mu shikenan.”
“I can’t wait to have you here with us Anti.”
“Soon my girl. Amma dai ta daina baki matsala ko?”
“Ta daina, tunda ta ga babu riba. Yanzu ba sosai ma take kulani ba dama ni haka nake so. Habib ne kawai sarkin rawar kai ya manne mata.”
PAGE 121
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
“Kada ki damu kwanan nan zan zo na gyara mata zama.”
Motsin da Khadeejan ta jiyo ne ya sa tayi sauri ta rufe sakinnin ta dire wayar a kan teburin da yake kusa da freezer din ta kama murfin freezer din ta daga kamar a lokacin ta rufe.
‘Anti ina wayar?’ Afaf ta fada bayan da ta karasa shigowa kitchen din.
‘Kin ganta nan a kan tebur, dauki.’
Ta karasa ta dauki wayarta ta fice ta koma parlor din.
Cikin sanyin jiki Khadeeja ta tsaya a ta jigina da freezer din ta kafa tagumi. Kusan wata takwas da suka wuce Mustapha ya kalli tsabar idon Baffa da Mommy yace musu ba auren Naja zai yi ba, amma gashi daga wadannan chats din da ta karanta yanzu har an kai kudin aure da sadaki. Wato ma Afaf ta san komai itace kawai bata san mijinta zai kara aure ba kenan; kuma kamar dai bashi ma da niyyar gaya mata. To me ta yiwa Mustapha ne? me yake tunanin zata yi a akna kara aurensa da yake boye mata? Ita dama da ya kai ta gidan da ya siya yanda taga gidan ta san sai ya kara aure, kawai dai bata zata Naja zai auro ba don kwata-kwata bata sake ganin wata alama da take nuna yana tare da Naja ba tun bayan da suka je wajen Baffa. Wato dama da take zargin Yaya Jidda ce take hure mata kunnen yara ashe Naja ce, tunda gashi nan ta gani har tana gayawa Afaf cewa zata shigo ta gyara mata zama. Ta jijjiga kai, ta goge gumin da ya fara tsattsafowa daga goshinta sannan ta tuna ce mata fa yayi nan da awa daya zasu zo.
Jikinta a sanyaye ta koma cikin gidan ta kirawo Rashida sannan suka fito suka kama aiki. Haka ta hadiye duk wani bacin rai tayi ta haba-haba da abokinsa, sai bayan sallar isha’i sannan yayi musu sallama ya tafi.
Ta san cewa ya kula da yanayinta yanda ya sauya, amma bai yi mata magana ba. Duk da dai ko da yayi mata maganar ma zata gaya masa gajiya ce kawai. Haka dai suka kwana shi yana baccinsa ita kuma Khadeeja duk lokacin da tayi juyi sai ta kalleshi tana tambayar kanta wai me tayi masa ne yake mata abubuwa kamar wata wadda aka aura ba don soyayya ba?
Haka ta hakura tayi ta danne zuciyarta har gari ya waye
PAGE 122
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Sai karfe biyu na rana take da lecture amma haka ta shirya da wuri lokacin da Mustapha ya shirya zai tafi office tace ya wuce da ita ya kaita gidan Mommy, in ya so daga can sai ta wuce makarantar ta kuma dawo gida. Haka kuwa aka yi.
Tunda ta shiga gidan Mommy ta karanta damuwa a fuskarta, ta dai kyaleta har Baffa da Nabila suka gama shirinsu suka fice. A nan parlor din inda suka barsu Mommy ta zuba mata ido na dan lokaci, har ta ji a jikinta Mommy din kallonta take. Tana juyowa kuwa suka hada ido; ta danyi dariya tace ‘Mommyy.’
Itama tayi dariyar tace ‘Ya aka yi ne? kamar dai kina da damuwa. Ko kuma ba kya jin dadi ne?’
Ta jijjiga kai tace ‘Mommy Mustapha aure zai yi.’
Ta dan zaro ido ‘Aure? Ikon Allah.’ Sai kuma ta saki fuskarta ta cigaba ‘Ko da yake wannan ba abin mamaki bane ai don haka kada ma ki sakawa kanki damuwa.’
Ta sunkuyar da kai cikin damuwa tace ‘Mommy nima ba damuwa nayi ba, kawai dai yayanyin abun ne.’
‘Ban gane ba.’
Nan ta sanar da ita wadda zai aura sannan ta sanar da ita a inda taga labarin auren da kuma irin sakonnin da Afaf take turawa Najan da kuma yanda take fama da Afaf din a ‘yan kwanakin nan.
Duk da Mommy bata yi mamaki ba amma dai ta ji babu dadi, musamman yanda Afaf ta zama ‘yar rahoton Naja. Tace ‘Ikon Allah, to shi me yasa yake boye miki auren?’
Tace ‘Wallahi ban sani ba, ko da wasa bai taba gaya min ba kuma danginsa ma babu wanda ya gaya min. Amma kin ga yaran har sun sani, tunda gashi har ana gaya musu za a zo a gyara min zama.’
‘Lallai mutum sai a barshi.’
‘Dama na gaya miki Mommy tunda naga gidan da ya saya nace miki gidan nan ba na mace daya bane, kin ga maganata ta tabbata.’
Sukayi shiru na dan lokaci, jimawa kadan Mommy tace ‘To da ce mata aka yi baki zauna daidai ba da take cewa zata gyara miki zama ko me? Amma kafin ta gyara miki zama ke ce zaki bi dare ki gyara zama ta hanyar addu’a, idan gari ya waye kuma ki dora da sadaka.’
PAGE 123
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Ta sunkuyar da kai tana koakrin boye kwallar da ta gangaro a kwarmin idonta; wannan kalmar ta za a gyara mata zama ta tsaya mata a rai. Domin dai kalma ce da zata iya daukan kowacce ma’ana. Amma kamar yanda Mommy ta fada hakan zata yi tunda ta san bata da gatan da ya wuce Allah.
Haka suka cigaba da hira Mommy tana ta bata baki kuma tana yi mata alkawarin daga nan ma zata dinga yi mata addu’a kuma da sadaka, ta tabbatar mata ba za tayi nasar