NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 40 of 105

ya bata ‘yaya wadanda zasu kalleta a matsayin uwa. PAGE 93 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ta rigashi kwanciya kamar yanda suka saba saboda yanda ta kula idan ta zauna jiransa su kwanta tare ita ake cuta tunda dole ta tashi kafin asuba ta shirya yara. Sai wajen sha biyu saura sanna ya gama abinda yake ya kwanta a kusa da ita, ta juya ta gyara kwanciyarta. Yana kwance amma ya daga waya yana chattinga kamar yanda ‘yan kwanakin nan ta kula kullum kafin ya kwanta sai yayi chatting. Ta mike taje ta yiwo fitsari, ta sha ruwa sannan ta dawo ta kwanta, zuwa lokacin ya gama chatting din ya ajiye wayar yana azkar. Ta kwanta ta gyara kwanciyarta, bayan da ta kula ya gama azkar din ta lalubo hannunsa ta rike cikin sanyin murya tace ‘Abban Afaf.’ ‘Umm.’ Ya amsa yana kallonta duka da hasken da yake cikin dakin bai kai ya kawo ba. ‘Uhm, gaskiya ina son zuwa asibiti naga gynae doctor.’ Ta fada tana wasa da hannunsa wanda ta rike. Ya rike hannunta a cikin nasa ya kara bata hankalinsa yace ‘Baki da lafiya ne?’ ‘No ba wani specific issue. Ka san dai kwanaki nace maka ina son naje a duba aga abinda yasa har yanzu ban sake samun ciki ba, kada naje wata matsala ce nayi ta zama gara naje a duba.’ Ya gyara kwanciya ya kara matsowa kusa da ita ‘Kina dai so ki dorawa kanki damuwa, har yanzu fa ba a yi shekaru biyu da barin ba. Iya wannan ya isa ya sa ki san cewa lafiyarki kalau, kawai Allah ne bai kawo ba tunda wancan din ma ba asibiti kika je kika samo ba ko?’ ‘Na sani, amma dai gaskiya ina so naje a duba ni din na sami nutsuwa. Tunda ka ga idan naje aka ce min lafiyata kalau ai dawowa zan yi kawai na cigaba da addua’a, idan kuma matsala ce sa na nemi maganinta.’ ‘Babu wata matsala kina dai son tonowa kanki matsalar. Ke yanzu ma da kike neman ciki ido rufe ya zaki yi da karatun? Tunda gashi kin shiga level 3 kuma ke da kanki kina cewa ya fi wahala. Ya zaki yi da laulayi ga karatu? Ko har kin mata ne? ai zai fi sauki idan ma dolene sai kin je asibitin ki bari ki gama karatun kafin ki kwantar da kanki.’ Suka yi shiru na dan lokaci, kowa da abinda yake tunani. PAGE 94 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Jimawa kadan tace ‘Ina son zuwa gaskiya, amma dai ina jin zan bari mu gama examsa din wannan semester in ya so kafin a koma hutu sai na samu naje.’ ‘To Allah ya kaimu.’ Tana son ta haihu duk da dai Mommy ma tace mata lafiyarta kalau amma ita gaskiya tana so taje a duba ta. Kuma yanda Mustapha yake gwada mata halin ko in kula idan ana maganar haihuwa ya sa gaba daya ta fara tunanin ko bai damu da ta haihu ba; to ya ma za ayi ya so ta haihu tunda shi masoyiyarsa ta haifar masa yara har uku? Haka tayi ta sake-sake tana juyi, sai gefin asuba sannan bacci ya dauketa. ______ kamar kullum yana shiga office din yau ma damuwarsa ta yaye; musamman yanda kamshin turarenta ya yiwa kofofin hancinsa maraba bayan da ya shiga office din nasa ya rufo kofar. Wannan ya tabbatar masa da cewa ta riga ta zo office din watakila wani office din taje. Ya ajiye jakarsa a kan table ya karasa ya zauna a kan kujerarsa cike da farin ciki. Sabuwar sakatariyarsa Naja’atu Musa Bello; watanta uku da fara aiki amma soyayya mai karfi ta kullu a tsakanisu. Duk wata damuwa da Khadeeja zata dora masa da ya shigo office din ya ganta yake mantawa da ita, idan kuma an tashi daga office ko a ranakun da babu aiki ya kan je gidansu zance. Duk da dai manya basu riga sun shiga zancen ba amma dai yana ji a jikinsa Naja’atu tasa ce. Bai dade da zama ba ta turo kofar ta shigo, daga tsaye ta sakar masa kyakkyawan murmushinta wanda baya gajiya da kalla. ‘Ranka ya dade barka da shigowa.’ Ta fada tana juya kwayar idonta. ‘Good Morning my dear.’ Ya amsa yana ta faman murmushin da yake barazanar karawa bakinsa fadi. Ta karasa ta zauna a kujerar gabansa, sannan ta dauki file a kan teburin ta mika masa. Nan take ya buda ya fara karantawa yana mata tambayoyi tana yi masa bayani. Bayan sun gama ya ajiye file din a gefe ya dubeta yace ‘To meye labari?’ Tayi dariya ta sunkuyar da kai a kunyace tace ‘Komai normal.’ ‘Good. So nayi mana order din lunch ko? Don na san ko ance kizo muje mu ci a waje ba kya son zuwa eateries, sai shopping ko?’ Tayi dariya tace ‘Gara dai ayi order din.’ PAGE 95 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Tayi dariya tace ‘Gara dai ayi order din.’ ‘Ba damuwa, kiyi mana order din sai ki turo min account number na tura kudin.’ ‘Yes Boss, an gama.’ Suka yi dariya gaba daya. Tana shirin tashi yace ‘Yauwa, gobe ana open daya a school din su Afaf, please idan kika shigo around 10am sai kije musu, ki jiyo min duk bayanasu da performances din su.’ Ta gyara zama tace ‘Uhm, ok. But Madam ba ta nan ne ko bata jin dadi?’ Ya gyara zama ya fara lilo a kujerar da yake kai yana kallonta sosai sanna yace ‘No, lafiyarta
🏠