h ya sa dai ba mai wahaka bane?’
Ta dan yi gajeran murmushi tace ‘Smin ya Allah.’
Suka yi shiru na dan lokaci, ya dubeta yace ‘Wai ya naga duk kin yi wani shiru ne? kamar ba abin nema ne ya samu ba?’
Ta kawar da kai tana murmushin yake tace ‘Bana jin dadi ne, bacci ma nake ji.’
Ta kwantar da kanta a jikin kujerar motar ta rufe ido, don haka shima ya kyaleta ya mayar da hankali a wajen tukinsa.
……
A haka Khadeeja ta dage ta cigaba da mu’amalarta tana yin duk wata hidima da ta saba. Ko a wanne yanayi ta tashi haka take daurewa tayi duk wata hidimarta don bata shirya drama da Mustapha ba. Ta riga ta san idan dai tana numfashi a gidan nan to duk wata hidima da matar gida take yi ba yafe mata zai yi ba; don haka ta daure ta cigaba da dagewa tana yi. Musamman da yake duk wani aiki da ta saba yi a gidan ta riga ta koyawa Rashida kuma ta iya sosai, gashi yarinyar bata da kyashi ko daya, don haka abubuwa suka zo mata da sauki sosai.
PAGE 126
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Sai dai fargabarta daya iyayen Rashida suna maganar ko da wane lokaci za a iya zuwa a dauki Rashida saboda aurenta ya kusa; duk da dai an ce za a kawo mata kanwarta to amma ta san akwai aiki.
Haka ta cigaba da rayuwarta tana goyon cikinta.
A hankali ta fahimci lokutan da yake zuwa zance wajen naja, kuma da yake shi yake kaita makaranta da ta shiga motar take gane Naja ta fita a motar ko kuma sun fita tare.
……..
Daidai lokacin da zasu fara jarrabawar karshe a lokacin cikinta ya shiga wata na takwas; ga hidimar gida, ga karatu kuma gashi tana kokarin hada project dinta. A dai-dai lokacin ne kuma Mustapha ya gama gyara gidansa wanda yake fatan da zarar sun koma za ayi bikinsa da Naja. Sau biyu yana kaisu gidan ita da yara, kuma duka zuwa biyun sai ta tambayeshi ko aure zai yi ne yake yin gidan kamar d zubin mata biyu. Amma duk lokacin da ta tambaya sai yace mata ko da zai yi auren to ba yanzu ba; ta rasa gane dalilin da yasa yake son boye mata aurensa da Naja. Don haka ma ta daina tambayarsa gaba daya.
Ranar asabar ce kuma tun dare ya sanar da ita da safe yara su shirya zai fita dasu, don haka tun wajen tara na safe ta bayan da suka ci abinci ta sallamesu ta koma ta kwanta. Ya dai ce mata gidan Hajia zasu je kuma suma yaran haka suka gaya mata; amma a ‘yan kwanakin nan yana yawan fita da yaran ranar da babu aiki yace wajen Hajia zai kaisu. Ta riga ta gane wajen Naja yake kaisu, sai dai bata ga dalilin da zai sa tayi masa magana ba tunda ‘yayansa ne sannan kuma gaya musu da yake suce mata gidan Hajia suka je su yake cutarwa ta hanyar koya musu karya.
Gaba dayansu suka fice banda Habib, wanda dama ya riga ya saba duk lokacin da za suyi wannan fitar shi baya binsu. A gida yake zama tare da Khadeejan da Rashida.
Sai wajen karfe biyar na yamma sannan suka dawo, lokacin ta riga ta gamamabincin dare ta zuba a flask tana kwance a daki. A dakinta yaran suka sameta tana kwance tana hutawa, suka sanar da ita sun dawo. Shukra kuwa sai ta wuce ta haye gadon ta kwanta kusa da ita tana cewa ‘Bacci kike yi Anti?’
PAGE 127
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Ta dan matsa jikinta tana gyara kwanciya, Khadeejan ta dan gyara kwanciyarta tana kawar da Shukran daga cikinta. Tayi dariya tana cewa ‘Na matsa ko Anti, kada na lotsewa kanina hanci.’
Tayi dariya saboda itace ta saba gaya mata hakan a duk lokacin da take son kwanciya a jikinta tunda cikin ya fara girma; domin Shukra yarinya ce mai son jikin tsiya kuma ta samu Khadeejna bata tureta. Tace ‘Yauwa, ashe dai kin gane. Kada a dinga ce miki yayar mai lotsttsen hanci.’
Suka yi dariya gaba daya; Shukra ta ci gaba da wasa da hannun Khadeejan guda daya yayinda Khadeejan take rike da daya waya a daya hannun tana chatting. Jimawa kadan cike da damuwa tace ‘Anti.’
‘Umm.’ Ta amsa ba tare da ta bar abinda take yi ba.
Tace ‘Gaskiya ni ba zan koma wajen Anti Naja ba, a wajenki zan zauna ko?’
Ta ajiye wayar tace ‘To wa yace zaki koma wajen Anti Naja kuma? Ai muna nan tare, ko ba gamu ba a gidanmu.’
Cike da damuwa tace ‘Ai itama tace aurota Abbanmu zai yi ta dawo gidanmu. Amma sai mun koma sabon gida. Shine yau da muka je wajenta take cewa Yaya Afaf idan ta tare duk wajenta zamu koma. Gaskiya ni dai ba zan koma ba ko?’
Ta dan yi shiru tunani yana nema ya birkita kwakwalwarta; duk da bai gaya mata ba ta san yana kai yaransa wajen Naja, amma maganganun da Najan take gayawa yaran basa kama da maganganun da ya dace a gaya musu a daidai wannan lokacin. Sai dai ta san babu yanda zata yi tunda shi ya bata dama.
‘Anti.’ Muryar Shukra ta katseta tana kiran sunanta.
Bayan ta amsa Shukran ta cigaba cikin damuwa ‘Tace saura wata biyu ta tare, gaskiya idan ta zo ki gaya mata ni a wajenki zan zauna ba a wajenta ba. Kuma ma na ji tana gayawa Yaya Afaf idan an koma sabongida sama take so kece a kasa, na gayawa Yaya Afaf mune a sama mu dake tace min wai da