NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 48 of 105

e kika daina kula shi shi da yaransa?’ Ta sunkuyar da kai cikin sanyin murya tace ‘Baffa ba daina kulasu nayi ba.’ Kafin Baffa yace wani abu Mommy ta shigo da sallama Nabila tana biye da ita dauke da tray wanda aka jera ruwa da lemo a kai, don haka Baffa ya tsaya ya amsa sallamarta. Ta nunawa Nabila inda zata ajiye tray din daga kusa da Mustapha, ta ajiye ta gaida Mustaphan sannan ta mike ta fice daga parlor din ita kuma Mommy ta kara ta zauna a kan kujerar da Khadija take zaune a kasanta. Ya juya ya gaida Mommy, bayan ta amsa Baffa ya sake duban Khadeeja yace ‘Ya aka yi Dije ina saurarenki.’ PAGE 112 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Tace ‘Baffa ba daina kulasu nayi ba fa.’ ‘To ai yace kusan kwana uku kenan ba kya kula kowa sai dai kawai ki kulle kanki a daki kin bar yara da mai aiki sannan kuma gari yana wayewa sai ki fice ki tafi makaranta. Kawai saboda ya tura sakatariyarsa taje makarantar yara kun hadu.’ Ta faki ido ta share kwalla; ya riga ya bawa Baffa kanun labaran don haka duk yanda take son ta kare mutuncinsa ba zai yiwuba domin itama dole ta kre kanta a wajen mahaifinta. Ta gyara zama tace ‘Wallahi Baffa ina bakin kokarina wajen kula da gidan da yaran, kuma babu laifi duk mun sami fahimtar juna da yaran gaba daya. Duk wata hidimarsu ni nake yi, kuma nice nake daukosu daga makaranta ranar da bana nan kuma sai mai-aikina ta daukosu. To shine ranar Monday suka yi open day a makaranta; nice na saba zuwarmusu don haka tun weekend suk gaya min, shi kuma na manta bamu yi maganar ba. Don haka gari na wyewa da na shirya zan tafi school sai na tsaya makarantarsu. Shine sai na ga har ya tura sakatariyarsa taje musu.’ Baffa yayi dariya yace ‘To ai babu komai Dije, watakila don baku yi maganar bane kuma kin ga ita din ai sakatariyarsa ce zai iya sakata wannan aikin duk da dai personal ne.’ ‘Ni Baffa ba zuwanta ne ya bata min trai ba…’ nan ta bashi labarin yanda taga sakatariyar a motar Mustapha din da kuma yanda tunda ta aureshi sau daya ya taba kaita makaranta a motarsa da kuma yanda ko ta shirya baya yarda ya fita da ita. Da kuma yana wasu lokutan tana tsaye a bakin titi yake dawowa daga kaisu; bata sani ba ko yana ganinta amma ita dai tana ganinsa. Baffa ya kalli Mustaphan ya kalli Mommy sannan ya kalli Mustapha wanda yayi tsamo-tsamo don bai zata Khadija zata kawo wannan maganar ba; shi da yaga ta daina damuwa ya rage mata hanya ma ya zata ta hakura gaba daya don haka bai san tana jin haushinsa a kan wannan ba. Yace ‘Ikon Allah, yanzu a ce a ki ragewa mutum hanya sai kace wani wanda ake jin haushi? Ko dai akwai wata matsalar ne Mustapha?’ PAGE 113 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Nan da nan ya fara gyara zama kansa a kasa cikin rawar murya yace ‘Babu wata matsala, em… dama yawancin lokutan ne ai bata shiryawa da wuri su kuma yaran idan 7:30am tayi rufe musu gate za ayi. Umm.. shi yasa dole muke tafiya, kuma wasu lokutan ma idan na kaisu gidan nake dawowa sai daga baya nake fita.’ Tace ‘Baffa ai ko ya dawo zai fita idan nace ya rage min hanya sai ya san abinda zai fada wanda zai sa ba zai tafi dani ba don haka ma tun tuni na daina tambayarsa.’ Suka dan yi shiru na dan lokaci Mustapha yana ta kokarin hada ido da ita yayinda ita kuma take ta kokarin kauce masa don ko gefen da yake bata kalla ba. Baffa yace ‘Shikenan abinda ya saka ki fushin ko akwai wani abun?’ kana jin muryarsa kuma ka kalli fuskarsa zaka san ransa ya sosu matuka, domin karsashi da rahar da ya fara wannan tattaunawar da su duka babu. Har ta gyada kai Mommy ta zungureta da kafa, ta dago suka hada ido. Ta sunkuyar da kanta tace ‘Baffa ita sakatariyar tasa kuma na tambayeshi menene a tsakaninsu; idan ma aurenta zai yi ai sai ya gaya min ba wai kawai na dinga ganinta a motarsa ba tana yawo a gari ni ina yawo a tasi. Saboda ni dai yanda naga ta nuna alakarsu ta fi karfin ta office kawai, don yaran ma duk sun santa ni kadai ce a gida na fara ganinta ranar.’ Baffa ya mayar da idonsa kan Mustapha wanda yayi sauri ya sunkuyar da kansa kasa, ji yake kamar ya zura da gudu don bai taba zata Khadeeja zata kawo wadannan maganganun a gaban Baffa ba. Suka yi shiru na dan lokaci kowa yana sauraron abinda Mustaphan zai ce, shi kuma ya sunkuyar da kai yayi shiru kamar wanda ruwa ya ci. Mommy ce ta gaji da shirun tayi gyaran murya tace ‘Uhm, ai gara ka gaya mata idan auren sakatariyar zaka yi ka ga tunda dai na san cewa ta san ka kai ka kara auren.’ Ya gyara zama yana shafa kewa yace ‘A’a ba ma shi bane, kawai dai da na aiketan ne to kuma ana dan wahalar mota shien nace taje a motata tunda ta iya tuki.’ Jimawa kadan Baffa yace ‘Allah ya sauwake.’ Mommy tace ‘Amin dai. PAGE 114 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Suka sake yin shiru na dan lokaci, sannan Baffa ya kirawo sunan Khadeeja, ta amsa ta dubeshi suka hada ido sannan yace ‘Kiyi
🏠