NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 51 of 105

zamu daidaita shi yasa nake son yanzu a kai kudin auren.’ Murmushin Alhaji ya kara fadi, ya dubi Hajia sannan ya dubi Mustapha yace ‘To ma sha Allahu. Wannan ai sai dai mu sa albarka kawai. Kaje ka sami babanka Safiyanu kayi masa bayanin ita yarinyar idan ya gama bincikensa ya tabbatar gidan mutunci ne ai sai suje su kai kudin. Allah ya sa albarka, Allah ya kara budi.’ Suka hada baki shi da Hajia suka ce ‘Amin.’ Hajia tace ‘To ka gayawa Khadeejan ko? Me tace?’ Ya shafa kai yana murmushi ‘Ban gaya mata ba tukunna, amma in sha Allahu zan gaya mata. So nake sai an gama magana tukunna idan ya zama saura kamar sati uku ko hudu sai na gaya mata ko don saboda gudun fitina. Kafin nan na siya gidan mun koma.’ Alhaji yace ‘Eh, to hakan ma yayi. Sai dai kuma Allah ya sa kada mata su rigaka gaya mata.’ PAGE 119 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Hajia tace ‘A’a babu wanda zai gaya mata, kayi abinka a hankali idan ka shirya ka gaya mata.’ Nan suka kare hirarrakinsu daga baya yayi musu sallama ya kama hanya. ………. Abu daya ne yake ciwa Khadeeja tuwo a kwarya rashin haihuwa, domin har yanzu tun bayan cikin da ta samu ya bare bata sake ko da batan wata ba. Gashi yanzu har sun shiga final year amma babu wani labari. Duk lokacin da tayi yunkurin zuwa asibiti Mustapha sai ya nuna halim ko in kula ko kuma yace lafiyarta kalau zata je ta fara neman fitna, don haka ta tattara ta hakura. Sai dai ta yanke kanta hukuncin cewa da zarar ta gama final exam zata je asibiti a dubata a tabbatar mata da abinda ya hanata samun ciki; ko babu komai itama tana so taga ta haifi dan cikinta. Tunda idan ta gama karatu bata san lokacin da zata sami aiki ba. Haka ta hakura ta mayar da hankali a kan karatunta tana addu’a. Zamanta da yaran Mustapha kadai ya isa ya sa ta ji tana son haihuwa; domin yanzu yaran sun girma tunda Shukra auta ma tana primary 1 yayinda Afaf take SS. Kusan gaba daya yaran yanzu ba dadinsu take ji ba, domin abinda suka ga dama sukeyi. Habib ne ma kawai wanda ya damu da rayuwarta kuma yake neman shawara a wajenta kamar uwa, amma Afaf da Nasreen ma bata san wanene yake basu shawara ba. Ta dai san duk wani abu na wulakanci da sukeyi mata da sa hannun Yaya Jidda. Ga wani mahimmanci da Musttapha yake bawa Afafa ta yanda ko da sun gama magana da Khadeejan Afaf tana iya saka shi ya canza. Duk abinda ya shafi yaran kuma ko da Khadeeja ce ta gaya masa to a karshe da Afafa din zai yi shawara. Hatta kitchen din gidan ya zama kamar na mata biyu; domin a lokuta da damam sai ta gama girka abinda kowa zai ci ta fita daga kitchen din sai Afaf ta shiga itama ta dafa abinda ta ga dama tace bata cin wanda Khadeejan ta dafa. Tayi magana har ta gaji, tunda Mustaphan ya fara nuna tana so ta takurawa Afaf ne saboda ba ita ta haifeta ba. ……… Tana kwance a dakinta tana jiyo hayaniyar yaran a parlor; Afaf ta shigo ta sameta ta mika mata waya tana cewa ‘Anti Abba ne yake waya yace yana kiran wayarki bata shiga.’ PAGE 120 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ta tashi zaune ta karba ta dan kalli wayar taga whatsapp call ne, sannan ta kara a kunnenta. Yace ‘Ina kika shiga ne anke kiran wayarki ana ta cewa not reachable?’ Tayi yar dariya tace ‘Sai dai ko idan network ne don ga wayar ma a hannuna.’ ‘Kin san Ali Ahmed ko? Abokina da muke zuwa zance tare.’ ‘Eh na san shi mana.’ ‘Yauwa da Allah shine ya shigo gari nan da kamar awa daya zamu zo gidan, me zaki iya dafa masa sai muyi dinner tare. Yana dai son tuwo’ ‘Ok, to sai ayi tuwon ai. Amma dai ka bari na duba freezer tukunna naga yawan kazarmu yada za samu kuma ayi muku peppersoup ko?’ ‘Eh, kwarai kuwa da zobo ma please. Duba idan babu kazar sai na bayar a kawo miki yanzu, rike wayar ki duba ki bani amsa.’ Ta mike ta dubi Afaf da take tsaye tana jiran wayarta ta nufi kitchen. Suna fitowa parlor Afaf din taga Nasreen ta canza channel ta mayar Disney Junior, da sauri tayi kanta tana cewa ‘Wane mara kunyan ne ya canza min channel ban gama kallo. Anti idan kin gama wayar ina nan.’ Ta shige kitceh ta barsu. Tana shiga ta karasa ta bude freezer ta duba sannan ta ce masa ‘Zata isa ma, amma dai idan zaka dawo sai ka siyo wata don gaba daya zan kwashe na dafa muku yanzun.’ Suka yi sallama ta katse wayar. Sunan da ta gani a jerin chats din kan wayar shi ya ja hankalinta ta fasa fitowa daga kitchen din tana karewa sunan kallo; Anti Naja aka rubuta da alamar zuciya ta emoji. Daga haka da take kallon hoton da yake kan sunan kuma tabbas Naja ce sakatariyar Abbansu. Ba tare da tayi wani tunani ba ta danna kan sunan ya bude mata chats din, har zata yi sama sai kuma wani sako da yake cikin jerin sakunan dake kasa ya ja hankalinta. Afaf ce ta turawa Naja sakon kamar haka “Congrats Anti, Abba ya ce min an kawo kudin auren ko?” “Eh my girl, sun kawo harda sadaki ma. Saura kawai ya gama gyaran sabon gida
🏠