wa babansu waya ya biya abinda ‘yayansa suka ci tunda yana kallo suna ci kuma ya san ba shi ya siyo ba.’
Hajia tace ‘A’a ba za ayi haka ba, sai kace a garin matsiyata ake.’ Ta dubi Mustaphan tace ‘Kai Mustapha kayi hakuri, bana son wannan rigimar taka. Wannan ma ai ba wani abu bane da za a daga tunda daga yaranta har nakan duk ‘yayanka ne.’
Muryarsa a makogoro yace ‘Shikenan Hajiya.’ Ya mike tsaye yana cewa ‘Bari naje wajen Alhaji mu ci tuwon tare, ko da yake ma a koshe nake me sanyin kawai zan sha
PAGE 84
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Yana shigewa Jidd a ta kalli Hajia tace ‘Kin gani ko Hajia, a kan kayan shiya zai yaga min rigar mutunci, wallahi yaron nan har yanzu bai yi hankali ba.’
Tace ‘Ya fi ki gaskiya, ya zaki karbi kudinsa kuma ki dinga bar masa yara da yunwa?..’
‘Hajia wallahi na gaya miki karya yaran nan suke yi, kawai don sun san za a biye musu ne suke abinda suka ga dama. Idan banda haka ya za ayi na hanasu abinci na bawa su Nawwara tunda ai duk tare suke wuni suna wasansu; kawai dai suna so su nuna su ubansu mai kudi ne.’
‘Ki dai bi shi a hankali kin ji na gaya miki. Bari ma ya fito naji sai yaushe zai kawo min yaran yawon Sallah ko kuma nima laifin naki ne ya shafe ni ya kai yaran wajen waddad da baya son ya bar mata su?’
……..
Haka yana ji yana gani ya hakura ya kyale Yaya Jidda; daman ya riga ya san Hajia ba zata taba bari a ga laifinta ba.
Kamar yanda aka yi alkawari ranar uku ga sallah tun wajen karfe tara na safe ya tafi daukan Khadeeja; da yake sun riga sun yi waya a shirye ya sameta don haka ba tare da wani bata lokaci ba ya daukota ita da mai aikinta Rashida suka kama hanya. Sai da suka tsaya a gidan Mama suka kwashi yara sannan suka wuce gidan Hajia.
Nan suka zauna a parlor ana ta hira yayinda yara suke ta kaiwa da kawowarsu. Jimawa kadan Yaya Jidda ta dubi Khadeeja tana nuna Rashida tace ‘Wannan yarinyar taki kuwa zata iya wani aikin kirki? Kada fu kuje a kama ku da child abuse?’
Tayi dariya duk da yanda maganar ta bata mata rai tace ‘Ah haba dai, shekarunta fa sha biyar yaya don dai kawai bata da girma ne. Aiki kam ta iya sosai ko a gida ma Mommy ta koya mata.’
‘To amma idan Habi ta dawo sai a mayar da ita ko? Tunda na ji Habi din tace baku da wata matsala da ita kuma tana nan itama tana shirin dawowa.’
‘Uhm, sai a hada biyu ma tunda kin ga ga hidimar gida ga ta yara, kuma ina zuwa makaranta.’
‘Haba wace hidima ce sai an hada ‘yan aiki har biyu a wannan gidan? Hidimar har nawa take?’
Kafin ta bata amsa Mustapha ya shigo yana cewa ‘Ku tashi mu tafi ko, don na san kuna da aiki a gidan nan don duk yayi kura.’
PAGE 85
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Suka fara shirin mikewa yayinda ita kuma Yaya Jidda ta kalli Mustaphan tace ‘Na ga kun samo ‘yar aiki, Baba Habi ma fa tana nan tana shirin dawowa.’
Yace ‘Ah ai kawai sai kice mata tayi zamanta tunda dai gaskiya bamu da inda zamu ajiye ‘yan aiki har biyu.’
‘Da nace ta mayar da wannan din idan Baba Habi ta dawo?’
‘To gata nan kuyi magana idan ta fi son Baba Habi din sai a mayar da wannan din.’
Ba tare da bata lokaci ba Khadeeja tace ‘Uhm ai gara a bar wannan din, in ya so in da wata matsala sai nayi magana a nan din a kawo wata.’
Haka dai dole Yaya Jidda ta barsu suka tafi ba tare da ta iya gamsar da su cewa Baba Habi zata dawo ba.
……….
Kamar yanda ya fada kuwa kaca-kaca suka tarar da gidan, sai dai suna shiga suka fara kokarin gyarawa. Kuma da yake yana ajiyesu ya sake fita harda Afaf da Habib aka yi aikin, don haka cikin kankanin lokaci suka gama.
A haka rayuwa ta cigaba; sai dai a bangaren Mustapha idan dai yana gidan ba a saka masa yara aiki, sai dai su suyi ta gara rashida komai ita zasu aika ko su saka. Khadeeja tana son ta tsawatar musu amma tana tsoron abinda ubans zai ce tunda ta ga sun dan sami natsuwa babu wata hatsaniya, bata so ta ja rigima. Don haka haka ta zuba musu ido; abu kadan sai a kwalawa Rashida kira ko da kuwa aikin Khadeejan take yi dole ta bari taje tayi musu yanda suke so.
……….
Ba a dade da sallacewa ba kuma aka bude gari, a hankali kowa ya koma harkokinsa.
Ranar Lahadi da daddare bayan yara sun yi bacci; suna zaune a parlor shi yana kallon balla a Tv yayinda ita kuma take chatting a waya; ta dago daga kallon wayar ta dubeshi tace ‘Babe gobe fa za a koma makaranta.’
Ba tare da ya dauke kai daga kallon TV din ba yace ‘Kin gaya min fa tun last week, kuma na siyo duk wani abu da ake bukata.’
Ta gyara zama ta ajiye wayar tace ‘Nima zan shiga school din na gano, wata kila an kafe timetable, amma sai wajen goma zan fita.’
‘Ok, to zaki dawo kafin 12:30pm kenan ko? Saboda dauko ‘yan makaranta tunda ni kin ga ina office.’
PAGE 86
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
‘Eh, zan yi kokari na dawo kuma idan ban dawo ba