NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 49 of 105

hakuri Dije, kin ji.’ Ta gyada kai shi kuma ya dan numfasa sannan ya cigaba ‘Kiyi hakuri ki bi mijinki, kin ji bayanin da yayi. Kuma idan ma yace zai auri waccan yarinyar wannan bai kamata ya zama matsala ba tunda dai kin san duka wani namiji mijin mace hudu ne. kiyi hakuri ki cigaba da hidimarki kamar yanda kika saba, kin ji. Batun kaiwa makaranta kuma kinga shi ‘yayansa yake zubawa a mota yake kaisu a makaranta kuma tabbas haka ya kamata uba nagari ya kasance, don haka idan kika gama shirya masa nashi yaran kema ki shirya kiyi min waya sai na zo na kaiki tunda dai kema ‘yata ce; kai ki makaranta kuma ba bakon abu bane a wajena.’ Ya gyara zama ya dago kai a razane ‘A’a Baffa ayi hakuri ai ba sai an yi haka ba, in sha Allahu zamu dinga tafiya ma. Dama ai bata gaya min ne shiryawa kawai take tace ta tafi.’ ‘Kada ka damu, zan dinga zuwa ina kaita wannan aikina ne.’ Baffa ya bashi amsa rai a bace. ‘Ayi hakuri Baffa, in sha Allahu ba za sake ba, ni din ma zan dinga kaita. Ayi hakuri.’ Mommy tace ‘Ke kuma kiyi hakuri da yaranki tunda su ba suyi miki komai ba, ki kula da su ku zauna lafiya. Shima kuma kin ji bayaninsa, kije kuyi zamanku lafiya kamar yanda kuka saba saboda Allah. Ita rayuwar aure hakuri ce, ku dinga hakuri da juna. Kuma nan gaba ko wata matsala ta taso muku kuyi kokari ku kasheta a tsakaninku.’ ‘Toh.’ Ta amsa cikin sanyin murya. Jimawa kadan suka yiwa Baffa da Mommy sallama suka fice; Khadeeja ta so shiga cikin gidan wajen Nabeela amma Mommy tace kada ta shiga ta barshi yana jira idan ta shirya ta dawo suyi hirar. …….. Tunda suka shiga motar bai ce komai ba sai muzurai kawai yake, don haka itama zuciyarta wasai take. Ta ji dadin yanda Baffa ya nunawa Mustapha cewa itama da gatanta; duk da dai har yanzu tana jin cewa ba zata dorawa kanta jiransa ya kaita makaranta ba balle ta dorawa kanta damuwa. PAGE 115 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Suna shiga gidan ta wuce dakinta shima ya wuce nashi dakin. Sai da tayi sallah sannan ta fito wajen yaran; zuwa lokacin Shukra har ta riga tayi bacci. Bayan ta tabbatar sun ci abinci ta wuce kitchen, ta kirawo Rashida tana tambayarta me suka dafa da daddare. Ta gaya mata indomie suka dafa saboda haka Afaf tace, ta nuna mata indomie din da ta saka a flask ta ajiyewa Abbansu. Ta riga ta san baya son indomie, musamman idan ta fara sanyi kuma itama yunwa take ji bata son cin indomie mai sanyi. Don haka Rashida ta tayata ta gyara busasshen kufi ta dafa musu jollof sphageti mai rai da lafiya. Nan da nan gidan ya dauki kamshi; zuwa loakcin yaran duk sun kwanta. Ta jera abincin a dining table sannan ta hada masa shayi mai kayan kamshi irin wanda yake so sanna ta wuce dakinsa ta tura kofa ta shiga. Saura kadan tayi dariya saboda ganin yanda dakin yayi kaca-kaca; ga kura ga kaya da tarkacensa ko ina. A ranta tace mutum sai kace kuturu, ya sa hannu ya gyara makwancinsa kawai ya gagareshi. Ta danyi gyaran murya tace ‘Ga abinci can na saka a dining,’ Dama tunanin abincin yake don yunwa yake ji sosai; ya riga ya san indomie suka dafa tunda jiya ma ita suka dafa don haka ya riga ya fara tunanin yanda zai yi sai kuma tace masa ga abinci. Ya dubeta ya dan sassuauta fuskarsa yace ‘Yanzu zan fito.’ Ba tare da ta bashi amsa ba ta juya ta fice, ya bi bayanta da kallo yana murmushin yake. Ya rasa dadi zai ji ta bashi abinci wanda hakan yake nuna zata cigaba da hidimarta; ko kuwa haushinta zai ji saboda yanda ta yaga shi a gaban Baffanta. Haka dai ya taso ya fito, babu kowa a parlor din don haka ya zauma ya ci abincinsa ya koshi; irin koshin da ya kwana biyu bai yi ba. Sai da ya gama cin abincinsa ya huta sannan daga baya yaje ya kullo gidan ya shiga dakinsa; har ya kwanta kuma ya tashi ya bi bayan Khadeeja. Ya kula idan ya biye mata ba zata nemeshi ba, ko ba komai kuma yana so suyi magana ya kara kwantar mata da hankali game da maganar Naja don ba yanzu yake so ta sani ba. Sannan kuma yana so ya nuna mata rashin jin dadinsa game da yanda taje ta kunyata shi a gaban Baffa. PAGE 116 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Duk yanda yaso ta taso su koma dakinsa su kwana kamar yanda ya saba bai samu, daga haka ya gane idan ya fiye takura mata zata sake dauke musu wuta; don haka sai ya hakura ya zubar da duk maganganun da ya taho da niyyar gaya mata. Ya hakura suka kwana a nan dakin nata tunda tace ta fara bacci bata son canza daki. ………. Tun asuba ta tashi kamar yanda ta saba, nan da nan ta shiga hidima da yara da taimakon Rashida. Ba karamin dadi ya ji ba da ya dawo daga masallaci sallar asuba ya jiyota a kitchen, don haka cike da walwala ya wuce daki ya koma bacci kamar yanda ya saba. Karfe bakwai na safe yana fitowa kowa ya shirya yayinda Khadeeja take kaiwa da kawowa tana jera masa nasa abincin a dininga table. Bayan ya amsa gaisuwar yaran yace ‘To kowa ya dauki kayansa mu wuce ko?’ Nan da nan suka mike suka far
🏠