NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 68 of 105

, yanda nake bukatar hutu daga kwana saboda jego haka nake bukatar hutu daga hidimar gida da ta yara, don dama wallahi dagewa nakeyi. Idan kuka gama arba’in din muka fara rabon kwan sai na dinga hadawa ina karba.’ Yaja dogon tsaki ya yarfar da hannu, har ya bude baki zai yi magana kuma sai ya fasa. Ya juya ya fice daga parlor din. …….. Duk yanda yake tunanin Khadeeja zata saurara masa hakan bai samu ba. Yana so ya mayar mata da kwananta da ya karab ya bawa Naja amma kuma yana son karin lokaci don ya kara sabawa da Najan. Haka dole ya hakura ya zuba musu ido; sai dai duk wani jin dadi da yake sa ran zai samu daga wajen Najan baya samuwa saboda yanda take wuni a gajiye saboda hidima. Suna kwanciya bacci yake kwasheta; gashi kullum cikin yi masa mita take a kan ita ya mayar da hidimar yara wajen Khadeeja. Duk da kusan Khadeejan ta sallama musu Hafsa tana tayata. Ita kuwa Khadeeja gaba daya haushinta yake ji don gaba daya ya daina kulata, a yanda yake ji yanzu ma baya jin zai kulata koda tayi arba’in din idan dai ba itace ta kawo kanta ta bashi hakuri ba. PAGE 160 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Duk yanda Naja ta zata kula da yaran nan zai yi mata sauki abun ba haka bane, domin da kyara take kaiwa yamma saboda gajiya. Gashi Khadeeja ta sallama musu Hafsa kullum cikin taimaka mata take; abu daya da Khadeeja ta hana Hafsa yi mata shine girki. Ta so kwarai ace ta dinga barwa Hafsa tana yi musu girki idan ta fita, amma Khadeeja ta ki bari. Don haka kullum kafin ta fita aiki sai ta dafa musu abincin rana kuma idan ta dawo sai tayi na dare. Gashi duk da suna shiri da Afaf ta gane Afaf ta fita son jiki, don duk yanda take jin zasu tayata aiki hakan ma bai samu ba. ……. Yau satinta biyu da tarewa; yana zaune a parlor dinta shi da yaransa kamar yanda suka saba suna kallon TV bayan sallar isha’i. Ita kadai ce a tsaye tana kokarin jera abincin dare a dining. Tana jerawa tana mita a ranta yanda yaran basa tayata aiki, ko da zata ce su tayata to fa idan dai yana nan ba zasu tayata ba; sai dai tayi aikinta ita kadai. Gashi kuma baya son Hafsa ta dinga yi masa girki. Bayan ta gama jera abincin suka taso gaba dayansu suka zauna harda ita suna cin abinci. Jollof sphagetti ce da kifi; ana cikin cin abincin Shukra ta daga kifin da yake kwanonta tace ‘Abba a cire min kaya.’ Har ta bude baki zata ce Afaf ta cire mata yayi sari yace ‘Ki mikowa Antinki ta cire miki.’ Haka Afaf wadda take zaune a tsakanin Najan da Shukran ta dauki plate din da yake gaban Shukran ta mikawa Naja. Ba tare da ta ce komai ba ta sa hannu ta bara kifin gida biyu ta cire kayar sannan ta mikawa Afaf wadda ta sake mikawa Shukra. Haka har suka gama cin abincinsu babu wanda Naja ta sake yiwa magana. ……. Tana zaune a gefen gado tana shirin kwantaw bacci ya tura kofar ya shigo da sallama, da kyar ta amsa sallamarsa saboda yanda take jin haushinsa. Gani take kamar da gayya ya bari matarsa ta sallama mata yaran sannan kuma sun kai su kula da kansu amma komai sai yace sai tayi musu. Ya karasa ya hau gadon ta bayanta ya kwanta, tana kwanciya ya janyota jikinsa. Ta dan tureshi tana cewa ‘Bacci fa nake ji Habibi, wallahi na gaji. Kuma ka ga gobe yara zasu makaranta kuma zan je aiki.’ PAGE 161 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ya kara kankameta yana laluba jikinta yana cewa ‘Sannu, bari nayi miki massage yanzu gajiya zata sauka.’ Ta dage ta janye jikinta ta zauna a kan gadon, hakan ya sa shima ya tashi ya zauna a kusa da itayana kallon fuskarta kamar mai neman amsa a fuskar tata. Kafin yayi magana ta langabe kai tace ‘Habibi ni dai don Allah ka mayarwa da maman Hammad kwananta, in ya so mu cigaba da yi kwana bibbiyu yanda tsarin yake.’ Da mamaki ya kalleta suka hada ido sannan yace ‘Kin gai dani kenan Baby.’ Ta mika hannu ta shafi gefen fuskarsa tana murmushin yake sannan tace ‘Ya za ayi na gaji da kai, ni kama ai ban ki ba ace ni kadai ce matarka kullum muna tare. Amma ka ga aiki yana yi min yawa sosai, yiwa yara abinci kadai ya isheni da shiryasu makaranta. Kullum a gajiye nake kai kanka baka samun yanda kake so a wajena. Amma ka ga idan zan dinga samun kwana biyu a tsakani na huta ai ina ga hakan zai fi mana sauki ko? Tunda nace a daukar min mai aiki kace Hafsa ta ishemu; ita kuma wannan yarinyar wallahi karin aiki ce saboda ta fi su wasa da son jiki. Ni ban ma san yanda akayi Khadeejan take zama da ita ba. Kawai dai kace ta karbi kwananta.’ Har ta gama maganar yana binta da kallo ba tare da yace komai ba, sai da ta gama ta numfasa sannan yace ‘Um haka ne, amma dai ai kinga kula da yaran yanzu fa ba wani aiki bane tunda gaba dayansu kowa ya iya kula da kansa. Kusan za a iya cewa abinci ne kawai sai an dafa musu.’ Ta kalleshi suka hada ido. Har ta bude baki zata yi magana kuma sai ta fasa; ta kula ba so yake ya karbi uzurinta ba. Yaran da hatta kula da kan nasu ma da yake cewa sun iya idan dai bata ts
🏠