aya a kansu ba babu wanda zai yi, idan kuma aka barsu haka yace zai yiwa mutane fada. Ta ja numfashi sannan tace ‘To ka dai mayar mata da kwananta don Allah, a fara rabon haka tunda ka ga yanzu saura kusan sati uku ta cika arba’in din.’
PAGE 162
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Ya numfasa ya zame sannan ya janyota jikinsa ta gyara mata kwanciya yana shafa bayanta sanna yace ‘Kada ki damu, in sha Allahu da safe zan yi mata magana. Ai na san kina kokari wajen kula da yaran nan kuma suma zaki ga suna jin dadin zama a wajenki, nagode sosai da kike kula min da su.’
A haka dai ya samu ya lallabata suka kwanta.
Ya san wulakancin Khadeeja, tabbas idan yaje yace mata za a fara rabon kwana yanzu ba lallai ta saurareshi ba. Baya jin ma zai iya tunkarata da wannan maganar idan dai ba so yake tayi masa dariya ba.
Haka ya cigaba da lallabar Naja don baya ma son ya tayar da maganar mayarwa da Khadeeja kwanata da ya kwace.
………..
Tunda ta kwana ashirin da bakwai da haihuwa ta yada wankan jego, kuma da yake ita din mace ce wadda ta damu ta fatarta sai ta mayar da hankali wajen gyaran fata da gahsin kanta wadanda ruwan zafi ya bata. A zaman da sukeyi da Mustapha ta san yana jin haushinta saboda ta ki ta cigaba da kula da yara shi da amarya suyi amarci, ta san ba lalli ya barta wasu kudi ba. Don haka ‘yan kudadenta da ta samu a barkan Hammad su ta fito da su ta nemi Baffanta ya kara mata dubu goma sannan ta hado kayan gayarn fata. Nan da nan cikin sati guda haske da santsin fatarta ya fara dawowa.
……….
Kamar yanda ya saba kullum da safe zai leka su gaisa kafin ya fita. Yau din ma haka ya shigo parlor din da sallama. Suna zaune a parlor din ita da Habib suna cin abinci; ita tana zaune ta mike kafa da Hammada a kan cinyarta yayinda shi kuma Habin yake zaune daga gefenta yana cin nasa abincin. Funkaso ne ta soya da zafinsa tare da parpesun kaza suke karyawa da shi; don kanta ta dafa farfesunta amma ta riga ta saba shi Habib idan dai tana nan baya cin abinci a wajen Naja. Don haka idan dai ya shigo bata hanashi, domin wani lokacin ma ajiyewa take yi don ta san zai zo nema.
Ya karasa ya zana a kan kujera daga kusa da Khadeejan, bayan ya amsa gaisuwarsu yace ‘Nan kuka kule kuna cin dadi ashe shi yasa na ji shiru.’
PAGE 163
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Tayi dariya kawai ba tare da tace komai ba, Habib ne yace ‘To ai Abba Anti Naja tuwo ta dafa jiya na san dumame za a ci shi yasa na gudo.’
Sukayi dariya gaba daya. Ta san so yke yace zai ci domin yana son funkaso, ita kuma bata so yace zai cib saboda dafawa tayi har abincin ran tunda so take ta fita idan ta dawo kawai sai taci abunta. Ya dubeta tana cinye funkason karshen yace ‘Idan akwai funkason ki zuba min na dan ci, duk da dai nayi breakfast amma ya bani sha’awa.’
Ji tayi kamar tace masa babu, amma Allah ya sa bata iya rowar abinci ba, musamman ga mutumin da shi ya kawo cefanen. Don haka bayan ta cinye nata ta mike ta kwashi kwanukan ta shige kitchen bayan ta mikawa Mustaphan Hammad; Habib shima ya kwashi nashi kwanukan ya bi bayanta. Jimawa kadan suka fito tare, ta kawo tray din da ta riko ta ajiye a gaban Mustaphan sanna ta sa hannu ta karbi Hammad; shi kuma Habib ya fice daga parlor din.
Ya sauka kasa ya fara cin abincin sannan ya dubeta yace ‘Shine kinyi funkaso ko ki kirawoni.’
Tayi ‘yar dariya tace ‘Ai na san ka riga ka ci better ka cika cikinka shi yasa na sa yarona a gaba muna ci mu kadai.’
Yayi dariya ya mayar da hankali wajen cin abincinsa.
Jimawa kadan ta tahsi ta shige daki, bata dade ba ta fito tana rike da takarda a hannunta. Sai da ta zauna sannan ta mika hannu ta ajiye takardar a gafensa tana cewa ‘Ga posting letter dina, jiya na karbo. Anyi posting dina gidan talabijin na ARTV.’
Nan da nan ya bata rai, bai ce mata komai ba sai da ya karasa cinye abincin sanna ya dubeta yace ‘Kin san dai bana son aikin jaridar nan ko, sai da mace ki saka ayi posting dinki makaranta amma shine kika je kika saka aka kai ki gidan talabijin don ki dinga fitowa a TV.’
Ta kawar da kai tana mamakin Mustapha. Tana karatunta na aikin jarida ya ganta ya aurota amma tunda yaga ta kusa gamawa yake ta faman gaya mata aiki daya zai bari tayi shine koyarwa. Watakila ma da ace bai kara aure ba da ta hakura tayi koyarwar amma yanzu kam babu yanda za ayi ya auro amaryarsa tana aikin office duk da dai ba na TV bane; sannan ita yace koyarwa zata yi.
PAGE 164
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Tace ‘Ni bani nace su kaini can ba, sun duba abinda na karanta ne kawai. Kuma idan nace a kaini makaranta naje na koyar dasu me? Ni da na karanci aikin jarida.’
Cikin halin ko in kula yave ‘Ko hausa ba sai ki koyar ba ko English, amma kin san babu yanda za ayi na barki kina fitowa a gidan TV duk duniya suna kallonki kina iya yi ko?’
‘To yanzu ya kake so ayi?’
‘Kije kawai su canza miki, i