NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 62 of 105

A nan ya shigo ya sameta tana zaune a kan dadduma tana gyangyadi; kallo daya tayi masa taji zuciyarta ta sake komawa cikin damuwa wadda ta fi ta da. Sai wani faman yage baki yake yana muzurai a lokaci guda; a sanin da tayi masa ta san murnace da doki yakeyi na amarya kuma yana kokarin tabbatarwa ita din bata kawo masa cikas ba. Nan da nan ta danne duk wata damuwa da take ranta ta kakalo murmushi tayi masa sannu da zuwa. A tsaye ya amsa yayi mata bangajiyar biki sannan yace ‘Um ni bari naje, na ga kema bacci kike ji. In ya so da safe na shigo da kanwar taki ku gaisa.’ ‘To Allah ya kai mu.’ PAGE 145 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ya juya ya fice ya rufo mata kofa. Ta ji dadi sosai da ya sanar da ita ba zai shigo da atarsa a wannan daren ba, domin gaba daya a gajiye take. Ba jikinta ba har ruhinta ma ji take ya gaji, fatanta kawai wadannan kwanakin su wuce ko kuma ma ta farka taga mafarki takeyi. Taga rayuwarsu ta dawo kamar yanda take a farkon aurensu; ko da yake a farkon auren ma babu wani abun kirki da zata dorar; kamar dai gara ma tace rayuwarsu ta dawo yanda ake kafin aure. Sai da bacci ya fara dibanta sannan ta tashi ta kwanta a kan ganto ta kashe fitila. ……… Cike da doki ya shiga dakin amaryarsa rike da ledarsa ta kayan ciye-ciye; tana zaune a can a kuryar gado. Ko da ace ta amsa sallamarsa to shi dai bai ji ba, amma ya riga ya san yanda amare suke. Har inda take ya karasa ya sameta bayan ya ajiye ledar hannunsa a kan mudubi. Ga mamakinsa bayan ya daga fuskarta kuka takeyi sosai da hawaye kamar wadda aka yiwa auren dole, don haka nan take ya shiga aikin lallashi. Sai da suka kusan minti talatin sanna ya samu ta goge hawayen ta saurareshi. ‘Wai me ya faru ne kike ta faman kuka haka sai kace wadda aka yiwa auren dole?’ Ta balla masa harara ta dauke kai sannan tace ‘Ni da ka kawo na zabi dakin da nake so a sama kusa da nka dakin shine za a kawoni a ajiye ni a nan, ka sa ina nema nayi musu da masu kawoni.’ Ya yi murmushin yake ya sake kamo hannunta wanda ta riga ta fizge yana cewa ‘Haba ke kuwa? Ai na zata da suka zo kafi sun gaya miki.’ Ta zumbura baki ‘Ni babu wanda ya gaya min, sai da aka kawo ni kawai naga an ajiyeni a kofar gida kamar wata wadda ba a so zuwanta ba.’ Nan ya shiga faman bata hakuri da bayani tana faman fizgewa har dai ya samu ta sauko. Ta kalleshi tace ‘Amma gaskiya ni fa ba zan zauna a nan ba, matarka da yaranka da kai kuna sama. Kenan fa duk ranar da ba kwana na ba ni kadai ce a kasa bakin kofa. Gaskiya wannan tysarin bai yi min ba, ko dai a bani sama ko kuma gaskiya ka nema min wani gidan. Wannan ai duk wanda ma ya zo ya san matsayina.’ PAGE 146 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ya kara matsawa ya janyota jikinsa ‘Kin ga, kada wannan ya dameki. Ko da ban kama wani gidan ba zaki iya komawa saman in ya so ko ni sai na dawo kasan ku kuma gaba daya kuyi zamanku a saman.’ ‘Ni dai ba haka nace ba, amma gaskiya ka cika min alkawari don ba zan yarda wata tana sama ni ina kasa ba.’ Haka yayi ta lallabata har ya samu ta amince masa. Ya tattara musu kayansu suka wuce sama dakinsu wanda da farko ta so ta ki zuwa, sai kuma ta tuna gara itama ta hau saman ta ga yanda Khadeejan zata yi. …….. Da yake dama Hammad bai saba barinta baccin safe ba yau din ma tun wajen 6am ya tashesu, bata bude dakin ba saida tayi wanka shima ta shirya shi. Ta riga ta ji motsinsu tun dare don haka ta san a dakin Mustaphan suka kwana. tana fitowa ta taso Hafsa suka shiga kitchen. Ya siyo burodi kamar yanda ya saba duk dare, don haka nan da nan ta soyawa kowa kwai ta hada kayan shayi tsaf ta bawa hafsa ta sauko da shi kasa. Kafin karfe takwasa ta jera komai da suke bukata ita da yara na breakfast a parlor din kasa. Tana shirin hawowa bene Hafsa ta biyota da wayarta ta mika mata tana ringing. Tana dubawa taga Baffa ne. Bayan sun gaisa ya kara yi mata nasiha sanna yace mata nan da awa daya Nabeela ta shirya Ahmad zai zo ya dauketa. Bata ji wata damuwa ba saboda dama ta san halin Baffa, ba tare da bata lokaci ba ta taso Nabila ta sanar da ita. Nan da nan ta hada kayanta don ko wanka cewa tayi idan taje gida tayi abunta, haka ma breakfast cewa tayi idan taje gida ta ci kosai don tabbatar yau lahadi kosai Mommy tayi. Wajen 9am suna zaune a dining table ita da yara in banda Afaf wadda bata tashi ba ko kuma bata fito daga dakinsu ba. Breakfast sukeyi suna ta hirarrakinsu Shukra sai labari take basu suna dariya gaba daya. Da sallama ya sauko daga benen ya karasa gaba table din yana cewa ‘Ina can ina nemanki a dakinki ashe kina nan ke da yara kuna ta jin dadinku.’ Tayi murmushi ta kwara da kai. Ita da yaran duka suka gaishehi, bayan ya amsa ya dubeta yace ‘Idan kun gama cin abincin ki zo ki bani nawa breakfast din ni da kanwarki.’ PAGE 147 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Tayi murmushin yake tace ‘Da yake mu ma brea
🏠