NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 66 of 105

asu zo sun ce min sun shirya ba na zata ma sun gaya maka kun wuce sai da Habib ya gaya min yanzu sannan na sani.’ ‘Ban gane ba, wai wace magana kike yi ne? to me yasa baki tashi kin shirya su ba?’ ‘Oh to ai wadda take da kwana itace da gida musamman ma da yake ni ina jego. Na zata da kai mata kwanan ka gaya mata abinda aka saba yi na running gidan.’ Mamakin da yake fuskarsa ya karu ya hade da takaicin Khadeeja, yace ‘Ban gane wadda take da kwana itace take da gida ba Khadeeja. Ke kika saba shirya yaran nan kullum kuma kin san haka, shine yau saboda ganin ido zaki ce ita zata shiryasu? Idan kina jin haushina ai sai ki gaya min tunda ba dole nayi miki kika bar mata kwanan ba ko? Zaki fara wulakancin naki ko Khadeeja?’ Tayi dariyar yake tace ‘Wallahi ni duk ban gane ba. Ai ni a yanda na sani duk matar da take da kwana da girki itace take duk wata harka ta kula da gida, nima idan na karbi girki sai na hada gaba daya nayi.’ ‘Khadeeja, bana son wulakanci. Yaran nan a hannunki suke kuma da ke suka saba, ya za ayi tana zuwa ki dora mata kula dasu ita da yau zata koma aiki.’ PAGE 155 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) ‘Amma dai ba dasu na zo ba a nan na samesu ko? Kuma idan ban manta ba nima daga zuwana aka hada ni da su, kamar ma ita an daga mata kafa. Hidimarsu ta makaranta ma wadda ta riga ta saba yi tun ma kafin ta auri ubansu balle yanzu da ta aureka, ai inaga wannan ma karamin abune.’ Ya gama kulewa har wani huci yake, ya cije lebe sannan yace ‘Khadeeja bana son wulakancinki fa, yanzu me kike nufi da yaran nan?’ ‘Alkhairi nake nufi da kowa, kawai dai duk wadda take da kwana ta hada duk har gidan da yaran ta kula da su. Shikenan.’ Har ya juya zai fita ya juyo ya nuna ta da yatsa yana cewa ‘Yanzu shikenan kintura mata yara har tsawon sati hudu?’ Ta dago ta kalleshi cikin halin ko in kula tana cewa ‘Na tura mata mijin ma?’ ‘Mtsewww!’ ya ja dogon tsaki ya fice ya maka mata kofar. Tayi ‘yar dariya ta cigaba da wasa da Hammad. …….. Har ya koma dakin tana kwance tana baccinta domin office din da zata ta riga tace sai wajen sha daya zata tafi saboda an canza mata branch sakamakon aurensu da Mustapha; ta san tunda yau zata fara reporting tana da damar makara. A hankali ya bude kofar ya shiga saboda kada ya tasheta daga bacci, ya karasa ya zauna a gefen gadon. Ya zuba fuskarsa a tafukan hannunsa yana shafa fuskar, gaba daya kansa ya kulle. Yayi zaton yaran nan tunda suna wajen Khadeeja shikenan a wajenta zasu cigaba da zamansu ko da ya kara aure. Gaba daya ma shi bai taba zama sun yi maganar yara da Naja ba, kawai dai yana sakata hidimarsu idan ta kama kuma yana nuna mata cewa yana so su sami kulawar da yake jin sun rasa daga wajenta. Baya jin zata bashi matsala saboda yanda yaga tana kulawa da su tun ma kafin ta aureshi balle yanzu da zata yi da hujja. Ya juya ya dan tabata. Ta bude ido ta kalleshi tayi murmushi sannan tayi mika. Tace ‘Honey har ka dawo?’ Ya dan kawar da kai sanna yace ‘Daga ina?’ ‘Umm! Na zata ‘yan makaranta ka kai.’ ‘No, ban kaisu ba sun riga sun makara sosai sai gobe.’ ‘Ok, Allah ya kaimu.’ Ta zuro kafafunta kasan gadon ta kwanta a kafadarsa tana cewa ‘Bari naje na yi wanka sai na fito na hada mana breakfast. Ina jin ma kawai sai na shirya ka bani lift.’ PAGE 156 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Yace ‘Ai kuwa sai kiyi sauri don ga yara can ma ke suke jira ki zo ki bamu abincin gaba daya.’ Ta daga kafadarsa ta dan kalli fuskarsa da mamaki ‘Antin bata nan ne?’ Ya kawar da kai daga kallon da ta kafeshi da shi, yace ‘Tana nan. To ai kin ga kece da kwana don haka kece zaki dinga yin baimcin duka gida kina kula da yara, in ya so idan ta karbi kwana sai ta cigaba. Duk wadda take da kwana itace da gida.’ Ta sake leka fuskarsa da mamaki a kan fuskarta tace ‘Ban gane ba, ai ni ban karbi girki ba, kwana ne kace ka tambayeta ta bamu har tayi arba’in. kuma yara ai na zata tunda a wajenta suke sai suyi zamansu duk abinda ya kama ai zan saka hannu.’ ‘A’a, wadda take da kwana itace zata dinga hadawa tayi komai kawai. Kiyi sauri kiyi wankan ki zo ki bamu abinci.’ Shiru tayi kawai tana binshi da kallo. Jimawa kadan ya kalleta suka hada ido, ya gyara zama ya kama hannuwanta duka biyun ya rike sanna yace ‘Kin ga wannan fa ba wani abun damuwa bane, ai dama kin san duk inda ake da mace sama da daya ai dama duk wata hidima rabawa ake yi. Idan yanzu kika ki yin wani abu ai sai ki janyo kwanan amarcin ya kare tunda kin ga dole ne na koma kan tsarin kwana bibbiyu don tabbatarwa an yi adalci ko?’ Ta sunkuyar da kai tana kallon kasa don gaskiya ita bata zata haka ba; ba wai ba zata kular masa da yara ba amma dai ta sa rai zasu yi zamansu a wajen uwarsu itace zata dinga hidimarsu ta kullum in ya so ita duk wanda yazo inda take a cikinsu zata yi masa duk wani abu da ya kama. Ta dago
🏠