gaskiya, don gaskiya hakuri kawai yake yi da ita ba tun yau ba. Da bakinsa ya gaya min babu ragowar kaunarta a zuciyarsa…..’
‘Ke rabu da shi, namiji ai munafiki ne. za dai muyi maganinsa tunda mun ga kamun ludayinta.’ Ta katseta tana yarfe hannuwa.
PAGE 140
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Ranar daurin aure tun da sassafe baki suka fara zuwa gidan, zuwan nasu ma sai ya fi mata sauki tunda ya bata dama ta baro Mustapha a sama ta taho wajen bakin. Ba zata iya tsayawa a inda yake ba yana ta faman walwala yana kaiwa da kawowa yana kwalliya, sai ta ga kamar yana yi ne don ya bata haushi. Don haka taji dadi sosai da aka ce mata Yaya Jidda ta zo da mutane.
Nan ta sauko suka gaisa, ta bude musu dakin baki tunda dama a daya parlor din suka sauka wanda ba na amarya ba. Sosai Yaya Jiddan ta so su hau sama amma sam Khadeeja taki bada fuska, don haka suka hakura suka baje zugarsu a nan kasan. Duk wani abu da suke bukata na cefanensu sun taho da shi da mayan tukwanensu, shi kansa Mustaphan bai san a nan zasu yi girkin ba da ya biya an girka musu don baya son a bata gidan nan. Amma haka yana ji yana gani kafin ma ya sauko an sauke kayan aiki an hau kokarin hura wuta; a cewar Yaya Jidda sun bayar a yi musu tuwon shinkafa da masa da shinkafa amma masu yi miyarsu bata dadai don haka su zasu girka tasu miyar. Nan da nan ya ja motarsa ya fice daga gidan suka tafi daurin aure.
Tunda Mustapha ya fita ta dauki Hammad ta haye sama, suka zauna da Nabila wadda dama bata sauko ba ma balle ta ga kalarsu. Hafsa mai aikinta dai ita dole ta zauna ana komai da ita, sannan ga su Afaf wadanda tuni suka shiga cikin dangi ana ta rawar kai.
Can kusan la’asar su Yaya Mama suka zo ita da cousins dinsu mutum biyu da kuma kannen Mommy su biyu. Bayan sun gaisa da Yaya Jidda a parlor din kasa kai tsaye suka haye sama.
Basu dade da hayewa ba kuma Hajia mahaifiyar Mustaphan ta iso da tata zugar, nan da nan gida ya cika ana ta kaiwa da kawowa.
Bayan an gaggaisa Hajia ta dubi Yaya Jidda tace ‘Ina Khadeejan ne? Ban ganta ba.’
Inna Ramla tayi sauri ta amsa kafih Yaya Jidan tace wani abu ‘A’a suna sama benen nan fa ita da ‘yanuwanta, benen da ‘yan gidan ma ban ga suna hawansa ba tunda duk gasu nan tare da mu.’
Ta sake duban Yaya Jidda tace ‘Ban gane tana sama ba.’
Ta tabe baki ‘Toh haka muka gani, tana saman ita da ‘yan uwanta.’
PAGE 141
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Kafin tace wani abu Khadeejan ta sauko sauko parlor din da sallama; Shukra ce ta hau ta gaya mata zuwan Hajia shine tayi sauri ta sauko saboda kada tayi laifi.
Ta ratsa mutanen har gaban Hajia ta tsuguna ta gaisheta cikin girmamawa sanna tayi mata Allah ya sanya alkhairi. Ta dubi mutanen duk suka gaggaisa tana kama sunan wadanda ta sani. Har ta mike Hajia tace ‘Ina Mommyn naki, bata zo ba?’
Tace ‘Eh, bata zo ba, su Yaya Mama ne kawai suka zo.’
‘To madalla.’
Ta mike ta fice tsakar gidan suka gaggaisa da mutanen dake zazzaune, ta kalli wajen da su Yaya Jidda suka yi aikinsu yanda yayi kace-kace ta dauke kai. Har ta juya zata koma ciki Habib ya turo gate ya shiga, daga inda yake ya kirawo sunanta ‘Anti.’
Ta tsaya ta juyo ‘Yaya Habib, ina ka shiga ne tun dazu Shukra take nemanka.’
‘Ina nan Anti, wajen abokina naje. Yanzu na wallahi yunwa nake ji, abinci zaki bamu.’
Tace ‘To ai Anti Jidda zaka yiwa magana ga abinci nan an dafa.’
Ya shafa kai yana cewa ‘Anti ai na gaya mata, tuwo ne fa da masa Anti don Allah ni dai ki bani abinci.’
Tayi dariya don ta san tabbas Habib baya cin tuwo da masa da ma abincin gargajiya da yawa, tace ‘Kaje sama wajen Anti Nabeela ta zuba maka.’
Har ya wuce yace ‘Ni da abokaina Anti?’
‘Eh, ka gaya mata ko ku nawa ne.’
Bai jima da hayewa ba itama ta bi bayansa, kafin taje ya dauko flask Nabeela ta zuba masa shinkafa da kaza ga coleslawa da sauce din dankalin bature wanda duk a nan saman suka dafa shi tunda basu da yawa. Ya dauko kwanukan ya sauko ya fice.
Haka aka yi ta hada-hada ana kaiwa da kawowa. Sai dai zuwan Hajia ya sa babu yanda Khadeeja zata yi dole ta zauna a kasa a yi da ita, don haka Yaya Mama da kuma Anti Innani suka sauko suka gaida Hajia suma suka zauna don tayata zama.
PAGE 142
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Bin mutane kawai takeyi da kallo zuciyarta tana kuna; ji take a ranta kamar da za a bude zuciyarta to da za a tara tana turirisaboda zafin da take ji. Fuskokinsu take kallo daya bayan daya, musamman Hajia wadda ake ta yi mata Allah ya sanya alkhairi ana barka da arziki tana amsawa kamar wadda aka yiwa bushara da kujerar Makka. Haka tacigaba da zama a cikinsu tana jin kamar ta ruga da gudu; sai dai loakci zuwa lokaci ta kan tashi kamar mai duba wani abu ta haye sama, idan ta ja numfashi ta share kwalla sai ta dawo. Haka suka yi ta yi har gefin magriba; abokan ango suka zo da motaci suka debi yan da