uka yi sallah kowacce ta kama hanyara gida.
Ko da ta zo gida bata tarar da wata matsala ba, Rashida ta kai Shukra gidan su Ummi ta dauko Nasreen daga makarantar kamar yanda ta bata umarni. Su kuma Afaf da Habib kusan tare da ita suka shiga gidan.
Ko da ya dawo tana jin sa yana tambayar taran wanda ya daukosu daga makaranta suna ba shi amsa, musamman Shukra wadda yake ta tambayarta me suka yi ita da Rashida a gidan bayan Anti ta fita. Haka tayi banza da shi ta cigaba da harkokinta.
Haka suka cigaba da yi, sai ya zama kuma da yake ba a fara lecture sosai ba sati biyun farko kullum Khadeeja bata fita da wuri sanna kuma tana dawowa kafin ya dawo gidan, don haka matsalarsu da sauki tunda zai zo ya tarar da ita tana ta hidimar yara.
…….
Sati daya da komawa aka kafewa su Khadeeja timtable, kuma da yake babu lokaci sosai timetable din a matse take. Haka dai suka cigaba da karatun.
Ranar Alhamis shine take da lecture 8am to 6pm, don haka ta san dole ta shirya ta fita tare da yara. Tun dare ta gama komai, tayi rabin aikin abincin safe sannan ta fitowa da kowa kayansa. Ta yiwa Rashida duk wani bayani da take bukata tunda yaran idan sun dawo daga makarantar boko babu islamiyya don haka nan zasu wuni a gidan.
Tun kafin asuba ta tashi suka fara aiki tare da Rashida.
PAGE 89
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Bayan Mustapha ya dawo daga masallaci sallar asuba ya sameta a kitchen, tana ta fama kaiwa da kawowa tsakanin dankalin da take soyawa da kuma hadawa yara abincin makarantarsu a lunch box. Bayan ya amsa sannu da zuwanta yace ‘Wai kin yi sallah kuwa? Na ga kamar a nan na barki fa.’
Tayi ‘yar dariya tace ‘Haba dai, nayi sallah mana. Sauri nake na gama saboda yau 8am to 6pm ne da ni kuma 8am din nan idan Prof. ya rigani shiga aji rufe min kofa zai yi wallahi shi yasa nake ta sauri don kullum sai yayi attendance.’
‘Oh kenan yau sai 6pm zaki dawo gidan?’
‘Eh.’ Ta amsa a gajarce tana kwashe dankalin da ya riga ya soyu.
Ya kara hade girar sama da kasa sanna yace ‘To a ina zaki bar yara wuni guda?’
Bata son hayaniyarsa don bata son abinda zai bata mata rai, ba tare da ta bar abinda take yi ba tace ‘A nan mana gidansu; Rashida zata dauko Nasreen su kuma su Afaf idan suka dawo zasu sameta a gidan sai suyi zamansu kafin na dawo, they will be just fine.’
‘Haba ai dadewar tayi yawa, kenan haka zasu zauna suyi duk abinda suka ga dama ba tare da wata kulawa ba.’ Ya fada a fusace.
‘Kada ka damu Rashida zata kula da su.’
Kafin ya bata amsa suka jiyo ihun Nasreen daga dakinsu tana cewa ‘Wayyo Anti.’
Ta riga ta san rigimar Nasreen, idan dai aka tasheta da sasafe zuwa makaranta sai tayi kuka ko ma waye ya tasheta, shima kuma ya san da haka. Amma ba tare da bata lokaci ba ya nufi dakin da sauri. Ganin haka itama Khadeejan ta ajiye abinda take yi ta bi bayansa, kusan a lokaci daya suka shiga dakin.
Nasreen tana zaune a kan gadonsu da hawaye shabe-shabe a idonta yayinda Rashida take tsugune a gaban gadon tana rike da towel.
‘Me aka yi miki kike kuka Nasreen?’ Ya tambaya kafin ya karasa shiga dakin.
Khadeeja tana shiga dakin ta sauko daga kan gadon ta rungumeta tana cewa ‘Anteee.’
Ya shafa kanta ‘Me aka yi miki?’
Cikin shagwaba tace ‘Rasheeda ce.”
Ya juya ya dubi Rashidan a fusace yace ‘Me kika yi mata?’
Nan da nan jikinta ya hau rawa tana gyara tsuguno, kafin tayi magana Khadeeja ta shafa kan Nasreen tace ‘Nas me Rashida tayi miki?’
‘Tashi na tayi daga barci.’
PAGE 90
MIJIN MARIGAYIYA
A HAUSA NOVEL by Sakina Yazid (Innar su Amal)
‘To ai kin ga shiryaki zata yi ki tafi school ko? Ko kina son ki makara Uncle ya koroki gida ne?’
Yayi tsaki ya fice daga dakin ba tare da ya sake cewa komai ba.
Ta lallaba Nasreen ta tura ta bandaki sannan ta juyo zata fito, kafin ta fito ta jiyoshi yana dawowa dakin yana cewa ‘Dankalin da kika bari a wuta ya kone, kije ki duba na kashe miki wutar.’
Ta wuceshi ta karasa kitchen din da gudu inda ta sami dankalin ya kone, ta kwashe sannan ta sake kunna wutar ta dora. Ya karaso ya tsaya a kofar kitchen din, ya dan dauki lokaci yana kallonta tana zubawa yara abincin rana wanda ta sauke a babban flask. Jimawa kadan yace ‘Kin ga irin abinda yasa bana son ki barsu da yarinyar nan ita kadai ko? Ya za ayi ta iya kula da yara tunda gashi nan bata ma iya tashinsu daga bacci ba?’
Ta kalleshi cike da mamaki tace ‘Nasreen ce fa, ko kaine ma ka tasheta sai tayi rigima, ko ka manta ne? Kuma kaine kace baka son Rashida ta dinga yi maka girki kuma ka ga dole abu daya zan yi a lokaci guda ba zai yiwu ina girka muku abinci ba kuma ina shirya yara.’
Ya juya ya fice ba tare da ya ce komai ba.
Ta ja tsaki ta share kwallar da ta taru a gefen idonta sannan ta cigaba da aiki. Bata ma san me take ji ba, kokari kawai take ta fita daga gidan idan taje makaranta ta samu tayi tunani ta fahimci me take ji.
Bayan ta gama abinci ta wuce d