ya yana kare mata kallo saboda yanda ya kasa fassara yanayin fuskarta domin kamar ranta ba a bace yake ba kamar ma dai tana cikin yanayi na nishadi. Yace ‘Common Khadija, na riga fa nagaya miki cewa ban sameki a waya ba shi yasa nace ita taje ko? Ko da wani abu ma ai sai ki shiryasu idan na kaisu makaranta sai mu karasa maganar kinga lokaci yana kurewa.’
PAGE 105
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
‘Babu ma wani abu, na riga na fahimci sakon.’
Ya mike yana cewa ‘To don Allah ki fito ki shiryasu kinga idan suka makara rufe gate za ayi.’
Ta cigaba da shan shayinta kamar ba da ita yake magana ba, ya fara kosawa don haka kamar a hasale yace ‘Kina ji ina miki magana ko?’
Ta kalleshi suka hada ido tace ‘Na ji.’
Ya kalli agogon bangon da yake dakin ya ga karfe shida saura kwata, ya juya ya fice ba tare da yace komai ba. Ya wuce dakin yaran don ya kula so takeyi su makara. Idan ya tasosu in ya so sai suzo da kansu su gaya mata ta taso ta shiryasu.
Yana ficewa ta tashi ta tura kofar a hankali ta mayar ta kulle ta bar mukullin a jiki, domin yau babu wanda zata shirya sai dai ayi duk abinda za ayi. Tana zama a kan daddumar taji Nasreen tana buga mata kofa tana cewa ‘Anti mun tashi.’
Har ta gaji da bugun ta ruga bandaki ba a bude mata ba.
Ya fito daga dakin nasu Rashida tana biye da shi, ya dubeta yace ‘Je ki tayat mana ku shirya yara, kun kusan makara fa.’
Ta wuce kitchen yayinda ya nufi dakin Khadeeja, ya murza hannun kofar yana turawa ya jita a rufe ‘Ya juyo da mamaki yana hango kitchen yana cewa ‘Ko kina kitchen ne?’
Ya wuce ya nufi kitchen din, yana shiga ya dubi Rashida yace ‘Bata fito ba?’
Tace ‘Eh.’
Yayi tsaki ya juya ya fice. Ya koma kofar dakin nata ya kara kwankwasawa, sai sai har ya gaji da kwankwasawa bata bude kofar ba, yana kallo ta kasan kofa ya ga duhu alamr an kashe fitilar dakin. Ya ja tsaki ya wuce dakinsa, yana shiga ya dauki wayarsa ya fara kiran lambarta. Sai dai har ya gaji da kira bata dauka ba. Don haka ya ajiye wayar a kan gadon ya fito daga dakin ya wuce kitchen, yana shiga ya tarar da Rashida tana tattare fulawar da ta kwaba jiya za ayi shawarma wadda Khadijab ta barta a nan a bude ta kwana har ta bushe. Yan shiga ta bar abinda takeyi ta tsaya tana kallonsa. Yace ‘Ya baki fara komai ba kika tsaya kina kallona?’
‘Uhm ai ban san me zan fara ba.’
‘Me kuke yi ke da ita idan zata shirya ‘yan makaranta?’
‘Um, ai itace take yin abincin ni tayata nake yi, kuma yanzu ban san me zata dafa ba.’
PAGE 106
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
‘Mtsewww!’ Ya ja tsaki sannan ya juya kamar zai fice sai kuma ya dawo yace ‘Ki dora ruwan shayi mana da abincin tafiya makaranta.’
Ya juya zai fita tace ‘Um to abincin makarantar me za a dafa?’
Ya kalleta cike da takaici; wai wannan wacce irin dakikiyar yarinya ce? Yace ta dafa abincin ma sai kuma ya gaya mata abincin da zata dafa. Kamar zai fice kuma sai ya tsaya yace ‘Ki dafa indomie.’
‘To.’ Ta amsa jikinta na rawa ta juya ta shige store domin dauko indomie.
Yana dawowa parlor din ya jiyo Afaf tana hayaniya da Shukra a kan shiryawa, har ya nufi dakin sai kuma ya fasa ya wuce kofar daki Khadeeja ya kwankwasa kofar a hankali yana cewa ‘Khadija ki bude mana.’
Babu wanda ya bashi amsa don haka ya koma parlor din ya zauna yana jiyo hayaniyar yaran a dakinsu suna shiryawa. Jimawa kadan ya tashi ya nufi dakin inda ya sa hannu ya fara kokarin tayasu shiryawa. Nan da nan suka gama sannan ya tasosu a gaba suka fito inda ya saka su a gaba suka sha shayi da burodi sannan a gurguje Rashida ta zuba musu indmie dinsu a flask ya tasa su a gaba suka fice.
Khadeeja tana jin fitarsu da mota ta fito daga dakin a shirye ta sallami Rashida ta sanar da ita idan ya dawo ta fice ta tafi makota in ya so idan zai fita sai yayi mata magana ta dawo; Haka suka saba tunda Shukra ta shiga makaranta; idan dai ba tare da yara zai fita ba sai dai Rashida ta je makota ta jira idan ya gama zai fita sannan ta dawo ta shiga gidan.
Bayan ta gama sallamar Rashida ta fice ta tafi makaranta.
………
Suna dab da karasawa makarantar aka rufe gate din, gaba daya masu gadi da sauran ma’aikatan suka shige ciki suka rufe kofa; wanda hakan yake nufi babu yaron da zai sake shiga. Ya tsaya ya cije lebe na dan lokaci sannan ya kunna motar suka kama hanyar komawa gida.
Nasreen tace ‘Mun makara, gashi bamu taba makara ba.’
Yace ‘E, kun tsaya kuna ta fada baku shirya da wuri ba.’
Afaf tace ‘Abba Anti bata lafiya ne?’
Ya shafa kansa yana cewa ‘Eh, bata jin dadi.’
PAGE 107
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Suna Shigowa gidan suka tara da Rashida a tsaye a bakin kofa kamar yanda ta saba jiransa, tana ganin su ta bisu suka shige. Shi kuma Abbansu ya karasa kofar dakin Khadeeja ya fara kwankwasawa yana yi yana cewa ‘Khadeeja daAllah ki bude mana.