a.’
‘Hmm! Bacci ne ya kwashe ni. Zauna ki jirani na shirya Hammad na miko miki shi nima na shirya mu tafi.’
Nan da nan ta shirya Hammad ta mikashi wajen Hafsa suka zauna a parlor sannan ta koma dakin ta shiga wanka.
A gurguje tayi wankan ta fito daure da karamin farin tawul dinta, tana rike da wani tawul din tana goge jiki. Mustapha ta hango yana zaune a gefen gadonta ya mike kafa yana kallo a waya. Ba karamin mamaki tayi ba domin gaba daya ta kasa tuna me yake jira. Ba wai baya shiga dakin bane amma dai tunda Naja ta tare bai zauna a dakin ba sai dai ya shiga ya gaya mata abinda zai gaya mata yana daga tsaye ya fice. Ta dan tsaya kadan ta kalleshi sannan tace ‘Ina kwana.’
PAGE 167
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Ya ajiye wayar ya amsa gaisuwar tata da fara’a. Ta karasa gaban mudubi tana goge jiki yayinda shi kuma Mustaphan ya mike tsaye ya nufota. Ya karasa ya tsaya a bayanta ya rungumota ta baya, ta kalleshi ta cikin mudubin suka hada ido tace ‘Fita fa zan yi ka ga ma na makara.’
Yayi murmushi ya saka bakinsa a kan kunnenta yace ‘Nima fita zan yi, amma diai kin san yau kinyi arba’in yau ko.’
Ta dan motsa saboda yanda yake kara shigewa jikinta tace ‘Um.’
‘Ok, ki karbi kwananki yau sai ki ajiye min dinner.’
Murya kasa-kasa tace ‘Toh.’
Ya sumbaci gefen wuyanta sannan ya saketa ya juya. Har ya kusa zuwa bakin kofa kuma sai ya juya ya dawo, kafin ya karasa inda take itama ta juyo don haka ya tsaya a gabanta. Cike da damuwa ya kirawo sunata, bayan ta amsa yace ‘Bana jin dadin yanda kuke zama da Naja kamar kuna gaba, please ki dinga dan zama a parlor din kasa saboda ku saba.’
Ta dan yi murmushi tace ‘Ba wata gaba da muke yi tunda muna gaisawa, kuma duk abinda ya kama na magana ai muna yi.’
Ya kalleta suka hada ido sannan ya rike kwayar idonta yana cewa ‘Duk da haka dai ki dinga dan zama a can kuna hira. Kinga idan kina nan ba zata shigo ba itama sai tayi ta zama a parlor dinta inda ke ba kya shiga.’
Bata son ta ja zancen saboda bata son ta makara, don haka tace ‘To shikenan.’
Ya sake tsattsareta da ido sannan yace ‘Please!’
Tayi gajeren murmushi ta daga kai.
Ya fice bayan tayi masa a dawo lafiya.
Ta ja tsaki bayan da ya fice; bata jin zata iya rabar Naja, ta tsaneta. Watakila hakan yana da alaka da yanda Mustaphan ya bata mata rai a kan Najan tun kafin aurensu da kuma maganganun da ta gani a wayar Afaf da suna chatting da Naja. Gaskiya ba zata iya hira da wata Naja ba, gahi kuma bata iya munafurci ba balle taje ta yi na karya. Shi dai da yaga Naja yana so ya aurota suje can su karata.
Cikin sauri ta karasa shiryawa suka fice ita da yaranta.
PAGE 168
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Tun kafin Magriba ta gama abincin dare, don haka Habib yana shigowa daga masallaci sallar magriba ta turashi ya kirawo kannensa a wajen Naja. Nan suka zauna a parlor dinta suka ci abinci inda ta dafa macaroni da miyar hanta da salad. Suna gama cin abinci Afaf wadda dama bayan sallama bata ce mata komai ba ta tashi ta fice daga parlor din. Sauran yaran kuma suka zauna a nan aka cigaba da hira ana kallon TV. Wajen 8:30pm duk suka fara jin bacci don haka da kanta ta tashi ta rakasu dakinsu, ta shirya shukra sannan ta tsaya Nasreen ma ta shirya suka yi brush suka kwanta sanna ta koma nata dakin. Shima Habib yayi mata sai da safe sannan ya wuce nashi dakin.
Har zuwa lokacin Mustapha bai dawo ba, sai dai yayi mata waya ya sanar da ita sun fita da Alhaji don haka sai ta ganshi.
Don haka bayan tayi wanka tayi shirinta na bacci sai ta koma ta jera masa abincinsa a table din parlor dinta sannan ta wuce dakinta ta kwanta.
……….
Sai wajen 9:30pm sannan ya shiga gidan. Kai tsaye bayan ya kulle gidan parlor din Naja ya shige tunda itace a kasa.
Tana zaune a kan kujera tana shan cornflakes ranta a bace. Ya karasa bayan ta amsa sallamarsa ya sumbaci kumatunta sanna ya zauna a kusa da ita yana cewa ‘Cornflakes kike sha a daren nan?’
‘Um. To me gidan ce da girki kuma bata bani nawa abincin ba shine na hada cornfakes nake sha tunda ban saba zama da yunwa ba.’ Ta fada tana kara shan kunu.
Ya dan shiga duhu, yace ‘Umm, Khadeeja bata yi abinci bane?’
‘Ta yi, amma nan ta turo aka kirawo yara suka je samanta suka ci abinci. Da suka gama cin abincin ma a can suka yi zamansu Afaf ce kawai ta sauko ta tayani hira.’
‘Um! To ai na zata kowaccenku dama girkinta zata dinga yi ko?’
Ta harareshu sanna tace ‘A ina ake haka? Tunda wadda take da girki itace zata dinga kula da yara ai gikin ma gaba daya zata dinga yi. Shi yasa nima idan nayi abinci nake fitowa dashi nan parlor din inda kowa zai iya diba, itace bata fitowa ta diba saboda bata son ganina.’
PAGE 169
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
‘Wa ya gaya miki? Ba haka bane. Bari zan yi mata magana in ya so sai ta dinga yi da ke, kema ranar naki girkin s