NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 28 of 105

n kula. Bata ma tsaya ta saurari amsarshi ba ta koma ta kwanta ta rufe ido. Nan ya tsaya yana kallonsu cike da mamaki; wai su yaran nan me yake damunsu ne? yanzu zasu ce zasu yi abu kafin wani lokaci sun canza ra’ayi. Gaskiya ya jinjinawa mata, ai idan ba mace ba babu wanda zai iya raino; jiya fa Afaf fushi tayi da shi saboda bai tasjeta ba amma yau kuma ita yake tashi tana ce masa wai yau bai kamata tayi azumi ba. Yana fitowa daga dakin ya hada indomie din ya juye a tukunyar ya rufe ya ajiye musu a kan idan gari ya waye sa ci abincin safe, sannan ya dawo ya karasa sahur dinsa. ……… Kamar yanda suka saba yau din ma da tunasuba suka tasheshi a kan yunwa suke ji, haka ya shiga kitchen Afaf ta taimaka masa ya hadawa kowa cereal domin duk sunce ba zasu ci indomie ba don tayi sanyimkuma basa son dumame, da ya takura musu ma sai Nasree cewa tayi ‘Abba kai fa idan ka dafa indomie bata dadi, ka bari idan Anti ta dawo ta koya maka.’ Don haka kawai sai ya mayar da indomie din ya rufe. ……… Tun wajen goma na safe yake sa ran shigowar Ummi don ya riga ya gaya mata yau ma tazo, sai dai ga mamakinsa har wajen sha daya saura bata shigo ba; gashi har na fara yi masa korafin yunwa kuma ana bashi warning ba za aci indomie ba sai da taliya ko macaroni. Yana shirin fita ya je gidan su Ummin aka buga gate; kanwarta ce wadda suke kira Nana, wadda bata fi shekaru bakwai ba. PAGE 65 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Bayan ta gaisheshi tace ‘baba yace na gaya maka Ummi ba zata sami zuwa wajen su Afaf ba yau don ta tashi da mura me zafi tana kwance, yace sai dai ko zuwa gobe idan ta sami sauki zata shigo.’ Jiki a sanyaye ya amsa ‘To, kice ina mata sannu kuma kice ina gaida Baban.’ Ya rufe komar ya koma cikin gidan gwiwarsa a sanyaye; ya zai yi da yaran ga gidan kace-kaca musamman kitchen din, ko ina kwanuka. Tukunna ma; mura fa aka ce Ummi take yi. Inna lillahi wa inna ialaihi raji’un! Allah ya sa yarinyar nan ba Covid-19 ta kwaso ba garin yawon tsiya, don tabbas idan ta kwaso to ta shafawa yaransa. ‘Subhanallah!’ ya fada a fili yana daf da karasawa cikin gidan. Bayan ya shiga gidan yayi musu bayanin Ummi bata da lafiya. Yana ji yana gani haka ya hakuri Afaf ta dafa musu jallof macaroni, bayan sun gama ci kuma ta kwaso wanke-wanke ta fice da shi waje ta wanko; duk da koakrinsa na hanata amma haka ta dage ta wankesu. Sannan ta umarci Halifa da ya share cikin gidan wanda shima nan da nan yayi, suka dawo suka zauna. Wunin ranar haka yayi shi yana gyangyadi domin ko ya rufe ido da niyyar bacci haka wani zai rugo kai kara har Afaf din ma, ko kuma azo ace masa ana bukatar wabi abu; ita kam Shukra haka kawai ma da taga ya shiga daki binsa takeyi, idan kuam a parlor ne da ya rufe ido zata kirawo sunanshi tace ya bude ido ta nuna masa wani abu. Haka har aka kusan magriba sannan ya samu da taimakon Afaf ya soya musu dankalin bature kuma ya dafa musu indomie ta dan yi dadi. Wuni yaran suka yi suna ciye-ciye amma ko da ka sha ruwa ma saka shi suka yi a gaba ana cin abinci suna masa surutu da rigingimu kala-kala; shi dai zai iya cewa ba a hayyacinsa ya ci abincin nan ba. Haka ya dinga ci yana kwarewa. Ya cika bakinsa da dankali Shukra ta mike ta jefar da dankalin da yake hannunta tana dafe duwawu tana cewa ‘Kashi Abba.’ Ji yayi wani malolo ya taokare masa makogoro; wai ita Shukra bata tashi kashi ne sai mutum yana tsaka da wata sabga? PAGE 66 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Lallai yanzu ya tabbatar Khadeeja tana da kokari don kusan tunda aka fara azumin nan sai ana tsaka da cin abinci sannan Shukra take cewa zata yi kashi kuma ta tashi ta sakata; idan ma tayi jinkiri shine yake nuna damwarsa. Ya dubi Afaf wadda ya kula kamar ta bata rai me yace ‘Yaya Afaf ki saka kanwarki a toilet tayi kashi.’ Ta tashi a fusace ba tare da ta amsa ba ta dire kofin shayin da taje sha a kasa, tana daga kafa tayi fatali da kofin shayin ya zube ya fallatsa ya bata Habib wanda yake kusa da ita. Ya mike a fusace yana nunata ‘Dalla malama ji yanda zaki konani da shayi saboda kashin wata.’ Ita din ma a fusace tace ‘To ka matsa mana, ko baka gani ne?’ Abbansu ya bude baki zai yi magana Shukra tace ‘Kashi Abba.’ Ya tuna yanda suka yi cikin dare ya tabbatar bai shirya wanke kashi a parlor ba don haka ya mike ya wucesu ya ja Shukra ya nufi bandaki da ita. Saida ta gama kashin ya wanke mata ya fito sannan ya saka su a gaba yayi musu fada, ya sa Afaf ta gyara inda ta bara da shayi. Ya kurbi shayinsa da ya bari yaji yayi sanyi, haka daiya hakura ya shanye ya dan kara cin abincin. Haka ya hakura ya nemi waje ya zauna yana tunani don zai iya cewa ba kkoshi yayi ba ya dai hakura da abincin ne kawai, haka ya dinga binsu da kallo sunata wasanninsu har loakcin kwanciyar bacci. …….. A cikin wannan halin Mustapha ya karasa kwanaki biyu shi da yaran a jigace, gashi duk wanda yayi atish
🏠