r dariya tace ‘Oh, ka san fa na dauka kai ka gaya min; ashe ba kai bane. Ina jin dai a cikin wadanda ka gayawa ne kace kada su gaya min aka sami wani ya gaya min.’
Ya sunkuyar da kai domin ya kasa hada ido da ita; wato duk wannan tsawon lokacin ashe kallonshi kawai takeyi duk abinda yake boyewa ta sani. Ba karamin mamaki yayi ba. Kafin yace wani abu suka jiyo kukan Hammad daga cikin gidan, don haka ta dubeshi tace ‘ka ji yarona can yana kuka, bari naje na gani.’
Ta fice ba tare da ta saurari amsarshi ba.
PAGE 133
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Tana fitowa daga dakin ustaphan ta tarar da Anti Binta a parlor tana ta jijjiga Hammad, tun kafin ta karasa wajensu tace ‘Yunwa yake ji, zo ki bashi ya sha.’
Ta karbeshi ta shige dakinta Anti Binta tana biye da ita. Haka ta daure ta hadiye malolon da ya tokare mata makogoro har ta gama bashi nono suna hira da Anti Binta. Sai da ya sha ya koshi sannan ta mikawa Anti Binta shi tana cewa ‘Gashi Anti Binta, bandaki nake son shiga.’
Ta karbeshi ta mike tana cewa ‘To muna can dakin yara muna hira da mutuniyata.’
Ta fice ta ja mata kofa sannan ta mike ta shige bandakin don ta san idan dai tana cikin dakin nan wani sai ya zo nemanta, idan kuma ta rufe da mukulli za ayi ta fama tambaya. Tana shiga bandakin ta turo kofar ta jingina a jikin kofar, take hawayen da take rikewa suka kwace kamar an kunna famfo. Ta hada tafukan hannayenta ta rufe fuskarta tana jijjiga kai, saboda tsabar takurar da zuciyarta tayi har wani daci take ji a bakinta. Yaushe Mustapha ya raina ta haka? Wannan ma ya fi karfin raina ya koma wulakanci. To me yasa yayi mata haka? Daman can baya sonta ne ko kuwa son da yake mata ne ya kare? Bata taba tunanin zata auri miji ta zauna ita kadai ba amma dai ta dauka idan ka auri mutum zai cigaba da girmamaka yana ganin mutuncinka har karshen tarayyarku. A halin yanzu ta rasa wanne zatayi; murna ta haihu itama ta sami yaro ko kuwa jaje zata yiwa kanta tunda ko babu komai wannan yaron da ta haifa zai karawa alakarta da Mustapha tsawon rai. Bata san tsawon lokacin da zata iya dauka tana jure wulakanci irin wannan da Mustapha yake mata ba, amma dai ta san tabbas ba zata iya jurewa har abada ba. Gashi shi ba dukanta yake ko zagi ba, wani irin wulakanci ne yake mata yana nuna cewa komai normal ne, kuma a mafi yawancin lokuta ma idan tayi magana sai a dinga nuna mata haka maza suke. Domin kowa ce mata kawai yake idan dai namiji ne bata ga komai ba. Ta barwa Allah al’amarinta kuma zata jira su tare ta ga yanda yanayin zaman zai kama; amma tabbas idan aka cigaba a haka bata jin zata iya zama da Mustapha.
PAGE 134
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
zuwa yanzu kuma duk wasu alamu sun nuna mata cewa ba zai taba yi mata adalci ba ita da Naja, kamar ma dai yanzu ne yayi aure na soyayya wanda yake sa ran zai more rayuwarsa a ciki; tunda ta gama yi musu wahala ta raini yaransa lokacin da suke tsananin bukatar uwa. Yanzu sun girma sun zama mutane don haka sai ya aure wadda yake so ta zo su more rayuwarsu ita kuma a mayar da ita samiyar ware.
A hankali ta zame a jikin kofar ta zauna ta sake fashewa da kuka. Sai da tayi mai isarta sannan ta bawa kanta hakuri ta wanko fuskarta ta fito daga bandakin.
……..
Duk yanda take cikin damuwa da zarar Mustapha yana waje to sai ta shiga walwalarta da yara, yayinda shi kuma duk wasu shirye-shiryensa na tarbar amarya ne. har ta kai baya iya boye murnarsa; shi da yara kullum hirarsu ta Anti Naja ce. Musamman Afaf wadda zuwa yanzu kusan gaisuwa ce kawai take hadata da Khadeeja.
Lafiya suka tare a sabon gida kuma kamar yanda ta zabi dakin sama haka ya hakura ya bata dakin saman; duk da daga baya yayi nadamar hakan. Domin da ace ya san ta riga ta san da maganat aurensa to da tabbas zai gaya mata amarya zai saka a sama. Sai dai a lokacin tunaninsa bata san da maganar auren ba kuma boye mata yake son ya cigaba da yi.
Tsaf ta gyara dakinta da parlor, dakin su Afaf kuwa tunda taga ra’ayoyinta suna cin karo na da Afaf kuma tana nema tayi mata rashin kunya sai ta hakura. Sosai dakinta yayi kyau, ta tsara musu komai nasu ita da Hammad, don Baffanta ma da Mommy sai da suka kara mata kudi tayi sayayya.
Sati yana zagayowa kuma aka shiga hidimar bikinsa.
Babu yanda bata yi da Mustapha ba a kan ita bata so ayi mata taro amma ya ki amincewa; domin yace Hajia tace dangi basu san sabon gida ba don haka zasu zo su karbi amarya sannan suga gida.
……..
Tun dare ta sanar da shi cewa idan gari ya waye zata bi ‘yan makaranta taje gida wajen Mommy, kuma ba tare da wani musu ba ya amsa.
Bayan ya kai ‘yan makaranta ya dawo suka zauna tare a parlor din sama suna cin abinci yayinda Hammad yake hannun Rashida. Shiru suke cin abincin babu wanda yake magana, kamar ma dai basa cikin walwala.
PAGE 135
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Ya ajiye cokalin dake hannunsa yace ‘Kin ce babu wani abu da kuke b