i kamar yanda take juya Baffansu, kuma gaskiya shi ba zai dau wannan ba.
Haka dai ya gama kwana-kwanarsa ya tashi ya kwashi yaransa suka wuce gidan Hajia cike da takaicin Mommy Khadeeja wadda duk ita ya dorawa laifi, gani yake kamar itace take juya Khadeeja da Baffan gaba daya.
Tuni Mommy ta bada umarni a samo mata ‘yar aiki.
………
Ransa a bace ya shiga gidan Hajia.
Yana shiga ya tarar da Yaya Jidda a gidan ita da yaranta, suna zaune a parlor din Hajia suna hira. A gaggauce yaran suka gaisa da Hajia da Yaya Jidda suka shige wajen Baffa da gudu inda yake zaune yana jiran Kaman dan autan gidan ya dawo daga shan mai ya kai shi unguwa. A nan Mustapha ya zauna wajen Hajia da yaya Jidda, bayan sun gaggaisaya dubi Yaya Jidda yace ‘Ke Yaya sai kace jira kike a bude gari ki taho, har ma kin rigani zuwa.’
Tayi dariya tace ‘Ni dama babu ni a lockdown in dai gidan nan ne kullum sai na zo, Alhaji ma ya gaji ya barni.’
Hajia ta dubeshi tace ‘Ya jikin Khadeejan?’
Ya dan karkata kai yace ‘Da sauki.’
‘Jiya ma munyi waya da Mommyn tata ai, ta dawo gidan ko sai kun fita daga nan zaku daukota?’
‘Mtseww!’ Ya ja gajeran tsaki sannan ya cigaba ‘Daga can muke, wai Mommyn tace bata gama hutawa ba kuma sai an mata wanka da gyara za a dawo da ita zuwa bayan sallah.’
Hajia ta gyara zama ta kama haba ‘Ikon Allah, to kai kuma sai kace me?’
‘To Hajia ya zan yi da su; shima baban nata bayan tuni muka gama magana da shi yace nazo na dauketa ina zuwa kuma ya canza zance; yace wai na barta. Itama kuma Khadeejan kamar haka ta zaba, kin ga kenan babu yanda zan yi da ita. Da ace ma ta bani hadin kai ne da zata iya canzawa Mommyn ra’ayi don kula kamar wannan shirin duka nata ne.’
Kafin Hajia tace wani abu Yaya Jidda tace ‘Ai kuwa lallai shiri, barin ne sai an yi wani wanka da gyara? Lallai matan nan, nifa dama shi yasa yaran ‘yan bokon nan basa wani burgeni, ciki fal iyayin tsiya.’
PAGE 70
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Hajia tace ‘To me suke nufi? Wannan duk ranar da ta haihu ai sai ta shekara sun gyara sannan zasu baka ita. To yanzu ya suke so kayi da wadannan ‘yayan, ko kuwa don ba ita ta haifesu ba? Tunda ia da nata ne hadawa zasuyi da su ko kuma ita da kanta ma ba zata yarda ta tafi ta barsu ba. Wannan ai ba tsari bane ba ma, sai dai da yake dama an bar gidan a hannun mace ai dole a ga son zuciya irin wannan.’
Ya gayara zama yace ‘Hmmm! Su suka sani kuma.’
‘To yanzu ya zaka yi da yaran? Ko kuwa haka zaku hakura kuyi zamanku tunda dama babu fita? Ko kuma nan zaka bar mini su sai muyi zamanmu, ka ga na sha allura a wajen Dr. Nasreen.’
Ya dubi Yaya Jidda sannan yace ‘Da tunani nake na barsu wajen Yaya Jidda sai na koma na dauko musu kayansu, in ya so sai a barsu iyayen Khadeejan muga lokacin da zasu dawo da ita.’
Har hajia ta bude baki zata yi magan Yaya Jidda ta tari numfashinta ‘Eh to kuma ka ga da sai muyi zaman mu, sai dai ka san gidan namu karami ne wajen kwanan zai iya yi musu kadan gaba daya da nawa yaran. Ko nan din ma ka barsu wajen Hajiyan ai duk muna tare tunda kullum ni nake zuwa na tsaya a kan hidimar gidan.’
Suka yi shiru na dan lokaci kowa da abinda yake tunani, jiamwa kadan hajia tace ‘To hakan ma ai yayi, ka bar min su a nan tunda ga baito nan tana nan zata iya duk wata hidimarsu. Tunda ka ga ai ba ma tsari ace kana zaune a gida daga kai sai yaranka yaran ma mata.’
‘Ba damuwa, zan je na dauko kayansu kafin biyar din ta yi.’
Ya tashi ya fice wajen Alhaji.
Yaya Jidda tabi bayansa da kallo; ya bata tausayi amma gaskiya ba zata karbi su Afaf ba, gara dai a nan din. Can gidanta idama ga nata yaran wadanda iadna ta ga dama nan take turosu wajen Hajia suci abinci suyi koamia sannan kuma a kara mata wasu? Gaskiya ba zata iya ba.
…..
Sai da la’asar ta kusa sannan ya fita yaje gidan ya hado musu kayansu ya kawo sannan ya koma ya barsu a nan.
PAGE 71
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Karo na babu iyaka kenana da ta dauki wayarta ta budo whatsapp ta duba; har yanzu bai amsa messages dinta ba kuma bai biyo whatsapp call din da ta yi masa ba. To me yake faruwa ne? Allah dai yasa lafiya Mustapha yake da shi da yaran. Da farko da taga tayi magana ta whatsapp bai kulata ba kuma ta kirawoshi ta whatsapp din bai daga ba sai ta zata ko fushi yayi, amma dai zuwa yau kwana uku abun ya fara bata tsoro kada taje ko wani abu ne ya sameshi.
Ta riga ta san babuu credit a wyar don haka ko balance ma bata duba ba; shi din ba mutum ne mai son saka mata credita ba, idan ma tayi magana sai yace wa zata kirawo ko kuma me zata yi da data din. Idan aka yi albashi dai idan ta yi magana yana saka mata naira dari biyar, shine zata samu ta raba ta sa data sauran ta dan yi waya. Don haka yanzun ma babu na wayar sai dai data din da ta yi mata saura. Tayi tsaki sannan ta sauka daga kan gadon Nabila inda take kwance ta wuce dakin Mommy.
A parlor t