d da shayi muka sha ba wani abu ba, amma dama naga bread din da yawa ka siyo gashi can mun bar muku guda daya ka dauka ka haye muku da shi. Ko a nan zaku yi breakfast din?’
Ya kalleta da dan mamaki ya cije lebe don baya son ya ja zancen a gaban yara yace ‘Um, idan kin gama dai kya hawo da shi.’
‘Ok.’ Ta amsa cigaba da cin abincinta.
Sai da suka gama cin abincinsu tsaf sannan ta dauki bread din ta haye sama, tana shiga babu kowa a parlor din don haka ta karasa kan dining table ta ajiye bread din ta shige dakinta.
Kamar tare suka shiga dakin don ko zama bata yi ba ya shigo ya tura kofar, yana daga tsaye a jikin kofar yace ‘Wai ya na ganki a nan ina breakfast din namu ni da kanwarki?’
Ta karasa ta zauna a kan gadon ta jingine ta mike kafarta tana cewa ‘Oh, ga bread din can na ajiye muku ai ko akwai wani abun ne?’
Da mamaki yace ‘Ai na zata zaki dan dafa wani abu ko don saboda ganin ga bakuwa kin kwana da ita a gidan.’
Bata san lokacin da dariya ta kwace mata ba, haka kawai maganar tashi sai ta bata dariya musamman da ta kalleshi kuma yana cewa wai “kin kwana da bakuwa”
Ta dan gintse tana kokarin saita fuskarta sanna tace ‘Na kawana da bakuwa ko ka kwana da ita? Tea and bread muka ci fa kuma gashi can na ajiywmata ita bakuwar tawa, ina ga kamar ai dafa ruwan zafi bai kamata ya zama matsala ba ga wanda aka bawa burodi ko?’
Ya bata rai saboda kwat-kwata bai zata haka ba; a iya saninsa sai sun kwana bakwai da amarya Khadeeja tana yi musu girki sannan sai araba kwana amma gashi tana nema ta kawo masa raini. ‘Ba fa na son raini Khadeeja, duk wanda ya kara aure matarsa ta gidan itace take yiwa amarya girki har sai ta kwana bakwai amma zan zo ina miki magana kina min wani zancen banza. Ai ko bazawara na aura kin san ya kamata kiyi mata abinci na kwana uku balle budurwa.’
PAGE 148
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Ta kalleshi ta kawar da kai; babu yanda za ayi ta yiwa Naja girki sai dai duk abinda zai yi ya yi; ta tsani Naja ta tsani jin sunanta. Watakila da ace ya biyo ta hanyar da ta dace wajen sanar da ita zai kara aure da wadda zai aura da haushin da take ji bai kai haka ba, amma gaskiya babu abinda zai sa ta yiwa wata Naja girki. Ya auro matarsa ya gama more kwanan amarci sanna ita kuma bayan bacci da bata yi cikin nutsuwa ba kuma ita yake so ta tashi da sassafe ta hada musu breakfast na warware gajiya, bata taba ganin rainin hankali irin wannan ba. Ta bata rai sannan tace ‘Ba a biya mana wannan hadisin ba a islamiyya.’
Mamaki ya kamashi ya bude baki amma ya rasa abinda zai gaya mata. Yana kallo ta zame ta gyra kwanciyarta ta juya masa baya. Bai shirya da wannan mahaukacin taurin kan nata ba wanda idan ta fara shi sai duk garin kowa ya ji. Ya dan tausa muryarsa yace ‘Bana son wasa Khadeeja, don Allah ki tashi ki samarwa yarinyar nan abinci. Next week ai zaku raba girkin kowa ta dinga yin nata, amma for now ki tashi ki bamu breakfast.’
Ta sake gyara kwanciya ba tare da tace masa komai ba. Ya kalli kasa yana jijjiga kai don ya san ta gama magana; takaici ya kamashi. To yanzu ya za ayi tana amarya ya bata bread ruwan zafin ma ace sai ta dafa. Haka ya fice daga dakin yana wasi-wasi.
Yana ficewa ta juyo ta harari kofar kamar yana wajen ta ja dogon tsaki tace ‘Dan rainin hankali!’
………
Yana shiga ya tara da ita ta fito daga wanka tana shirywa. Tun kafin ya gama shiga dakin tace ‘Allah ya sa dai an gama abinci don wallahi yunwa nake ji kamar an min sata a ciki.’
‘Akwai dai bread, sai dai idan kin fito ki dafa ruwan zafi da kwai haka sai mu karya.’
Da mamaki ta kalleshi tana cewa ‘Ruwan zafin ma sai na dafa? Yau ne fa kwanana na farko a gidan, haba! Kitchen din ma ban san inda yake ba.’
Cikin damuwa yace ‘To ko order za a yiwo?’
‘Ni ban gane ba, wai ita matar gidan bata girki ne?’
PAGE 149
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Ya karasa kusa da ita yana kokarin kama dogon gashinta da take tajewa yana cewa ‘Ki bar wannan maganar, ki zo muje na nuna miki kitchen dinki sai ki samar mana ruwan zafi mu karya. Idan kuma akwai inda zaki iya yiwo mana order a kawo nan da awa daya haka to sai na tura kudin.’
Ta jijjiga kai ‘Gaskiya babu, sai dai ko na rana don wallahi kwana bakwai din nan sai na yi su ba tare da na dora tukunya ba. Don ni abinda na sani matar gida ko ‘yar gwal ce idan aka yi amarya ita take girki kafin a zauna a raba.
Haka yayi ta bata hakuri yana lallabata, daga karshe ta shirya suka sauko parlor dinta ta dafa musu ruwan zafi sanna ya debo kwai ta soya musu.
Wajen 12pm ya hadasu a parlor dinsa yayi musu introduction; ita naja amarya sai muzurai takeyi tana wata yanga, ita kuwa khadeeja cike da walwala tayi mata maraba suka gaisa babu laifi. Ya sanar da su idan an kwana bakwai zasu raba kwana kowacce kwana biyu.
Ba karamin mamakin Khadeeja yayi ba, ko da yake wannan ba bakon abu bane a wajensa. Tayi masa ra