NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 39 of 105

aki ta sameshi bayan ta zubawa yara abinci suna ci, yana kwance a gefen gado yana fama latsa waya ta wuce har ta kusa shiga wankan yace ‘Idan na kai yara dawowa zan yi kin sani, sai wajen 10am zan fita, ita wannan yarinyar taki haka zaki bar min ita a gidan daga ni sai ita?’ Cikin halin ko in kula tace ‘Eh, ita da Shukra zasu zauna idan zaka fita kawai ka gaya mata don ta san cewa ka fita ta cigaba da aikinta.’ Har zata shige bandakin yace ‘Gaskiya bana so, kuma kema kin san bai dace ba ki barni a gida daga ni sai mai aikinki mace. Irin hakane kuma idan an ce za a auri mai aikin kuce baku yarda ba.’ Duk bacin ran da take ciki sai da ya bata dariya, duk da dai dariyar takaici ce tace ‘to ai gaka nan gata nan ka aureta mana, ai itama mace ce.’ PAGE 91 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) ‘Ni dai na gaya miki bana son ki barta a gidan idan ina nan tunda ke bakya nan, ki sami inda zaki ajiyeta idan na fita sai ta dawo gidan.’ ‘Uhhm!’ Ta amsa sannan ta shige wankan cike da takaicinsa, har ji take kamar zuciyarta tana turiri. Zuwa makaranta lecture kawai ya zama wata drama. Nan da nan ta karasa shiryawa ta shirya yaran, ta hada tea ta zauna tana sha. A haka Mustafa ya fito ya samesu lokacin 7:15am. ‘Ku tashi muje.’ Ya fadawa yaran. Ta mike rike da kofin shayinta tace ‘Bari na dauko hijab dina na saka ku rage min hanya.’ ‘A’a zaki makarar damu ne fa, gashi ko shayi baki gama sha ba kuma kin san idan suka makara korosu za ayi.’ Ya juaya ga yaran wadanda sun riga sun mike kowa da kayansa a hannu yace ‘Mu je.’ ‘Anti sai mun dawo.’ Suka fada sannan suka juya suka fice ya bi bayansu. Ta bi bayansa da kallo cike da mamaki; ta kasa gane motarsa ce baya son ta dinga shiga ko kuwa tsabar bakin ciki ne a kan zata fita yake hanashi rage mata hanya. To amma kuma yana kaita unguwa, ko da yake wannan fita ce da shi ya ga dama kuma kusan duk inda zata tunda ta aureshi tare yake kaita da yaran suna biye da ita. To me yasa idan dai makaranta zata tafi sai ya san yanda yayi ya tafi ya barta ba tare da ya ko da rage mata hanya ba? Haka har ta gama shirinta ba tare da ta samo amsar tambayarta ba; ta fito ta sami Rashida a kitchen tace ‘Idan babansu ya dawo ki koma daki ki zauna in ya fita sai ki fito ki cigaba da aikin; idan Shukra ta zauna a wajensa shikenan idan kuma ta taho wajenki to don Allah kada ki bari tayi kuka yaji.’ Tayi mata sallama ta fice tana sauri saboda 7:20am ta riga tayi kuma bata da tabbas din zata iya kaiwa BUK kafin 8:00am. Ta kusa isa titi Mustapha ya karyo kwana ya shigo layin, ta dauke kanta daga kallon inda yake; bata sani ba ko ya ganta ko bai ganta ba. Ta karasa titi cikin sanyin jiki ta hau Napep tambayoyi daban daban suna ta yawo a kanta; wai ina babe dinta ne? wanda yake son ta? Wanda kafin aurensu har so yake ya daukota daga makaranta ya kaita unguwa ko ya kaita gida don dai tana hanashi ne saboda ta san Baffa ba zai bari ba a lokacin. PAGE 92 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) To shikenan soyayya ta kare ko me Mustapha yake nufi da ita? Shekara daya fa kenan da ‘yan watanni da aurensu. Kwanci tashi cikin wannan rayuwar da Khadeeja take a gidan Mustapha har ta gama level 2 a karatunta ta shiga level 3, kuma shekararsu biyu kenan da Rashida mai aikinta. Zaman dai haka ake yinsa cikin dagewa da dagiya; idan Mustapha yana son bukatarsa a wajenta sai taji kamar ba shi ba saboda yanda yake kwantar da kai ya samu bukatarsa ta biya. Amma kuma da zarar tayi maganar karatunta ko wani abu da zai sa ta fita daga gidan ba tare da ta tafi da yara ba to sai ya nuna bacin ransa. Domin a halin yanzu kowa a danginsu ya santa da ‘yayanta domin tare ake ganinsu ko bikin wa ake yi. Gidan Mommy kuwa sun mayar da shi kamar gidan kakarsu, kuma da yake sun sami karbuwa sai suka sake sakewa. Karatunta yana tafiya daidai tunda ta saka auduga ta toshe kunnenta daga duk wata mita ta Mustapha, sai dai kawai kullum a gajiye take daga aikin gida da kuma aikin tunanin abinda zata yi Mustapha ya daina nuna mata halin ko in kula. Yaran basu saba bata matsala ba a da, amma zuwa yanzu duk tana neman ta rasa kansu; musamman Afaf da Nasreen. Idan dai aiki ta saka su ba zasu ce ba zasu yi ba amma idan basu ga dama haka za suyi kunnen uwar shegu da ita sai dai ko ta yi aikinta ko kuma ta sa Rashida tayi mata. Sannan kuma yanzu Afaf ta kulla kawance da Samira ‘yar wajen Yaya Jidda, don haka kusan duk wani motsi na Khadeeja Afaf sai ta gaywa Samira wadda take kaiwa uwarta rahoto na kai tsaye; don haka ne ma matsawar da Yaya Jidda takewa Khadeejan ta karu. Sai dai a yanzu ba wannan ne damuwar Khadeeja ba, babbar damuwarta itace rashin haihuwa. Tun bayan da tayi bari a loakcin corona ko batan wata bata sake yi ba gashi ana neman shekaru biyu. Zaman gidan baya mata dadi, bata jin dadin yanda yaran suke mata, musamman Afaf wadda a da take tunanin sun zama daya. Tana fatan itama Allah
🏠