NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 65 of 105

zkar dinta sannan ta koma ta kwanta. Tun kafin a daura aurensa da Naja ya riga ya gaya mata amarci zasu yi na kusan kwana talatin domin lokacin da zata tare zai yi daidai da kwanan Khadeeja goma sha biyu da haihuwa. Don haka ya sanar da ita gaba daya kwanan nata ne har sai Khadeeja ta gama jego kwana arba’in. Ita Khadeejan ce bai gayawa ba shi yasa ma ta zata za ayi yanda aka saba ne ta karbi kwananta bayan kwana bakwai. Ba karamin dadi yaji ba da Khadeeja ta amsa masa ko da yake dama bai sa ran zata bashi matsala ba tunda dai ta san ba zata biya masa bukatarsa ba wadda a wannan lokacin ko allah ma bai haramta masa ya kaiwa daya matar tasa bukatar ba. Cikin walwala suka kwana shi da amaryarsa, ko da ya fito da asuba zai tafi masallaci ya hango fitila ta kasan kofar dakin Khadeeja don haka ma ya san ta riga ta tashi. Da sallama ya shigo parlor din bayan ya dawo daga masallaci, kai tsaye ya nufi kitchen din don ya jiyo motsinta a can. Tana tsaye da goyon Hammad tana zuba ruwan zafi a flask. Bayan ta amsa sallamarsa ta gaisheshi; yana ta wani kau da kai yana muzurai kamar yanda ya saba idan yana so ya gwada mata son kai haka ya amsa gaisuwar tata. Ta mayar da kettle din inda take sanna ta bude fridge don ta dauko ragowar peppersoup dinta. Yace ‘Ina yaran? Basu taso ba.’ ‘Eh.’ Ta amsa a gajarce ba tare da ta bar abinda takeyi ba. Ya kula da yanayinta idan ya takurata zata iya birkice masa a safiyar don haka yace ‘Ok, idan sun shitya kice su biga min kofa please.’ ‘Ok.’ Ta sake bashi amsa a gajarce. Ya juya ya fice daga kitchen din. Ta karasa dumama soup dinta ta juye a flask, ta dauki ruwan zafinta ta hada ta kai daki sannan ta dawo ta dauki kayan shayi duka ta shigar daki. Ta zauna ta ci burodi da soup ta sha shayinta mai kauri sannan ta koma ta kwantar da Hammad itama ta kwanta. PAGE 153 MIJIN MARIGAYIYA A HAUSA NOVEL by Sakina Yazid (Innar su Amal) Bata dade da kwanciya ba kuwa bacci ya dauketa saboda dama na jiya ba isarta yayi ba. Kamar a mafarki taji ana buga mata kofa, tayi firgigit ta bude ido. Ko ba a gaya mata ba ta san wannan bugun Habib ne don haka ta tashi zaune ta janyo wayarta ta duba lokaci; 8:25am. Ta janyo zanin goyon Hammad dake kusa ta rufe jikinta sanna tace ‘Shigo Habib.’ Ya turo kofar ya shigo da sallama, tun kafin ta gama amsa sallamar tasa yace ‘Anti yau makara kika yi ne? Yanzu har past 8 fa kinga bamu tafi makaranta ba.’ ‘To me yasa baki tafi ba, ni ai na zata kun tafi tuni.’ Ya karasa ya zauna a bakin gadon da mamaki a fuskarsa yana cewa ‘Anti baki tashemu ba fa; nima bayan mun dawo daga masallaci da Abba har nayi wanka fa na dan kwanta don na san zaki tasheni shine bacci ya kwasheni. Su Afaf ma gasu can ko sallah ma basu yi ba sai yanzu na taso su har Hafsan.’ Ta kama haba tana cewa ‘Ikon Allah. To ai ba nice da girki ba Habib, Antin ku ce. Itace zata tashi kowa ta shirya shi yasa ma ka ga ban fito ba.’ Ya tabe baki yana zare ido ‘Tab, to ai kuwa daga ita har Abban babu wanda ya fito.’ ‘To Allah ya sa dai lafiya, kaje ka buga musu kofa. Ka murda kofar parlor din a bude take sai ka kwankwasa dakin kaji.’ Ya mike ya fice daga dakin yayinda ita kuma ta zame ta gyara kwanciyarta da niyyar komawa bacci. …… A tsakiyar parlor din Habib yaci karo da Abban nashi yana fitowa da gaggawa, suka hadu a tsakiya suka yi cirkocirko. Abban nasu yace ‘Kai Habib meye haka? Na cewa Anti ku taso ni idan kun shirya me yasa baku taso ni ba? Kai ko uniform ma baka saka ba.’ Yace ‘Abba ai makara muka yi, Anti Najan bata tashemu mun shirya ba.” Kafin ya bashi amsa sauran yaran suka shigo kowa da kayan bacci, ya kallesu sannan ya mayar da hankalinsa kan Habib din yana cewa ‘Wace Anti Naja kuma, ko dai Anti Khadeeja?’ ‘To ai itama Antin bacci takeyi yanzu naje tashinta tace min ba itace da girki ba Anti Naja ce zata shirya mu.’ Mamaki ya kama shi; ya za ayi Khadeeja ta gayawa yaro wannan maganar? Wane irin wulakanci ne bayan itace ta saba shirya yaran kawai kuma yanzu sai tace Naja ce zata shiryasu? PAGE 154 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ba tare da yace komai ba ya wuce yaran ya nufi dakin Khadeejan. Habib ya dubi ‘yanuwansa yace ‘Yau dai mun yi mising school, ni yunwa nake ji ma kuzo muje kasa bread yana can ko shayi sai mu hada.’ Ya wuce suka bi shi suka sauka kasa. Kusan a fusace ya tura kofar, hangota da yayi a kwance tana bacci ya kara harzuka shi. Sautin bude kofar ne ya farkar da Hammad daga bacci. Ta tashi zaune tana mittsike ido sanna ta mika hannu ta daukeshi. Ta dubi Mustapha cikin halin ko in kula tace ‘Ohhh! Abba ka tayar min da yaro yanzu babu sauran bacci.’ Ta daga shi yayi mika sannan ta saka masa nono yayinda Mustaphan yake cewa ‘Me ya faru naga baki tashi kin shirya yara ba bayan yau akwai makaranta, kuma fa ko da asuba sai da na ce miki idan sun shirya kice suyi min magana?’ Tace ‘Oh! Ai b
🏠