwa ba. PAGE 176 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ajiye fork din dake hannunsa yayi yayi shiru saboda takaici; mantawa ma yayi ya bawa Khadeeja mukullin dakinta saboda a da yayi alkawarin ba zai sake bata mukullin dakinta ba saboda yanda take kulle kanta a ciki tayi burus da kowa. Ya ture kwanonsa ya mike, itama Naja ta mike a lokacin. Ya kalli plate dinsa; ya riga ya ci da yawa sannan kuma sauran duk ya dame da sauce. Cike da damuwa ya cewa Naja ‘Ko wannan zaki ci naje na dubo.’ ‘No, kada ka damu. Ku ci abincinku akwai bread a kasa zan je na ci.’ Ta juya ta fice daga parlor din ba tare da ta surareshi ba. A fusace ya nufi dakin Khadija, tuna kafin ya fara buga kofar ya kirawo sunanta. Ba tare da bata lokacin ba ta amsa sanna
🏠