ukata saboda taryar baki ko?’
Ba tare da ta daina cin abncinta ba tace ‘Eh. Ni kam mai ai don dai ka hana ne da sai nayi tafiyata wajen Mommy idan aka kawota aka tafi sai na dawo da daddare ko ma da safe.’
‘No, don Allah ki bar wannan maganar. Ai ya kamata dai ace a samu a karbi bakin nan cikin mutunci.’
‘Um.’
Suka cigaba da cin abincinsu, jimawa kadan yace ‘Hajia ma tace a nan zasu zo suyi biki ranar lahadin, in ya so sai su tsaya su karbi amarya sannan su tafi.’
Ta kalleshi suka hada ido sannan ta kawar da kanta, wani malolo ya zo ya toare mata makogoro; su Hajia zasuyi biki a nan? Saboda suna murna za ayi mata kishiya ko me? Ta dauki kofin shayinia mai zafi ta kurba da fatan zafin shayin zai tafiyar mata da abinda ya tokare mata makogoro amma hakan bai samu ba. Ta kalleshi a jigace tace ‘Ka ga shikenan sai na tafi gidan Mommy ko? Tunda ka ga masu karbar amarya zasu zo.’
Ya dan zaro ido yana cewa ‘Haba dai! Hakan kuma ai bai yi tsari ba, kina matar gida kuma azo biki gidan ba kya nan. Ko ba haka ba ma kin san Hajia zata ga kamar kin rainata ne shi yasa zaki tafi ki barsu su kadai suyi bikin. Please kiyi hakuri kawai saboda kada abun ya zama wata fitna kuma. Kin ji?’
Ta daga kai tana cewa ‘Uh.’
‘Yauwa, please kiyi hakuri a gama taron nan ba tare da wata matsala ba.’
Tayi gajeran murmushi tace ‘In sha Allah.’
Ya ture kwanon bayan ya kurbe dan ragowar shayinsa sannan yace ‘Zan saka miki kudi a account dinki saboda na san zaki iya bukatar wani abun ko don baki. Akwai ruwa da lemo wanda zan kawo, abincin kuma dama tunda kika ce ba zaki yi a nan ba na bayar da kudin don haka su Hajia zasu taho da shi.’
‘Ok.’
‘Idan kuma da bukata zaki iya yin wani abincin a nan ko da kadan ne.’
‘Ok, babu damuwa.’
Ya mike ya shige dakin domin ya karasa shiryawa. Nan take itama ta ture kwanon indomie din ta mike ta haye sama. Kuka take son tayi ko zata ji sanyi a ranta, amma bata so ta bata lokaci musamman da yake yana jiranta kuma tare zasu fita.
PAGE 136
MIJIN MARIGAYIYA
A Huasa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Haka tayi sauri ta shirya suka sauko tare, ta karbi Hammad a wajen Anti Binta suka fice suka bar Anti Binta Hafsu wadda kanwar Rashida ce aka kawo mata bayan an yi auren Rashidan tun kafin ta haifi Hammad.
Haka suka zauna a mota babu wanda yake magana da dan uwansa; ya riga ya kula da yanda take nema ta tayar masa da fitna a wajen bikin nan amma ba zai barta ba. Sosai ya ji dadi da Hajia tace zasu zo nan suyi biki don baya so ta bayar da matsala idan an kawo amarya, amma ya san tunda Hajia tana nan babu wata matsala da zata basu. Haka yaje ya ajiyeta a gidansu sannan ya wuce.
………
Tana shiga gidan ta sami Ahmad a parlor yana shan shayi; nan da nan ya mike ya karbi Hammad daga hannunta.
‘Ina Mommy?’ ta tambaya bayan ta amsa gaisuwar da yake mata.
‘Tana dakin Baffa.’
Ba tare da ta bashi amsa ba ta bar masa Hammad ta wuce ta nufi dakin.
A zaune ta hango Mommy a kan dadduma ta mike kafa da waya a hannunta, ta jefar da mayafinta ta karasa gaba daya ta fada jikin Mommy ta rushe da kuka.
‘Inna lillahi wa Inna ilaihi raji’un! Khadeeja me ya faru? Ina Hammad din?’ Mommy ta tambaya cikin tashin hankali.
Da kyar ta bude baki tace ‘Yana hannun Ahmad.’
Ita kanta saida taji ajiyar zuciyar da Mommy din tayi, sanna ta cigaba ‘To me ya faru kike wannan kukan haka? Ko Mustaphan sakinki yayi ne?’
Ta jijjiga kai alamar a’a ba tare da ta dago ba, ta cigaba da kukanta. Kawai sai Mommy ta hakura da tambayar ta zuba mata ido, a hankali ta daga hannunta tana shafa kanta; ta dai san da maganar saura kwana uku a daurawa Mustapha aure don haka watakila wani abun yayi mata wanda ya sosa mata rai shine ta taho nan tazo tana wannan kukan. Saida ta dauki loakci tana wannan kukan sannan ta dan numfasa ta dago ta kalli Mommy, suna hada ido kuma sai ta sake fashewa da kuka.
Cikin sheshekar kuka tace ‘Mommy ba zan iya ba, ba zan iya ba Mommy.’
Ta dago fuskarta tana share mata hawayen tace ‘Menene ba zaki iya ba Khadeeja?’
PAGE 137
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Ta tsagaita da kukan sai dai hawayenta ya kasa daina fita; ta sa bayan hannunta ta goge hawayen ta kalli Mommy suka hada ido na dan lokaci. Ta kawar da kanta tace ‘Mommy ban san me Mustapha yake so da ni ba. Bayan ya gama raina min hankali lokacin da yana neman aure yanzu kuma duk da ban bashi matsala ba amma ba zai barni na zauna lafiya ba.’
Ta share mata hawaye tana cewa ‘Me yayi miki kuma.’
‘Mommy nace masa ina so ranar da za akawo amarya na taho nan idan sun gama kaita sai na koma ya hana ni, na hakura nace zan zauna amma ba zan yi taro ba; su kawo amaryarsu kawai su tafi. Da farko har ya yarda amma yau yake gaya min wai babarsa tace zata zo a nan gidan namu zata yi biki, kuma yace ba zan tafi na barsu ba. Mommy so suke bakin ciki ya kasheni? Dansu zai yi min kishiya