NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 33 of 105

a mana indomie amma idan mun je ba a dafa bana, bakin shayi ake bamu da ragowar kosai ko kunu.’ Ya dauki shukra ya ja hannun Nasreen yana cewa ‘ku zo muje.’ Bayan sun gaisa da Hajia tace ‘To ka barsu suje gidan Jidda ta dafa musu indomie din su karya sai su dawo ko? Yunwa suke ji gasu nan.’ Nan suka yiwa Hajia bayanin abinda ake basu idan suka je gidan yaya jidda; itama tayi mamaki sosai. Tace ‘To me yasa baku taba fada ba?’ Nasreen ta zumburo baki tace ‘Yaya Meena ce tace duk wanda ya fada sai taci ubansa ta karta masa rashin mutunci don ta san mu da tsinin baki.’ Daga Hajiyan har Mustaphan mamaki ne ya kamasu, Meena itace babbar ‘yar Yaya Jidda. To amma me zai sa tayi haka bayan Jiddan da kanta ta gayawa Hajia ya turo kudin indomie da kayan karin kumallon yaran? Tace ‘Lallai daga Aminan har Jiddan zasu zo su sameni.’ Saboda tsabar takaici Mustapha kasa magana yayi. A nan ya sake bada kudi Habib ya fita kanti ya siyo musu indomie, yana kawowa Afaf ta dafa musu da kwai tunda dama da akwai kwai a gidan. Haka ya saka su a gaba duka saida suka karya azumin suka ci suka koshi. Nan ya zauna suka cigaba da hira wajen Hajia tunda shima Alhaji ya fice; sai dai har la’asar ta kawo jiki Yaya Jidda bata zo gidan ba saboda yaronta Abdallah ya shigo gidan lokacin suna cin indomie shima ya zauna aka ci da shi kuma yana gamawa ya koma gida ya gayawa uwarsu Abban Afaf ya zo harma ya saan dafa musu indomie da kwai. Don haka tana sanetaki zuwa saboda rashin gaskiya. Haka ya wuni a gidan ransa a bace yana tunanin mafita; tabbas duk Khadeeja ce ta janyo masa wannan wulakancin. Tunda da ta dawo babu wanda zai yi wa yaransa wannan wulakancin, Kuma shi ya tabbatar ta sami lafiya ko daga ganinta ma ai an San kalau take PAGE 77 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) To yanzu ya zai yi da yaran? Idan ya tafi dasu ba zasu barshi ya zauna a nutse ba, kuma ma ya san Hajia ba zata yarda ya tafi dasu gida su zauna tare da shi ba. Sai dai kamar yanda ta riga ta fada yaje ya siyo abubuwan da suke bukata ya kawo ita sai ta dinga dafa musu kafin Baito ta zo; domin itama Baito din mijinta ne bashi da lafiya take jinyarsa shi yasa ba zata iya zuwa da safe ba. La’asar tana matsowa ranshi ya sake baci, kuma har loakcin Yaya Jidda bata iso ba. Bayan ya idar da sallar la’asar yana zaune a kan dadduma yana tunanin mafita Habib ya shigo ya sameshi. Bai dade da zama ba yace ‘Abba da ma ka kaimu gidan Mama, ka ga dama mun dade bamu je ba tunda muka koma gida.’ ‘Um, to ai da sallah zaku je ko? Ko ba kwa son zama a nan din ne? ai ka ga yanzu Hajia da kanta zata dinga baku breakfast din ko?’ ‘Um, nan din ma muna son zama amma can din ma muna so, in ya so idan Anti Khadeeja ta dawo sai mu dawo.’ Nan sauran yaran suka shigo suka saka shi a gaba a kan su gidan Mama suke so suje; shi din ma yana so ya kaisu don ya san ba za a barsu da yunwa a can ba tunda ko babu mai aiki akwai ‘yan mata. To amma yanzu hakan yana nufin kenan ba za a iya rike masa yaransa a gidansu ba ko me? Ita kuma Yaya Jidda me take nufi? Gashi taki zuwa, shi kuma ba zai je gidanta ba don ya fi so tazo suyi a gaban Hajia. Haka dai yaran nan suka saka shi a gaba dole ya amsa zai wuce da su. Itama Hajia da ya gaya mata zai kaisu sai da ta nuna bacin ranta don gani take kamar fushi yayi da yanda ya sami yaran, sai da Alhaji ya sa baki kuma suka ga nasreen tana nema ta saka musu kuka sannan suka bari ya kwashi yaran suka wuce gidan Maman su Ma’u. PAGE 78 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Duk da bai ce mata zai zo yau din ba amma dai haka kawai zuciyarta take gaya mata zai zo tunda an bude gari kuma tun wancan lokacin da aka bude gari basu hadu ba. Ta san dai yana jin haushinta daga yanda yake amsa wayarta amma ta nutsu a zuciyarta cewa zai zo din. Tun wuri ta tashi tayi wanka ta shirya don ya sameta a shirye; sai dai ga mamakinta har azahar tana zaune a parlor tana ta faman duba waya, duk wanda ya buga gate da hanzari take tashi ta bude tana saka rai Mustapha ne amma har la’asar bai zo ba. Dab da la’asar tana zaune a parlor tana ta faman latsa waya tana duba whatsapp ko ya bude sakon da ta tura masa amma ga mamakinta har zuwa lokacin bai bude ba. Mommy ce ta fito daga dakinta; har ta kama hanyar kitchen sai kuma ta kula da Khadeeja a zaune a parlor din. Ta dawo ta tsaya tace ‘Ya na ganki a nan, ina Nabila PA din taki?’ Tayi dariya tace ‘Tana can tana abinda ta saba wato bacci.’ Ta wuce kitchen ta barta a nan, jimawa kadan ta fito ta dawo parlor din ta zauna a kan three seater daga bangareb da yafi kusa da single seater din ta Khadeeja take zaune. Ta dan yi gyaran murya tace ‘Uhm, ai na zata Mustapha zai zo yau din, ko sai da yamma zai zo?’ Ta dan gyara zama tace ‘Umm! Ina jin dai sai da yamman, watakila gidansu ya wuce tunda shi da yara ne.’ ‘Um to bari mu gani. Amma dai kuna waya ko?’ ‘Eh, jiya da daddar
🏠