NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 37 of 105

ma kafin na fita zan je da Rashida taga makarantar tasu idan lokaci yayi bandawo ba sai taje ta dauko Nasreen.’ Ya gyara zama ya kalleta kamar a foirgice ‘Wai wannan yarinyar ce zata dinga dauko yaran daga makaranta kuma ta zauna ta zauna dasu a gidan ita kadai?’ Cikin halin ko in kula tace ‘To ya za ayi, ai kaga dai nima dole naje makaranta ko? They will be fine fa, yarinyar tana da hankali sannan kuma ka ga ga Afaf tana nan idan ta dawo. Suma ita da Habib na gaya musu idan an tashi daga makaranta su taho tunda na ga ko nice ma naje daukosu idan muka rasa napep a kasa muke tahowa.’ Ya kare mata kallo sanna yace ‘Wai me kike fada ne? su Afafa din ne kike so su dinga tahowa daga makarantar su kadai kuma a kas, sannan harda Nasreen? Wadda sai an tasheta da minti talatin sannan a tashesu?’ ‘To babe ya zamu yi? Ai ka ga dai kamar Afaf bashi da wani amfani ace sai Rashida taje sannan zasu taho tare ko? Ni kuma duk lokacin da ta kama ina gidan zan je na daukosu.’ Suka yi shiru na dan lokaci kowa da abinda yake tunani. Jimawa kadan yace ‘Ni barin wannan yarinyar taki ma a gidan ita kadai gaskiya bai yi min ba, ya za ayi duk mu fice a barta ita kadai kuma a bar mata mukullin gidan? Ai idan muka dawo sai abinda muka gani kenan, za ma ta iya fara shigo da maza gidan ko ayi mata wayo ayi mana barna idan aka gane ita kadai ake bari a gidan.’ ‘To yanzu ya kake so ayi? Ka ga dai da ni da yaran ai dole duk muje makaranta ko?’ ‘Ni ma ban sani ba, kece zaki san yanda zaki yi. Zaki maiya fita da ita ki rufe gidan in ya so sai ku dawo tare ki dauko yaran, duk yanda dai kuka yi. Amma dai gaskiya wannan tsarin na barinta a gidan bai yi min ba.’ Ranta ya fara baci; me yake nufi ne? so yake yace ta bar makarantarta kawai saboda ta zauna masa da yara ko kuwa mai aikin yake so ya korar mata? Wannan bayanin da yake yi ma sam ba zai yiwu ba gara dai ya sake lissafi ko kuma shi ya dinga baro office yana zuwa yana daukosu. PAGE 87 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal Tace ‘Uhm, to ai ka ga ba ni nake rubutawa kaina timetable ba, wani malamin ma sai 1pm yake fara lecture kuma dole nayi attending idan dai ina son na gama degree din. Sai dai ko ka kawo wata dabarar da kai kake ganin za ayi da daukosu in ya so ita Rashida idan zan fita sai na fita da ita duk lokacin da na gama lecture sai mu dawo tare.’ Suka yi shiru na dan lokaci, jimawa kadan ya tashi ya jefar da remote din TV din da yake hannunsa ya shige daki. Ta bi bayansa da kallo tana mamaki; wai me mutumin nana yake nufi ne? shikenan sai ta jingine rayuwarta ta zauna ta kular masa da yara? To ai ita ko ‘yayan da ta haifa ma haka ko tana so ko bata so zata dinga barinsu da mai aikin ta tafi makaranta tunda dai haka taga masu yaran suna yi. Ko kuwa da yake ta auri tuburarre hakura zata yi da komai ta zauna sai yanda suka yi da ita? Haka suka kwana a wannan daren kowa da abimda yake ransa. Ko da gari ya waye tun asuba ta tashi uta da Rashida wadda ta tayata nan da nan suka shirya yara sannan suka hadawa kowa abinci. Kamar yanda ya saba sai karfe bakwai da kwata sanna ya fito, zuwa lokacin sun shirya suna jiransa; ya kwashesu ya kaisu ya dawo. Sai wajen karfe tara da rabi sannan ya gama shirinsa, lokacin fitowarta kenan daga wanka saboda sai da ta tsaya ta gama abincin rana ta juye a flask sannan ta fara shirin. Ya sameta a daki tana shafa mai rike da mukullin motarsa, yana daga tsaye a bakin kofa yace ‘Ni na fita.’ Ta juyo da sauri tana cewa ‘La! Babe don Allah bari nayi sauri na saka kayana sai ka bani lift.’ ‘No ba ta hanyarku zan bi ba, ki wuce kawai sai na dawo. Kada ki manta min da yara.’ Ya fada yana ficewa daga dakin. Tabi bayansa da kallo da baki bude; lallai ma mutumin nan. Kiri-kiri dai shi baya son ya dauketa a motarsa idan dai makaranta zata, in banda haka ai ko ba hanyar makarantarsu zai bi ba ya sauketa a bakin titi ya rage mata tafiya. Ta juya ta cigaba da shiryawa cikin sanyin jiki tana tunanin son kai irin na Mustapha. Allah ya so ta ma Baffa ya tura mata kudi kuma ya sanar da ita duk wata zai dinga turo mata kudi saboda karatunta, idan tana son wani abu sai ta yi masa magana. PAGE 88 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Tabbas ta san da ace da Mustapha ta dogara da sai dai ta hakura da karatunta ta zauna ta kular masa da yara. Nan da nan ta karasa shiryawa ta fito ta sallami Rashida wadda ta barsu tare da Shukra bayan ta yi mata duk wani bayani da take bukata sannan ta kama hanya zuciyarta cike da damuwa da wasi-wasi. Kafin sha biyu ta gama duk wani abu da take yi a makarantar sai dai bata son ta dawo ta dauko yara; ba wai yaran ne bata son daukowa ba amma bata son ta daukosu Mustapha yaga kamar fadansa ne ya sa don haka duk lokacin da zata fita ya zata zai yi mata fada ta dauko masa yara. Don haka suka nemi inuwa ita da kawayenta suka zauna suna hira, sai wajen 1;30pm sannan suka karasa masallaci s
🏠