uko amarya sannan suka tafi dauko amarya.
Hak ta yi sallar magriba zuciyarta tana dukan uku-uku; ta rsa ma abinda yake bata mata ran. Tabbas tana kishi to amma ta fi tsoron rashin adalcin da take ji a jikinta Mustapha zai shimfida; amma tana addu’a kuma za zata fasa ba don ta san tabbas Allah ne gatanta.
Wajen 8:30pm aka shigo da amarya, nan da nan gida ya dau guda mata na ta shewa. A lokaci guda kuma bugun zuciyar Khadeeja ya kara gudu. Tana zaune a kan kafet kusa da Hajia; duk su Yaya Jidda suka mike suna tarbar amaya, aka budawa wadanda suka riko amarya suka karasa gaban Hajia wadda take hakimce a kan 3-seater. Aka zaunar da amarya a gaban Hajia, mata suka cigaba da zabga guda.
Sai da hayaniya ta lafa sannan aka gaisa da masu kawo amarya, suka mikata hannun Hajia. Hajia tace ‘Ma sha Allah, Allah ya sa wannan aure har aljannah. Wannan ai ‘yar uwarta za a bawa ita ba ni ba, ina Khadeejan ne da fa tana nan zaune kusa da ni.’
Wadda take zaune kusa da Khadeejan tace ‘Gata nan fa.’
Mutane ne suka zauna a gabanta suka kareta da aka shigo da amaryar; nan da nan aka buda. Hajiya ta mika hannu yayinda Khadeejan ta matso tna cewa ‘Zo Khadeeja ga kanwarki an kawo miki.’
PAGE 143
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Ta sunkuyar da kanta tana duban cinyarta domin tana tsoron kada idanuwanta su bada ita ta hanyar tunkuda awaye a daidai wannan lokacin. Hajia ta kama hannunta sanna ta kamo hannun Naja ta dora ta hada ta rike tana kallon Khadeejan tana cewa ‘Ga amanar kanwarki nan, ki riketa amana ku zauna lafiya ku samarwa da mijinku nutsuwa. Allah ya hada kayuwanku.’
Mata suka kaure da amshi ‘Amin. Amin.’
Wata cikin iyayen amaryar ta karbe ta cigaba ‘Eh gata nan amana, a yi hakuri uwargida sarautar mata ku zauna cikin amincin Allah domin kayan Alah na annabi ne.’
Aka sake kaurewa da guda.
So take ta zare hannunta amma hajia bata basu dama ba; bugun zucuyarta kara sauri yake yayinda take jin hanunta kamar ta rike wuta. Kokari take ta dafe bakinta saboda kada abinda yake zuciyarta ya fito; Amana! Ita za a bawa amanar matar Mustapha? Ina ruwanta da ita? Ko sunyi mantuwa ne? shi da yaga zai iya da amanar ai yayi gammo ya dauko. Don me zasu ce ita aka bawa amana? Tabbas wanna amana ce da bata karba ba kuma ba zata taba iya karba ba.
Sai da aka gama addu’oi sannan Hajia ta saki hannuwansu, cikin dabara Khadeeja ta faki ido ta goge kwallar da ta taru a kwarmin idonta.
Ba dadewa kuma aka fara mikewa aka kama hannun amarya aka nufi dakinta, a haka ne Khadeeja ta samu ta sulale ta haye sama, yayinda su kuma matan suka bi bayan amarya.
Haka ta koma cikin su Yaya Mama ta cigaba da dagewa, su kuma suna ta bata baki da nasiha. Wajen 9pm gayya ta fara watsewa, aka kirawota ta yi sallama da Hajia, ba dadewa kuma su Yaya Mama suma suka yi mata sallama suka barta ita da Nabeela.
Tana zaune a gefen gadonta tana jiyo yara wajen 11pm suka hawo saman, gaba dayansu sai da suka leka dakinta suka yi mata sai da safe amma banda Afaf, suka wuce dakinsu inda suke kwana tare da Hafsa. Basu dade ba kuma Nabila ta fito daga dakin bakin da yake saman ta turo kofar dakin a hankali ta shiga, ta wuce Khadeejan a gefen gadon ta zagaya ta kwantar da Hammad a gafe ta lullubeshi. Ta zagayo ta zauna a kusa da Khadeejan, bata motsa ba kamar ma bata san an zauna a kusa da ita ba.
PAGE 144
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Ta mika hannu ta dafa nata hannun da yake kan cinyarta tana kallon fuskarta tana cewa ‘Yaya Khadeeja ga Hammad fa na kwantar miki da shi.’
Ta kalleta suka hada ido, ba tare da tace komai ba ta sake kawar da idonta saboda ta tokare hawayen da suke neman kwace mata. Nabila ta dan matsa hannunta tana cewa ‘Ya Khadeeja.’
Kafin tace wani abu hawayen ya fara bin idonta, gaba daya ta sakesu saboda yanda take faman rikesu tana jin kamar an dora mata dakon wani kaya mai nauyi. Gaba daya ta fada jikin Nabeela wadda ta rungumeta gaba daya suka sa kuka. Ita Nabeela auren ma gaba daya ya kara bata tsoro’ kuma ta tabbatar ko da wanne lokaci za a iya daura nata auren; tunda da ba don Ahmad ya tafi UK karo karatu ba da tuni ta shekara a daki. Ita kuma Khadeeja gaba daya komai ma ya tsaya mata; tana dai fatan Allah ya sa Mustapha ya zama mai adalci.
A hankali suka fara lafawa, Khadeeja ta zare jikinta ta kalli Nabeela. Suna hada ido suka tuntsire da dariya duk da hawayen da suke fuskokinsu. Suka rike hannun juna suna murmushi. Khadeeja ta dubeta tace ‘Sorry.’
Itama murmushin tayi mata tana cewa ‘Its’s ok, you will be fine in sha allah. Komai zai wuce kamar ba ayi ba.’
Murmushi ta sake mayar mata sanna tace ‘Kije ki kwanta, na san yanzu Abbansu zai shigo.’
Ta sake rungumeta sannan tayi mata sallama ta fice ta rufe mata kofa.
Ba tare da bata lokaci ba ta mike ta shiga bandaki inda ta yiwo wanka sannan ta fito da alwala, ta shirya ta sa kayan bacinta sannan ta kabbara sallar isha’i.