NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 44 of 105

‘Baka gaya min ka mayar da ita wakiliyarka a makarantar yara ba, har sai da naje musu open day sannan sai na ganta wai kai ka turata. Har tana cewa wai na bata takardun yara ita kace ta karbo.’ ‘Eh, ai ni nace ta karbo tunda na fita ban gaya miki ba.’ ‘Kuma ka kasa yi mi waya kamar yanda kafin yau duk abinda kake so ayi na yaran kake min waya ko da ina sama jannati ne naje nayi?’ Ya fara hasala saboda yanda take maganar a tsiwace ga wani kallon raini da take masa. ‘Ba fa na son wulakanci khadeeja; ni na turata ta karbo ko ban isa bane? Na zata zaki yi murna tunda kullum cikin korafi kike da mitar hidimar yaran saboda kina gani ba ke kika haifesu ba, ke naki karatun ne a gabanki. Tayi murmushi tace ‘Ka isa har ka yi yawa, kuma alhamdulillahi tunda an sami mai karbata yanzu kam zan huta da wasu abubuwan. Kuma na gane nice ban isa na shigar maka mota ba shi yasa ita da kake ganin mutuncinta ka koya mata mota har gashi nan ta kai ta dauki motarka ta fita yawo.’ Ta daga kafa zata shige bandaki sai kuma ta tsaya ta kalleshi suka hada ido sannan tace ‘Bayan hidimar yaran sai kuma wacce hidimar take maka? Ko ma dai ka aureta ne nice ban sani ba?’ ‘Ba fa na son iskanci Khadeeja! Kina ji nace miki sakatariyata ce kike wannan maganar banzar. Na aiketa don haka na bata mota ta taje ta dawo, shine kike wannan rashin kunyar? Idan da kina hidimar yaran ba tare da kosawa ba ai babu wanda zan nema. Na san idan na gaya miki sai kinyi mita don haka na nemi wadda zata yi cikin walwala na sakata, sai dai duk abinda zaki yi kije kiyi amma idan kika zageni wallahi ba zaki ji da dadi ba.’ Tayi murmushi ‘Hmmm! Ka fi karfin zagi yallabai, amma tabbas kayi yanda kake so don haka nima zan yi yanda nake so.’ Ta juya ta shige bandaki ta turo kofar ta barshi nan tsaye. PAGE 103 MIJIN MARIGAYIYA A HAUSA NOVEL by Sakina Yazid (Innar su Amal) Haka ya gaji da tsayuwa ya juya ya fice daga dakin; tana jin fitarsa ta fito ta saka mukulli ta kulle dakin ta bar mukullin a jiki ta koma ta kwanta. ……….. Tun a office Naja’atu ta sanar da shi haduwarsu da Khadeeja, kuma ita kanta sai da ta nuna rashin jin dadinta a kan ya san Khadeeja zata je ya tura ta. Sai da yayi ta faman bata hakuri sannan ya samo kanta. Bai taba zaton Khadeeja zata bashi matsala, don ya zata idan yace mata sakatariyarsa ce zata fahimceshi, yanzu gashi itama Khadeejan so take ya lallasheta. Yana da niyyar auren Naja don sun ma yi magana da Alhaji kwanan nan ma za a kai kudin aure; kawai dai bai shirya gayawa Khadija ba saboda bai shirya ba, ya fi so sai magana ta tsaya an kusa biki sai ya sanar da ita. Kafin lokacin ya gama gininsa sai su tashi su koma don a can yake so amarya ta tare. Yanzun ma kuma da hakan ta faru ba gaya mata zai yi ba, idan ta gama fushin nata ya san me zai gaya mata. Tun yana saka rai zata bude kofar dakin har dare ya fara yi bata bude ba, yara har sun gaji da tambayarta. Haka ya sa Rashida ta basu abinci sannan ta tayasu suka shirya suka tafi suka kwanta, shima ya shiga dakinsa ya kwanta yana sauraron lokacin da zai ji motsinta. PAGE 104 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Da asubar fari ya tashi, bayan ya gama alwala ya fito da niyyar tafiya masallaci ya karasa kofar dakinta ya murza hannun kofar ko zai jita a bude amma sai ya jita a rufe, sai dai ya hango fitila ta kasan kofar dakin a kunne. Don haka ya kada kai ya wuce masallaci ya san ta riga ta tashi. Tun kafin ta tayar da sallah cikinta yake kugi saboda jiya bata ci abincin dare ba ta kwanta, don haka tana idar da sallah ta gama azkar dinta ta bude kofar dakin ta fito ta wuce kitchen; a lokacin Rashida da su Afaf babu wanda ya tashi domin dama itace take tashin Rashida kafin tayi sallah su kuma su Afaf bayan ta idar da sallar. Tana shiga ta dora ruwa kofi daya ta jira ya tafasa, ta hada shayinta mai kauri a babban kofi ta dauki burodi ta gutsura ta dauka ta nufi daki. A falo ta ci karo da shi ya shigo daga masallaci, ya dubeta yace ‘Shayi zaki sha da sanyin safiya kuma.’ ‘Um.’ Ta bashi amsa sannan ta wuce dakin. Da hanzari ya bita don kada ta rufe kofar, ya cimmata a daidai lokacin da take zama a kan dadduma tana ajiye shayin nata. Ko kallon inda yake bata yi ba balle ta nuna ta san mutum ya shigo. Ya karasa ya zauna a gefen gado yana cewa ‘Sai kin gama zaki taso yaran ne? akwai school fa.’ Ta gutsiri burodi ta tsoma a shayin sannan tace ‘Bani da lecture sai 9am so idan na gama zan dan koma ne na rage bacci zuwa kamar 8am sai na tashi na shirya.’ Ya dan yi dariya a kaikaice don ya san kwanan zancen, yace ‘Haba dai, ai kya daure ki shirya yaran kafin ki koma ki kwanta ko?’ ‘Oh, ai kuma ka cire al’amarinsu daga hannuna ka saka a hannun sakatariyark kamar yanda ka sanar da ni a aikace jiya don idan ban manta ba ma itace ta kawo muku dinner. Ko ba komai ma ka huta da mita ta.’ Ta dauki kofin sahyinta ta cigaba da kurba. Ya dan tsa
🏠