NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 47 of 105

a abinda ya faru da kuma yanda Khadeejan take rufe kanta a daki, sai dai ce masa yayi ya rasa Khadeejan ne a waya shiyasa ya tura sakatariyar tasa. Baffa yayi dariya yace ‘Kishi ne nasu na mata ya motsa, ka san a kan wata macen komai son da matarka take maka to za aji kanku. Kada ka damu bayan Magriba ka daukota ku zo nan. Zan kirawota don ma kada tace zata yi taurin kai.’ ‘To Baffa, na gode.’ Yayi musu sallama ya fice yana jin dadin matakin da ya dauka tunda ya san ko babu komai Baffa zai yi mata fada kuma ya san dole ta shiga hayyacinta. _____ Suna shirin shiga lecture wayarta tayi kara, tana dubawa taga Baffanta ne don haka ta ja da baya ta nemi waje ta amsa. Bayan sun gaisa yace ‘Khadeeja, na cewa Mustapha ku zo bayan magriba ke da shi kin ji ko?’ Tace ‘Um Baffa yau? Wani abu ya faru ne?’ ‘Babu abinda ya faru, ku dai zo din.’ ‘To Baffa in sha Allahu zamu zo, in ya dawo zan gaya masa.’ ‘Kada ki damu na gaya masa ma, yanzu ya bar nan.’ Ta amsa suka yi sallama da Baffa tana dariya, don ta san inda zancen ya dosa, ta gane Mustapha kararta ya kai duk da bata zata haka ba. Page 110 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ta jiyo motsin shigowar Mustapha gidan amma bata yi zaton zai yi saurin tafiya ba, don haka ma ta jira sai da ta gama abinda takeyi tunda ta jiyoshi da Baffa a tsakar gida. Sai dai ga mamakinta ko da ta fito Baffa ta tarar shi kadai, yana shirin shigewa mota tayi sauri ta karasa. Tace ‘Naji kamar kai da Mustapha ne, ko har ya tafi ne?’ Ya tsaya yana rike da murfin mota yana cewa ‘Shine, matar tasa ce ta fara gwada masa tutsun nata shine ya taho kawo kara da sassafe.’ ‘Ikon Allah, Khadija Iya-rigima. Me tayi kuma?’ Ta Nan ya bata labari kamar yanda Mustapha ya bashi, ya kara da ‘Na ce su zo bayan Magriba don itama yanzu zan kirawota na sanar da ita kada tayi taurin kai, kin san hali.’ Tayi dariya ‘To Allah ya kaimu, ai an auna arziki ma da aka dauki lokaci haka bata fara rigimar ba.’ Suka yi dariya ta yi masa a dawo lafiya ya wuce sannan ta koma ciki. ……… Sai da yamma tayi sannan ta kirawo Khadeeja a waya, bayan sun gaisa tace ‘Me ya hadoki da Mustapha ne ya kawo kararki da sassafe ne?’ Tayi adriya sannan ta bata labari, bayan ta gama ji tace ‘Ikon Allah, to neman mata Mustaphan yake yi kenan ko kuwa dai aure yake nema?’ ‘Nima ban sani ba Mommy, amma dai ko ma menene ai da akwai cin fuska ace ina yawo a taxi ita kuma tana yawo a motar mijina; at least ya bari ta aureshi sai ya bata wannan ikon. Kuma sannan idan itace zata dinga yi masa hidimar yaransa ai sai ta karba gaba daya ni kuma na huta gaba daya.’ Mommy tace ‘Um! Da wannan, amma dai ki bari abi abun a hankali. Saura kuma idan kun zo kiyi shiru ki ki yiwa Baffa bayani ya yanke miki hukunci in ma ya ga dama yace ki bawa Mustaphan hakuri.’ Tayi ‘yar dariya ‘Ba zan yi shiru ba Mommy.’ Suka yi sallama suka ajiye wayar. ……… Sai dab da magriba ya dawo gidan, ya yi mamaki da ya jiyo Rashida da Afaf a kitchen suna kokarin dafa abincin dare; a tunaninsa tunda ya san Baffa ya gaya mata yana nemansu ya kamata ace ta shiga hankalinta. Bayan ya amsa sannu da zuwansu ya wuce dakinta; kofarta a rufe take, ya saka mukullinsa yaji har yanzu bata cire mukullin ba don haka ya daure ya kwankwasa. PAGE 111 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Sai da ta gama yaukinta sannan ta bude ta rige hannun kofar ta matsa ya shige. Ya so ya zare mukullin kofar to amma sai ya ga idan ya zare ai duk da haka ba lallai ta dinga fita daga dakin ba balle ma ta dinga yin hidimar da ta saba; tunda dai wulakanci ne kawai ta shirya zata yi. Don haka ya bi bayanta suka shige dakin, tun kafin ta gama zama a inda ta tashi yace ‘Baffa ya gaya miki muje yana nemanmu ko?’ Cikin halin ko in kula tace ‘Karfe nawa zamu je?’ Ya so ace ta bashi dama suyi magana su kashe wannan rigimar in ya so ya kirawo Baffa yace masa sun shirya amma sai dai ga alama ta fi so suje wajen Baffan. Yace ‘Da na dawo daga masallaci sai muje.’ Ya juya ya fice daga dakin ba tare da ya saurari amsarta ba. Ta bi bayansa da harara tana dariya; wato shi uban ‘yan son kai har yanzu bai ga laifinsa ba don haka ita yake tsammani ta bashi hakuri kenan. Tabbas yau sai ta kure wannan son zuciyar na Mustapha duk da har yanzu wata zuciyar tana gaya mata kada taje ta yiwa mijinta tonon asiri a wajen iyayenta. ……… Yana dawowa daga masallaci ya sameta a shirye, ko zama bai yi ba suka sallami yara suka fice daga gidan. Suna shiga gidan suka sami Mommy wadda ta basu umarni su karasa parlor din baki domin Baffa yana can yana jiransu. Yana zaune a kan kujera 3-seater don haka Mustapha ya zauna daga gefen damansa jikin 2-seater ita kuma Khadija ta koma daya gefen jikin single seater ta zauna. Bayan Baffa ya amsa gaisuwarsu ya dubi Khadeeja yace ‘Dije, me ya hadaki da maigidanki n
🏠