a ficewa.
Ya dubi Khadeeja wadda take fitowa daga kitchen yace ‘Baki shirya ba ke, ko sai an jima zaki tafi.’
Da murmushi tace ‘No, yau bamu da lecture ba zan je ba.’
‘Ok.’
Tayi musu a dawo lafiya suka wuce.
Bayan ya dawo haka yayi ta tambayarta idan ta san zata je makaranta ta gaya masa ya jirata ya tafi da ita ya kaita; sai da ta tabbatar masa ba zata fita ba sannan ya fita ya tafi office.
…….
Washegari ranar Juma’a ce; kamar yanda ya saba yana kwance a daki bayan ya dawo daga masallaci yana rage bacci kafin a gama shirya yara ya kaisu makaranta. Wayar Khadeeja ce take ta faman ringing a dakin tana katse masa bacci, baya saon tashi don haka yayi tsaki ya gyara kwanciyarsa. Sai dai wayar da ta tsinke sai a sake bugowa; to waye ma yake kiranta da wannan safiyar bayan ko wayewa garin bai gama yi ba? Wayar tana fara ringinga a karo na uku ya mirgina ya mika hannu ya dauko wayar daga kan durowar gefen gado. Ya kallin screen din inda sunan wanda yake kiran ya bayyana “Baffa” ya karanta a fili yana watssakewa. To me yasa Baffan Khadeeja yake kiranta yanzu? Allah ya sa dai ba wani abun ne ya faru a gidan nasu ba.
Nan da nan ya sauko daga kan gadon dauke da wayar ya nufo kitchen inda Khadeejan take faman zubawa yara abinci suna tsaye kowa yana karbar nasa.
PAGE 117
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Ya mika mata wayar wadda take ringing yana cewa ‘Ki amsa Baffa ne yake ta kiranki kin baro wayar a daki.’
Tana karba ta amsa ta kara a kunnenta; yana tsaye yana kallonta yana tsoron kada ace wani abu ne ya faru a gidan nasu.
Bayan sun gama gaisawa da Baffan tace ‘A’a Baffa, ina nan ne muna shirin makaranta ni da yara.’
Daga daya bangaren Baffa yace ‘Karfe nawa ne lecture din naki Dije?’
Tace ‘Karfe takwas.’
‘Idan nazo 7:30am ai kin gama shiryawa ko?’
‘Eh Baffa.’
‘To ki shirya idan na karaso zan yi miki waya ki fito na kaiki makarantar sai na wuce office.’
Cike da girmamawa kamar wadda zata tsuguna a wajen tace ‘To Baffa na gode, Allah ya kara lafiya.’
Ta ajiye wayar bayan ya amsa, kafin tayi wani abu Mustapha yace ‘Lafiya kalau dai naga Baffa yana kiranki da safe.’
Ta mikawa Habib shayinsa da ta hada masa tana cewa ‘Uhm zai zo ya kaini school ne shine yake tambayata karfe nawa zai zo.’
Habib ya karbi shayinsa ya fice yayinda Mustaphan ya matsa kusa da ita cike da kulawa da damuwa yana cewa ‘Makaranta kuma? Ba nace zan dinga kai ki ba? Yanzu ke saboda rashin tausayi sai ki taso shi da wannan safiyar kawai don ya kai ki makaranta? Ke abu ba zai wuce a wajenki ba?’
Ta juya cikin halin ko in kula tana cewa ‘Shine ya karbi timetable dina yace zai dinga zuwa yana kaini ko? Ai a gabanka ya fada.’
‘Kuma a gabanki na bashi hakuri ai; wannan wanne kalar abin kunya ne ina nan kuma ina da abin hawa amma zaki taso Baffa ya zo ya kai ki makarnta don Allah?’
Daryace take son ta kwace mata saboda yanda duk ya muzanta kamar ma Baffa yana tsaye yana kallonsa. Kafin ta bashi amsa ya dauki wayar tata ya dannawa Baffa kira ya mika mata waya yana cewa ‘ki gaya masa zan kai ki ba sai kin yi min wulkanci ba.’
Kafin tayi magana har Baffan ya dauka, don haka ta kara a kunnenta tace ‘Um Baffa ka bari ma Abban Afaf zai kai ni makarantar.’
Yace ‘Ah, kin tabbata dai ko?’
‘Eh Baffa, gasu ma tare zamu fita gaba daya shiryawa muke.’
Ya zare wayar daga hannunta kafin ta sake magana ya kara a kunnensa cike da girmamawa yace ‘Baffa zamu tafi tare in sha Allahu, zan dinga kaita. A yi hakuri.’
PAGE 118
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid
Yace ‘To, to babu laifi. Allah yayi muku albarka.’
Ya ajiye wayar yana harararta yana cewa ‘Yanzu zan je na shirya, kema ki shirya sai mu fita gaba daya ko kuma idan na kaisu sai na dawo kafin nan kin karasa sai mu wuce.’
Tace ‘Um, ka ga babu komai fa, zaku iya tafiya ma sai na wuce kawai ba sai na gayawa Baffan ba.’
Ya kakkafeta da ido yana harararta har sai da ta sunkuyar da nata idanun, ya juya yana cewa ‘Ki shirya nace.’
Ya fice ya barta a nan.
Tayi dariya ta cigaba da aikinta.
Bata da zabi haka ta shirya suka fita tare, kuma daga wannan lokacin ya zama ko da wanne lokaci zata makaranta haka yake barin abinda yakeyi ya zo ya kaita. Sai dai idan ta gama abinda takeyi kawai sai ta hawo motar haya ta dawo.
.......
A zaune yake a parlor din Ahaji, yayinda Hajia take zaune a kusa da Alhajin. Zuwa yayi musu da labrin auren yana son ya kara don har ma yana gaya musu sati me zuwa yake so aje a kai kudin aure.
Cikin walwala Alhaji yace ‘Ai kwanaki da mukayi magana da kai da na jika shiru na zata ka fasa.’
Yayi ‘yar dariya ‘Ba fasawa nayi ba Alhaji, na dai dan tsaya ne na kara shiryawa, na gaya maka zan sayi gida ai. To dama tsayawa nayi a samo gidan, kuma yanzu an samo, cinikin ne ma bai fada ba saboda ina so su dan yi min ragi. Amma in sha Allahu ina sa ran