NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 7 of 105

bata fahimcesu ba; amma dai zata dorasu a saiti kwanan nan. Tana cikin juye Indomie din suka shigo kitchen din suka wanke hannuwansu, sai dai abinda ya bata mamaki babu wanda ya dauko plate din da yaci abincin ya kawo kitchen din; duk a dining table din suka baro mata. Ta gama juye Indomie din ta mikawa Habib bayan ya gama wanke hannu. haka ta fito ta kwashe kwanukan daga dining su kuma suna zaune suna kallon TV. Ta hado shayi ta dauki guntun bread dinta ta wuce daki. Bayan ta gama shan shayin ta dauko kofin ta fito, tana isa gaban sink din zata ajiye kofin ta ga Indomie din da ta dafawa Habib ko rabi bai ci ba kuma ga dukkan alamu ya koshi kenan. 'mtsewww' ta ja tsaki a Fili. Ta wanke hannunta ta fito daga kitchen din. Har zata wuce daki Abbansu yace ‘Kizo ki shiryasu sun fara jin bacci kinga 10 har ta gota.’ Ta juyo ta dawo, ta dauki Shukra wadda ta riga ta fara gyangyadi Afaf, Habib da Nasreen suka bi bayanta. Sune suka nuna mata kayan baccinsu ta taimaka musu duk suka yi brush sannan suka shirya, ‘yan matan gaba daya suka haye gadon. Ta kalli gadon taga ma ba zai ishesu ba don haka ta koma dakinta ta dauko katifar da aka kawo mata saboda baki ta shimfidawa Habib a kasa. Ta gama tsaf zata kashe musu fitula Nasreen yace ‘Anti ba a kashe mana fitila sai mun yi barci.’ Ta mayar da fitilar ta kunna musu sannan ta fice daga dakin, ta wuce Abbansu a parlor ta shige dakinta. Ta riga ta gaji sosai don haka itama kayan bacci kawai ta saka ta rufe dakin nata ta wuce dakinsa, ta kwanta ta rufe idonta. …….. Lokacin da Khadeeja ta fito daga dakinsa ya zata dakinsu Afaf zata koma don su kwana tare, amma sai ya ga ta shige dakinsa. Ya tashi ya shiga dakin yaran inda ya tarar dukansu sunyi bacci, don haka ya kashe musu fitilar ya fito daga dakin. Ya kashe fitilun falon ya shige daki. Tana kwance a kan gado kamar ma bacci takeyi, don haka ya kyaleta. Bayan ya gama shirinsa ya kwanta, ya mika hannu ya tabata, ta juyo ta bude ido tace ‘Babe, ka shigo?’ 'Um.' Ya amsa a gajarce. Ta fara kokarin matsowa jikinsa, ya tashi zaune yana cewa ‘Kin baro yara su kadai, kin ga daga nan ma ai ba lallai ki jiyo motsinsu ba. Ni da na zata ma tare zaki kwana da Shukra a dakinki fa, she's just 3 bata saba kwana ita kadai ba.’ Ta dan matsa ta koma inda ta baro tana cewa ‘No, they will be fine fa, ba kaga a tsakiyar yayunta na sata ba kuma duk fa sun yi bacci. Ka ga na ma saka alarm wajen biyun dare zan je na dubasu sai kuma da asuba.’ 'Uhm, amma dai da kin daure kin kwana da su din.’ 'Kada ka damu ina jinsu.’ Ta fada sannan ta gyara kwanciyarta ta juya masa baya ta rufe ido. Haka kawai zai ce taje ta kwana a cikin yara; to ai ko ‘yar da ta haifa ce shekara uku ai raba wajen kwana zasu yi. Ba zama ta fara wannan aikin ba balle ya sallamawa yaran ita. Har barci ya fara daukanta suka ji an murda kofar, ya riga ya murda mukullin da ya shiga don haka sai kofar bata bude ba. Aka kwankwasa a hankali, suka tashi zaune tare shi da Khadeejan. Kafin suce wani abu Nasreen tace ‘Abba Shukra ce ta tashi zata sha shayi.’ Ya kalli Khadeeja yace ‘Oh, na manta ban gaya miki ba tana farkawa shan tea da daddare, tunda aka yaye ta ta saba. Kije ki hada mata shayi, da ga ta sha zata koma bacci.’ 'Shayi? A wannan daren? Ko fa 4 hours basu yi ba da cin tuwo, ikon Allah.' ‘Idan baki bata ba haka zata yi ta yiwa mutane kuka har sai an bata, kije ki hado mata gobe sai ki hada ki sa a flask kafin ta kwanta.’ Ya fada yana sake bata rai. Ta daura zaninta a kirji ta sauka daga kan gadon ta fice daga dakin cike da takaici. A tsakiyar gadon ta sami Shukra tana kuka, duk yanda zuciyarta ta kai ga kuna a wannan lokacin dole ta danne fushinta. Ta mika mata hannu tana dan murmushi tana cewa ‘Ahh! Sorry Shukra, ya aka yi? Kukan me kike yi?’ Cikin shesshekar kuka da gwarancinta tace ‘Tea.’ Ta zauna a gefen gadon ta rungumeta tana shafa bayanta tana mata magana cikin lallashi ‘Ya Isa, ya isa. Da safe ke zan fara hadawa shayi kinji Baby Shukra, kinga dare yayi ko? Muyi bacci da safe sai mu sha tea ko, harda bread ma da kwai ko?’ Ta gyada kai alamar eh, amma fa hawayenta ya ki daina zuba harda shesshekar. Ta cigaba da shafa bayana tana lallabata yayinda Nasreen ta koma ta kwanta har bacci ya fara daukanta. Abbansu ya ya turo kofa ya shigo dakin, Shukra ta leko ta kafaradar Khadija cikin shessheka tace ‘Abba tea zan sha.’ Ta kwace daga jikin Khadijan ta sauko ta taho wajensa, ya rage tsawo ya dauketa ya rungumeta yana cewa ‘Ya isa, Anti bata baki shayin ba?’ 'Tace sai da safe.’ ta fada tana shessheka. Ta mike ta rungume hannuwanta a kirjinta ta kalleshi da fuskar tausayi tace ‘Babe, ka barni da ita zata koma bacci kuma a hankali zaka ga ta ma daina farkawan shan shayi da daddaren. Ka barni na lallabata idan tayi bacci zan taho.’ Kallonta yake da mamaki a fuskarsa, sai da ta gama sannan yace ‘Yunwa fa take ji, haka z
🏠