NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 29 of 105

awa ko tari a cikin yaran sai ya firgita saboda gani yake kamar corona ce ta kwantar da Ummi kuma suma sun shafa a wajenta. Kamar yanda aka sanar ranar asabar aka bude gari, ba karamin dadi wannan budewar ta yiwa Mustapha ba. Tun waje karfe takwas ya shirya sannan ya shirya yaran gaba daya, sai dai da ya duba lokaci yaga safiya ta yi da yawa ya bari zuwa wajen tara da rabi sai su fita; domin so yake su je su dauko Khadeeja sannan idan ya kawota gidan ya barsu ita da yaran ya wuce gidan hajia ya gaishesu. Sai wajen goma saura sannan suka kama hanya. PAGE 67 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid Tun kafin ya gama tsayar da motar yaran suka balle kofofi suka fice suks shiga gidan da gudu, bayan sun gaida Mommy wadda take zaune a parlor tace su shiga dakin Anti Nabila su taso Antin tasu inda take barci. Jinsu kawai tayi a kanta suna shewa, ba shiri itama ta mike. Nan take aka shiga bata labarin abubuwan da suke faruwa a gidan. Itama tayi kewar yaran kuma ta ji dadin ganinsu sosai. A farfajiyar gidan Mustapha ya tsaya sai da Mommy ta tura Nabila ta shigo da shi, ta bude parlor din baki tayi masa iso inda Baffa yake jiransa don shima fita zai yi jin isowarsu ya sa ya tsaya. Bayan sun gaisa Baffa ya tambayeshi wajen su Alhaji sai yayi gyaran murya yace ‘Yauwa, ina ga zaka bar Khadeejan ta dan kara kwana biyu don mahaifiyarta tace akwai abubuwa suke yi na gyara wanda al’ada ta tanada. Don haka ina ga ka barta ta dan kara kwana biyu mu gani.’ ‘Eh, kuma da zuwa mukayi mu tafi da ita Baffa.’ ‘Allah sarki, ina ga a dan daga musu kafa su gama shirye-shiryensu, ba zasu dauki lokaci ba suma na sani in sha Allah.’ Babu yanda ya iya kwarjinin Baffa ya sa ba zai iya yi masa wani dogon musu ba, don haka sai kawai ya sunkuyar da kai. Baffa yayi masa sallama ya fice ya barshi a nan cike da takaici; yaya Baffa zai yi masa haka? Wannan din shawarar Mommy ce ko kuwa dai Khadeejan ce bata son ta koma? Amma dai bari Khadeejan ta fito ya ji daga bakinta. Ya gyara zama ya hadiye malolon da ya tokare masa makogoro ya dana saita fuskarsa da ya ji motsi ana taba kofar daga cikin gida, ya mike ya koma kan kujerar zaman mutum daya ya zauna. Khadeeja ce ta shigo da sallama, bayan ya amsa ta nemi guri ta zauna a kan three seater ta gefen da ya fi kusa da shi, bayan sun gaisa tace ‘Ya kuke kai da yara? Sun ce min ku kadai ne a gida ko gidan Hajia baka kaisu ba.’ ‘To ina zan kaisu gari yana kulle, dole haka muka zauna mu kadai; don ma dai Ummi tana taimakawa, jiya ne kawai da shekaranjiya aka ce bata da lafiya.’ ‘Allah sarki ai iyayenta suna mana kirki gaskiya, Allah ne kawai zai biya su.’ PAGE 68 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Suka yi shiru na dan lokaci; idan ma da yana da niyyar gaya mata wasu kalamai masu dadi to Baffa ya goge masa haddarsu, yanzu haushin kowa ma yake ji. Sai dai fatansa daya ya ga ko zai iya tsaran Khadeejan ta canza wanna tsarin don yana jin idan tace tana son ta koma ba za a hanata komawa ba. Yace ‘Uhm, da ni fa zuwa nayi mu tafi amma na ji Baffa yace kamar zakiyi wanka ne ko gyara wai sai an kwana biyu zaki dawo.’ Ta dan gyara zama ‘Eh, Mommy tace a barni sai nayi wankan jego kuma dai da ‘yan gyare-gyare na kara hutawa sai na komawa.’ ‘Wai baki gayawa Mommy cikin bai karasa wata uku ba ma, na zata haihuwa ake wa wankan jego. Ke dai idan akwai wani dalili ki gaya min sai muga yanda za ayi.’ Tayi ‘yar dariya ‘Shine dai dalilin gashi na gaya maka, don kaga har yanzu ma ban gama jini ba kusan kwana biyar kenan.’ ‘Uhm! To yanzu babu yanda za ayi mu koma yau, na san ai duk wani gyara ba zai gagare ki ba tunda kin sami lafiya ga laulayin ma yanzu babu.’ ‘Gaskiya kayi hakuri kawai muyi yanda Baffa ya fada, kwana nawa ne zaka ga ma na dawo gidan.’ Ya sunkuiyar da kai; tabbas wannan tsarin na Khadeeja ne sai dai bai san laifin me yayi mata ba take son tayi purnishing dinsa haka. Muryarta ce ta katse masa tunani ‘Kada ka damu in sha Allahu zuwa bayan sallah zan dawo, ka ga kafin nan ma Mommy ta samo min mai aiki.’ ‘Bayan sallah? Haba! Wajen sati uku fa kenan? Ai na zata duk inda aka kai nextweek kin gama hutawar. Kuma mai aiki ai Habi zata dawo bayan sallah ko?’ ‘Ban sani ba, wai dai don kada ta bani mamaki gara a samo min wata runda ga aikin gida ga hidimar yara sannan ga makaranta zan koma idan an bude gari ka ga ina bukatar taimakon mai aiki ko.’ Sai a lokacin ma sannan ya tuna ashe tana zuwa jami’a; amma dai shi har yanzu bai gane dalilin da yasa ba zata koma yau din ba har sai nan da sati biyu. Ya dai fahimci so take kawai tace aikin gida da na yara ya mata yawa, kuma shi bai ga wani wahala a ciki ba tunda Ma’u ma ko sau daya bata taba daukan mai aiki ba haka take komai da kanta. PAGE 69 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Kawai dai ya fahimci Mommyn Khadeeja tana da son zuciya da iko shine take son ta juya sh
🏠