‘Ko dai abun ya zo ne a tanadi goro da ledar amai.’
Ta sake fashewa da sabon kuka.
Suka yi tsuru-tsuru. Rahma ta shafa bayanta tace ‘Kawata kina fadar mana da gaba fa, don Allah me ya faru? Ko Babe bashi da lafiya ne?’
PAGE 100
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Haka suka yita jero mata tambayoyi, ita kuwa tayi banza da su har suma suka gaji suka yi shiru, suka zauna kawai suna jiranta. Sai da tayi mai isarta sannan ta basu labarin abinda ya faru.
Rahma tace ‘kada fa nayi ashar kawata, kut! Wannan wanne kalar wulakancine mutumin nan yake miki?
Farida tace ‘Motar da yake kyashin daukanki yaje ya bawa budurwa ko ma karuwa take yawo a titi? Lallai an gaida uban Afaf.’
Rahma tace ‘Gaskiya idan ya dau yau ya kamata yayi miki bayani na ganewa, duk da babu wani explanatin da zai sa na yarda babu wani abu a tsakanishi da ita ba sakatariya ba ko DG ce wallahi. Yayi miki bayani kuma kema ki karanta masa; wannan ai zubar da mutunci ne kina yawi a motar haya wata sidechick tana yawo a motar mijinki? Mijinki na sunna fa, Haba! Gaskiya dai ya kamata ki san yanda zakiyi ki kwaci kanki a hannun mutumin nana tunda shi ga alama bai san mutunci ba.’
Amina tace ‘Don Allah ku barta ta bai abun a hankali.’
Ta kalleta rai a bace ‘A hankali Amina? Shi a hankali kika ga yana yi min? Ni budurwarsa take cewa wai na kawo takardun yara ta kai masa saboda tsabar samun waje? Haba mana!’
Farida tace ‘Toh shi dai na gani, aure ai ba hauka bane. Wallahi ya kamata ki dage ki gaya masa abinda yake ranki tunda dai an dade ana ruwa kasa tana shanyewa, ai ba siyoki yayi a bakin rimi ba da zai mayar dake kamar wata sokuwa.’
Amina tace ‘Don Allah ku bari a bi abun a hankali, miji fa ba kamar saurayi bane haba!’
Rahama ta ja hannun Amina tace ‘Taso ‘yar uwa mu nemo abinci wannan batun na masu aure ne ba namu ba kin ji.’
Haka ta wuni a makarantar nan Amina tana bata baki yainda Farida da Rahma suke kara jaddada mata ya kamata ta dauki mataki idan ba haka ba rainin zai wuce haka.
Sai bayan la’asar sannan ta kwaso kayanta ta dawo gidan.
……….
Wunin ranar haka ta karasashi cikin kunci, saida ta cewa yara bata da lafiya sannan suka kyaleta don kowa yana so ya bata labarin sports day. Rashidace ta karasa duk wata hidimar gida da ta yara, har abincin ma da baya so Rashidan ta girka yau cewa tayi ta girka don a yanda take jin ko ta dafa ba zai yi dadi ba.
PAGE 101
MIJIN MARIGAYIYA
A HAUSA NOVEL BY SAKINA YAZID (INNAR SU AMAL)
Sai bayan sallar magriba sannan ya dawo gidan, bayan ya gama hayaniya da yara ya wuce dakin ya sameta. Tana kwance bata ko juyo ta kalleshi ba don haka ya yi zaton bacci takeyi. Sai kawai ya kintsa ya fice daga dakin.
Bata son yiwa yaro alkawari ta karya don haka tun da ta dawo ta sa Rashida ta hada mata duk wasu kayan da take bukata na hada shawarma sanna ta kwaba mata fulawar, yanda idan ta fito bayan isha’i sai ta hada shawarma kamar yanda ta yiwa Habib alkawari idan yayi passing Hausa.
Suna zaune shi da yaran ta wucesu ta shiga kitchen, nana da nan ta fara koakrin dorawa.
Tana daga kitchen ta jiyo yana amsa waya yana kwatancen gida; ta ja tsaki a fili tana fatan Allah ya sa ba bako zai yi ba don ko me zai yi ba zata gaisa da wani bako ba balle ta bashi ko da ruwa. Sai dai yayi duk abinda zai yi. Kafin ta gama wannan tunanin ta jishi yana cewa yanzu zai fito, inda ba tare da bata lokaci ba ta ji fitarsa.
Jimawa kadan ya shigo da leda ya wuce ya sameta a kitchen tana yayyanka fulawa zata fara gasawa. Ya mika mata ledar yana cewa ‘Ga wannan shawarma ce; sakatariyata ce Naja ta aiko delivery man ya kawo a bawa yara. Sai ki duba ki zubo a tray mu ci don na ji kamar da yawa’
Ta kalleshi da jajayen idanuwanta wadanda suka kode saboda kuka da tsabar mamaki; tayi murmushi mai daci sannan ta kashe wutar abinda ta dora a wuta ta nufoshi yayinda ya mika ledar a zaton zata karba. Ta bigi kafadarsa ta wuce ta shige daki ta barshi a nan tsaye.
Ya bi bayanta da kallo cike da tsananin mamaki saboda Khadeeja bata taba yi masa irin wannan wulakancin ba; kuma a gabn yara don duk biyoshi suka yi da suka ji yana maganar a juye a ci.
Nan take ya ajiye ledar kan sink sanna ya bi bayanta daki; yana shiga ya sameta a tsaye a gaban mudubi tana cika tana batsewa kamar ma jiransa take yi.
‘Wannan wane irin wulakanci ne ina miki magana zaki yi min tsaki a gaban yara saboda raini.’ Ya tambaya cikin jin kai da isa.
Ta kalleshi ta dauke kai tana murmushin takaici tace ‘Ji nayi kamar zagina kayi.
PAGE 102
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Kallon takaicin da yake mata ya koma na mamaki, ya tsareta da ido kuma itama ta ki dauke nata idon. Yace ‘Ni na zageki? Ko kuwa dai ke kika zageni?’
Ba tare da ta bashi amsa ba tace ‘Wacece Naja?’
‘Mtseww!’ ya ja tsaki sannan ya cigaba ‘Sakatariyata ce; shine kike nema ki zageni saboda nace ta kawowa yara abu?’