cewa Mommy, ni dadi miji zan bi mijina kenana ko me?’
‘Ba wani dadi miji, ai aurene kuma itama ta sani.”
‘To gaskiya dai ka bari sai bayan sallar kawai.’
Haka dai suka dauki lokaci suna waya ba tare da ta amince zata dawo din ba, maimaita mas kawai take sai bayan sallar. Don haka kusan a fusace ya katse wayar ba tare da sun yi wata sallamar kirki ba.
PAGE 74
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Ta jefa wayar a kan gadon kusa da ita ta ja tsaki, sai kuma ta kifa kanta a kan pillow sai hawaye. Ta godewa Allah nabila tana dakin Mommy tana bacci da sai ta gayawa Mommy tana kuka. Ta fara nadamar sakawa da tayi Mommy tace ta zauna a gida har bayan sallah, yanzu gashi yana fushi da ita. Ita bata zata wannan abun zai sa yayi fushi ba don da ta san zai yi fushi ma da ko gidan ba zata taho ba zata hakura yaje ya daukota. Bata sani ba ko zata iya jure jinsa a cikin damuwa har na tsawon sati biyu ko uku, amma dai zata gwada. Don da kunya tace a barta sai bayan sallah sannan yanzu kuma ta zo tace zata koma.
Haka ta karasa wunin ranar cike da damuwa da nadamar zaman da ta zaba zata yi a gida.
Haka ta cigaba da hakuri tana buga masa waya wanda kullum idan ta buga gaisawa kawai suke yi babu wata magana mai dadi, kamar ma shi dole take masa. Abun yana matukar damunta don haka ta fara rama wadda Mommy ta zata don ta cigaba da azumi ne tunda ta sami lafiya; idan tayi zuru-zuru aka yi magana sai tace azumin ne da wahala.
____
Tun da ya kaisu gidan Hajia bai sake zuwa ba tunda garin a rufe yake ba a fita, sai yau asabar a lokacin saura sati daya sallah.
Yana fita ya tsaya a shagon telansa ya karbar musu dunkunan kayan sallansu wanda tun kafin a fara azumi ya kai; wanda harda na Khadeeja a ciki, ya tsaya aka bashi leda ya ware nata wadanda bashi da niyyar kai mata gidansu. Ya dai yarda zai ajiye mata a dakinta duk lokacin da ta dawo ta gani.
Yana karba kai tsaye ya wuce gidan Hajia cike da kewar yaransa.
Tun daga nesa ya hango Habib a zaune a kofar gida tare da wani yaro, ba wasa sukeyi ba a zaune suke kawai sun yi shiru kowa da abinda ya dameshi. Kafin ya karasa tsayar da motar ya taso da fara’arsa; ya gyara tsayuwar motar ya bude kofa yana sake karewa Habib din kallo wanda ya yi zuru-zuru kamar wanda ya kwana da yunwa.
‘Abba sannu da zuwa.’ Muryar Habib ta katseshi.
‘Yauwa Habib, ya naganka kamar kana jin yunwa ko azumi kake ya fara baka wahala tun da safe haka?’
Idonsa ya dan yi rau-rau yace ‘Eh, azumi nakeyi.’
‘To baka yi sahur bane?’
PAGE 75
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
‘Ba sosai ba, bakin tuwo ne kuma bana ci gashi kuma babu wani abincin a gidan sai shi, na dan ci kadan dai.’
‘To ba sai ka fasa yin azumin ba? da safe kayi breakfast.’
‘Hajia ma haka tace na fasa yin azumin amma ni nace zan yi, idan ma ban yi ba ba abinci zan samu ba sai an sha ruwa. Tunda muka zo ma sau daya na sha azumi.’
Cike da tsananin mamaki yace ‘Ban gane ba abincin kake samu ba sai kace wani almajiri? Ba a baka abinci ne a gidan? Ina baito?’
‘Ai Baito sai da rana take zuwa, kuma safiya tana yi Hajia take cewa mu tafi gidan Anti Jidda muyi wanka a can muci abinci a can. Kuma idan mun je sai Anti Jiddan tace babu abinci sai dai kawi wata ran ta bamu bakin shayi da ragowar kosai ko doya. Idan kuma mutum ya dameta sai ta yi masa fada, itama Shukra da Nasreen ragowar kunu ne kawai ko kuma idan an yi sa a an rage abincin shan ruwa shine ake basu.’
Mamakinsa ya karu, yace ‘A’a, ai na turowa Anti Jidda kudi a sayi indomie da cornflakes harda madara, ba a siya ba ko me ya faru da su.’
Ya dan zaro ido ‘Tab, tunda muka zo bamu taba cin indomie ba ko cornfalkes. In an sha ruwa dai da yake muna gidan hjia shine aka hada mana shayi da madara harda kwai ma ake soya mana da kaza, amma dai da rana babu wanda yake bamu abinci. A wajen Hajia ma muke shan ruwa tare da ita da Alhaji.’
Yayi matukar mamaki kuma ya ji tausayin Habib; amma kuma yana matukar mamakin yanda za ayi ace Yaya Jidda ta bar masa yara da yunwa. Ranar da ya kawosu bayan ya tafi ta kirawoshi tana tambayarsa kudi a sayi kayan shayi da indomie, kua a take ya tura mata naira dubu goma don a siyo da wuri. To me ya faru da kudin da ake hora masa yara da yunwa?
Tare suka jero da Habib din suka nufi cikin gidan, suna daf da shiga suka ci karo da Afaf tare da Shukra da Nasreen kowacce sanye da hijabinta, nan da nan suka fada jikinsa suna murna ‘Abba, Abba.’
Bayan ya amsa gaisuwarsu yace ‘Ina zaku je?’
Afaf tace ‘Gidan Anti Jidda zamu je suyi breakfast.’
‘Ke kina azumin ne?’
‘Eh ina yi.’
‘To ku zo mu wuce ciki kuyi breakfast din a nan.’
PAGE 76
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Nasreen tayi dariya tace ‘Tab ai babu abincin, da an gama shan ruwa Baito take juye duk wani ragowar abinci ta tafi da shi. Kuma Hajia cewa take muje gidan Anti Jidda a daf