ai ki dinga yi da ita kun ma ragewa kanku aiki.’
Ta zumbura baki ‘Ah to don ni dai haka na san duk masu mace sama da daya suna yi.’
Yayi mata sallama ya wuce sama. Bata taba sanin idan Khadeeja ta karbi kwana abun zai sosa mata rai ba sai a wannan lokacin. Gaba daya zucuyarta tayi kunci, haka tabi bayansa da kallo har ya fice daga parlor din ya rufe mata kofa. Nan take hawaye ya wanke mata fuska; ta ajiye kofin da yake hannunta akan tebur ta hada kai da gwiwa ta sa kukan da ta kasa gane me ya kawo shi. Haushin Khadeeja ta karbi kwana ko kuwa haushin an barta da yunwa?
………..
Yana karasa shiga parlor dinsa ya kalli dining table, bai ga alamar abinci ba. Kamar ma ko taba wajen ba ayi ba tunda ya fita da safe. To me Khadeeja take nufi? Duk wannan dokin da yake na zuwa wajenta ita ashe bata gama fushin ba kuma bata gaya masa ba?
Cikin sanyin jiki ya karasa ya shiga dakinsa. Ga mamakinsa dakin ma ba a gyara ba. Yanda Naja ta fita ta barshi da safe yana nan a haka, babu ma alamar da take nuna mutum ya shiga dakin bayan fitarsa. Khadeejan ma da yake sa ran zai gani a dakin bata ciki. To ina take? Me take nufi bayan ya sanar da ita yau itace da kwana? Gaba daya ranshi ya gama baci; baya son fitnar Khadeeja don ita rigima da ita ba ta karewa, musamman a yanzu da yake da bukatarta.
Har ya juya zai fita kuma ya fasa, ya tsaya ya canza kaya ya shirya sannan ya dauki wayarsa ya fito ya nufi dakin khadeejan.
PAGE 170
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Yana shiga parlor dinta ya kai hankalinsa kan dining table, yanda ya ga wajen a jere da kwanuka ya tabbatar abincin ne ta dafa ta ajiye masa. To me yasa tayi hakan? Ya karasa kan tanle din ya bude kwanukan ya ga abinda ta dafa, sannan ya taba flask din ruwan zafi ya jishi a cike; tabbas ya san shayi ta dafa masa. Ya gyada kai ya juya ya nufi dakinta.
Duk da ita ba mace ce mai son mu’amala ta turaren wuta da humra ba amma dai tana son kamshi, tana da hadaddun turarkanta na jiki da nakaya wadanda idan dai ta zauna a waje sai ka ji kamshinsu. Yana tura kofar dakin nata kamshin turarenta yayiwa hancinsa maraba. Fitilar dakin a kashtake sai dai dim-light wadda take ajiye a kan durowar gefen gado itace a kunne; ga alama bacci ne ya kwasheta ba tare da ta kashe fitilar ba. Ya karasa kan gadon inda take kwance, ya leka fuskarta; bacci takeyi hankalinta a kwance gashi yanayin baccin ya yiwa fuskarta kyau. Kamar ya kyaleta sai kuma ya canza tunani, ya zauna a hankali a gefen gadon daidai inda kafafunta suke, ya daga abinda ta rufa dashi ya sosa mata tafin kafa a hankali. Ta janye kafarta da sauri sannan ta bude ido a hankali hankalinta gaba daya yana kan Hammad wanda yake kwance a cikin gadonsa na baby a gefen gadon nata.
Yayi dariya a daidai lokacin da ta ganshi, ya lakace mata hanci yana cewa ‘Yanzu mutum daya ne a rayuwarki wato Hammad ko? Ke na taba amma ba abinda ya tabaki kike nema ba yaronki kike nema kada a taba miki shi.’
Ta yi murmushi ta mutssike idonta tana gyara zama sannan tace ‘To ina laifi, nice gatansa kaga kuwa dole na kula da amanar Allah.’
‘Hakane. To a taso a bani abincina yunwa nake ji sosai.’
Ta zubo kafafunta daga kan gadon ta mike tana cewa ‘Bari na wanko baki.’
Ta wuce ta gabanshi ta nufi bandaki.
Ya bi bayanta da kallo yana yaba yanda jego ya karbeta. Ya dade bai ganta a haka sanye da rigar bacci kamar wanna ta jikinta ba sai yau kuma tayi matukar burgeshi. Yana nan zaune yana lissafi ta fito daga bandakin suka fito parlor din.
PAGE 171
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Sai daya zauna a table din sannan ta zuba masa abincin ta ajiye a gabansa, ta koma ta hada masa shayi kamar yanda yake so shima ta ajiye masa ta koma ta zauna a kujerar kusa da shi.
Tun kafin ta zauna ya fara cin abincin saboda da gaske yunwar yake ji; bayan ya cinye lomar bakinsa ya dubeta yace ‘Ke kin ci abincin ne?’
Tace ‘Um, mun ci ni da yara mun koshi tun dazu.’
Suka yi shiru na dan lokaci, jimawa kadan yana cin abincinsa yace ‘Wai me yasa baki saka abincin a parlor na ba kika kawoshi nan?’
Ba tare da wata damuwa ba tace ‘Ba komai, kawai dai nan din ya fi min kusa da kitchen saboda saukin aiki ko?’
‘Um hakane. Ki dinga sakawa a parlor din kawai kin ji can din zai fi yanda duk wanda yake son yaci zai iya diba.’
‘Ok, next time in sha Allah.’
Suka sake yin shiru na dan lokaci, jimawa kadan ya ajiye cokalinsa ya fara shan shayin. Bayan ya kurba ya ajiye kofin sannan yace ‘Kuma na ga baki gyara mana dakin ba, yanzu zaki gyara kenan ko a haka kike so mu kwana?’
Ta kalleshi da mamaki tana dan zare ido ‘Duk gyaran da nayi kuwa? Ko dai baka kalli dakin ba? Koda yake baka kunna fitila shi yasa ba zaka ga dakin sosai ba amma na gyara sosai fa.’
Ya kula da tana maganar hankalinta yana kan kofar dakinta kamar dai ta zata dakinta yake nufi bata gyara ba, yace ‘Ba fa dakinki nake nufi ba, dakina nake nufi tun