’
Rashida ta fito daga dakin su Afaf tace ‘Antin ta tafi makaranta.’
Ya kalleta da mamaki yace ‘Makaranta? Yaushe?’
‘Bayan kun fita.’
Ya wuce dakinsa ya barta a nan.
To me Khadija take nufi ne? Daga yin abu ta ma ki ta zauna ayi magana tana ta wulakanci, gashi har ta sa yara sun rasa makaranta. Yanzu gashi dole ya fita ya barsu a gidan su kadai abinda baya so. Amma wannan wulakancin na Khadeeja fa ya fara yawa, ta ma ki ta saurareshi gaba daya. Yanzu ya take so ayi?
Haka ya wuce dakinsa ya zauna ya fara kiran wayar Khadeeja amma har ya gaji da kira bata dauka ba. Ya duba lokaci yaga karfe takwas da rabi, gashi yana da meeting karfe tara. Don haka a gurguje ya tashi ya shiga wanka ya shirya. Ko abinci bai tsaya ci ba ya fice ya bar yaran.
……….
Babu wanda ta gayawa yanda suka yi da Mustapha, don ko su Rahma bata cewa komai ba; su kuma da suka kula bata son magana sai kawai suka kyaleta. Haka tayi zamanta a makaranta har wajen karfe biyar na yamma sannan ta kamo hanya ta dawo gidan. Tana shigowa yara suka fara yi mata oyoyo; da murnarta ta amsa sannu da zuwansu kamar yanda ta saba. Ta kalli Afaf tace ‘Bari na je daki na sha magani na huta, kaina ciwo yake yi.’
Ba tare da ta saurari amsarta ba ta shige dakin ta turo kofa.
……….
Sai bayan sallar isha’i sannan ya dawo, lokacin Afaf ta sa Rashida ta dafa musu taliya sun ci abncin dare saboda Khadeeja tace kada wanda ya sake buga mata kofa.
Yana shigowa gidan ita ya fara tambaya suka ce masa tana daki, sai dai ga mamakinsa yana taba kofar ya jita a rufe. Nasreen ce ta sanar da shi cewa tace a dina buga mata kofa bata lafiya. Don haka shima sai kawai ya kyaleta ya cigaba da harkokinsa har sai da yara suka kwanta.
Wajen karfe goma na dare ya sake kwankwasa mata kofar, tayi banza da shi bata ce komai ba. Ya matsa jikin kofar yace ‘Wallahi Khadeeja idan baki bude kofar nan ba zan balla ta.’
PAGE 108
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Tana daga ciki ta dauki ‘yar saman rigar baccina ta saka sanna ta zo ta bude masa kofar tana rike da wayarta tana chatting. Ta koma ciki ta karasa kan gado ta zauna ta mike kafarta ba tare da ta ce masa komai ba. Yana daga tsaye ya kare mata kallo sannan yace ‘Wai wanne irin wulakanci ne wannan kike yi ne Khadeeja? Kin bar min yara sun makara a makaranta kuma kin fice kin bar gida ba tare da wani bayani ba?’
‘To ai ka san dai yau ina da lecture ko?’ ta bashi amsa sannan ta sake mayar da hankali a kan wayarta.
‘To don me baki tashi kin shirya yara ba kuma da kika dawo kika sake rufe kofa kika barsu.’
‘Au wai Najan bata zo ba? Ai na zata tayi musu komai tunda yau itace da aiki.’
Ya cije lebe sannan ya ja dogon tsaki ya fesar da iska saboda yanda Khadeeja take kureshi ‘Na gaya miki babu komai atsakanina da ita sakatariyata ce kawai, don Allah wai me kike so nayi miki ne a kan wannan maganar. Idan kuma don taje makarantar yara ne to kiyi hakuri ba zata sake zuwa ba, babu wata alaka tsakanina da ita dama sai ta office.’
‘Ai naga alama.’ Ta fada ba tare da ta daina kallon wayara ba.
A fusace yace Khadeeja ni nake miki magana kina danna waya ko kallo ban isheki ba?’
Ta ajiye wayar a gefenta ta kalleshi tace ‘Shike nan, na ji duk abinda ka fada.’
‘Please kada ki sake rufe kofar nan, kuma ga yara can sun kwanta da safe ki tashe su da wuri kada su makara.’
‘Ok.’
Har ya juya zai fita ya dan tsaya yace ‘Kuma kin san kema ba a nan kika saba kwana ba.’
‘Ok.’
Ya fice ya barta.
Ta murguda baki kamar yana kallonta tace ‘Dan rainin hankali, baka yi laushi ba tukunna kaje ka dauko Naja ta zo ta dinga yi maka hidimar kai da yaran.’
Yana fita ta zame tayi kwanciyarta sai dai bata rufe kofar ba. Tana jinsa ya dawo dakin ya leka fuskarta tayi kamar bacci take, don haka ya fice ya barta bayan ya kashe mata fitila.
PAGE 109
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Yayi zaton kamar yanda ta amsa masa da daddare zata tashi ta shirya yara, sai dai abinda tayi jiya shi ta sake maimaitawa. Ta saka mukulli ta kulle dakin, ya buga har ya gaji bata bude ba; don haka ba tare da bata lokaci ba ya tsaya a kan yara suka shirya ya kwashesu ya kai su makaranta. Kafin ya dawo ta fice ta bar masa Rashida a gidan. Takaici ne ya sake kamashi; to me Khadeeja ta mayar da shi ne? wannan wane kalar taurin kai ne take yi haka? Kuma me take nufi? Yanzu me take so yayi mata; yaya ma zai yi da ita don gaskiya idan ba so take ya doketa ba bai san me zai yi mata ba.
Haka ya shirya ya fice ya nufi office.
Har ya kusa karasawa office din dabara ta fado masa; ya karkata kan motar ya nufi gidan su Khadeeja. Gara yaje ya kai kararta waje Baffa in ya so su tsawatar mata don shi yanzu idan ba duka ba bai san me take so yayi mata ba. Ya ci sa’a ya sami Baffa yana shirin fita, bayan sun gaisa Baffa yace ‘Lafiya kuke dai na ganka da sassafe ko?’
Nan ya mayar masa d