NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 70 of 105

dan kuma ba haka ba ni zan je a canza amma ba zakiyi aikin TV ba matukar da aurena a kanki bana so.’ Ta dan gyara zama tace ‘To ai ko naje gidan ARTV din ma ba lallai na dinga fitowa a TV ba tunda aiyukan suna da yawa kuma ba duk ma’aikatan ne suke fitowa a TV ba.’ ‘Ni dai bana son kije wajen kwata-kwata tunda idan dai kana wajen wata rana za a sakaki a wani shirin kuma babu yanda zaka yi. Kawai kije su mayar dake makaranta ko kuma ki bani takardun ni naje.’ Ya fada yana mikewa tsaye. Bata ce komai ba yace ‘Ni na tafi gidan Hajia.’ ‘A dawo lafiya, ka gaishe min da su.’ Ta fada ba tare da ta kalleshi ba, kuma da yake shima ba kallon nata yekeyi ba bai ma san yanayin da tae ciki ba. Ta bi bayansa da kallo bayan da ya fice daga parlor din; ta ma rasa me zata ce masa. Koyon aikin jarida ya ganta tana yi ya aurota, kuma sau da dama ta sha gaya masa cewa babu abinda take so take buri kamar ace yau gata a gidan talabijin tana karanta labarai ko kuma gabatar da wani shiri. Sai da ta kusan gama karatun sannan yake sanar da ita shi baya son matarsa ta dinga fitowa a TV, kuma duk lokacin da ya gaya mata ana gaya masa cewa ita kuma burinta daya kenan a duniya. Daga baya nema ta fahimci cewa da ba don ya auro Naja a ma’aikaciya ba to da tabbas ba zai barta tayi aiki ba ma gaba daya. Yanzu kam ma sai taga kamar yana dai so ya takurata ne saboda bata yi masa yanda yake so ba, amma zata san yanda zata bullowa lamarin. ………. Sai da ta bari dare yayi lokacin ta san Baffa yana zaune a gida sannan ta kirawoshi, bayan sun gaisa ta sanar da shi abinda Mustapha din yace game da inda aka kaita bautar kasa. PAGE 165 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Bayan a saurari bayaninta yace ‘To ke kije makarantar mana, ai ba shine aikinki ba tunda bautar kasa shekara daya ne kawai.’ Tace ‘To ai Baffa idan naje ina fatan ne su rikeni su bani permanent aiki, kuma ka ga Baffa gaskiya ba zan iya aikin koyarwa ba don za a dinga samun matsala dani.’ ‘Um hakane, to bari mu gani. To ko gidan rediyo zaki je a mayar dake? In ya so sai na yiwa Mustaphan bayani.’ ‘Baffa ni dai da ka yi masa magana ya barni naje gidan TV din.’ Yace ‘A’a, kiyi hakuri ki yi a gidan rediyo tunda dai yace baya son a dinga nuna matarsa a TV kinga kuma hakan ya nuna yana kishinki. Kije kiyi a gidan rediyo ta yanda ko da an saka ki a wani shiri to muryarki kawai za a ji ba za a ganki ba.’ Ta so kwarai ace Baffa ya goya mata baya ta tafi gidan TV domin shi ya san tun tana yarinya burinta kenan, amma ta san tunda yace haka ba zai goya mata baya ba; sai dai idan ta matsa ranta ya baci. Don haka sai kawai ta hakura. Suka yi sallama da Baffa suka ajiye wayar. Sati yana zagayowa ta fara bautar kasa a gidan radio na Freedom Radio bayan da Baffa ya kirawo Mustaphan yayi masa bayani sanna ya bashi hakuri a kan ya barta tayi a nan din. Haka ya bari ba don ya so ba. ……… Tunda ta fara zuwa aiki kuma sai aikin gida da na yara suka kara taruwa suka yiwa Naja yawa. Domin sai ya zama kullum idan Khadeeja zata fita da hafsa take fita saboda rike mata Hammad a wajen aiki. Gani haka ya sa Naja ta saka Mustapha a gaba sai da ya bari ta dauki mai aiki wadda take zuwa kullum tana tafiya da yamma; tunda ya ce ba zata rabawa su Afaf wanke-wanke da gyaran gidan su dinga yi idan sun dawo daga makaranta ba. Babu yanda bata yi da shi ya mayarwa da Khadeeja kwananta ba amma ya ki; saboda ki-fadi. Duk da shi dinma yanzu zai so ace sun fara kwana bibbiyun tunda yanzu yana son shiga harkar Khadeejan; amma dai ya san Khadeeja ba zata karbi kwanakin nan da ta bayar ba tare da son ranta ba sai ta saka masa ciwon kai. PAGE 166 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ita kuma ta so ta yiwa Khadeejan magana amma ba zata yi ba, saboda kusan tunda ta zo gidan ba wata magana da take hadasu da Khadeejan bayan gaisuwa; da yake ma Khadeejan ba mai son fitowa bace sai ya zama idan dai ba aiki zata je ba to zasu iya kwana biyu ma basu hadu ba. Haka suka cigaba da rayuwarsu. ……… Ranar Juma’a ce ta kama ranar da Khadeeja ta cika arba’in. Duk wani shiri ta gama yinsa, ta gama gyaran jikinta kamar yanda duk wata maijego take yi. Sai dai bata sa rai zai bata kwanan ba kuma ta ci alwashin ba zata taba kai masa kanta ba sai dai shi ya kawo kansa. Bayan ta idar da sallar asuba sai ta sake bin gado ta kwanta tunda ta san Hammad ba zai taba wuce karfe takwas yana bacci ba zai tasheta. Bata san iya tsawon lokacin da ta dauka tana bacci ba bugun kofar da ake mata ne ya tasheta, a tare suka farka da Hammad wanda ya sa kuka. Ta lalubo wayarta ta duba lokaci inda taga 8:30am; nan da nan ta mutssike ido don ya kamata ace kafin karfe tara ta fita ta tafi gidan rediyo. Sai da ta dauki Hammad sannan ta mike ta bude kofar. Hafsa ta gani a tsaye; bayan ta gaisheta tace ‘Anti na gama aikin gaba daya na ga baki fito ba kuma jiya kin ce min na shiya da wuri zamu fit
🏠