d (Innar su Amal)
‘Kashi zan yi.’
‘To ai ba sai kinyi kuka ba Shukra, sauko muje na saka ki a toilet.’
Ya sauketa daga kan gadon ya ja hannunta suka wuce bandaki, suna shiga ya cire mata wando ya fara kokarin daurata a kan toilet ta dafe duwawu tana juyi tana cewa ‘Ina Fo na Abba a shi zanyi.’
Cikin muryar lallashi yace ‘To ai ba ganshi ba ki yi hakuri ki hau toilet.’
‘Muje ka duba bandakin Anti fo dina yana nan Abba a shi zan yi kashin.’
Ya dauketa gaba daya ya dora a kan toilet yana cewa ‘To ki gama kashin kada ya fito in ya so idan kika gama sai muje mu dubo fo din.’
Kafin ya rufe bakinsa ta zame ta sauka daga kan fo din, tana kuka. Ta cigaba da bubbuga duwawunta tana shirin ficewa daga bandkin tana cewa ‘Fo na yana bandakin Anti bari na daukoa shi zan yi kashin.’
Cike da tsananin mamaki da takaici yake kallonta, ga dukkan alamu kashin ya matseta amma ita bata da niyyar zama a toilet din nan so take dole sai ya dauko mata fo; fo din da ya riga ya jefar ba tare da kowa ya sani ba. Ya kai hannu ya damkota tana shirin ficewa daga bandakin, ya mayar da ita kan toilet din ya zaunar da ita yana cewa ‘Anti ta kulle dakinta ta tafi da mukullinta sai ta dawo zata bude mana, kiyi kashin a nan.’
Ta sake direwa ta sauka daga kan toilet din tana buga duwawu harda juyi saboda yanda kashin ya matseta tana cewa ‘Ka zo na nuna maka Abba bata rufe ba, a bude dakin yake dazu nma na shiga.’
Kafin yayi wani abu kashin ya kwace mata, dan kadan ya fado ya zame daga duwawunta ya bata tsawon kafarta sanna ya dire a kasan toilet din. Yayi wuf ya dauketa ya daka mata tsawa yana cewa ‘Ki zauna a nan kiyi kashin nace, kalli yanda kika bata jikinki kika bata toilet din da kashi.’
Ta sake fashewa da kuka tana yi tana shessheka, takaici ya sa ko magana ba zai iya yi mata ba don haka ya kyaleta kawai yana tsaye tana rungume da kafarsa yana jira ta gama. Ko minti daya bata yi ba tace masa ta gama kashin, ya leka toilet din shi bai ga komai ba. Yace ‘Idan fa kika yi min kashi a wando zaneki zan yi Shukra gara ki gama kashin nan a nan.’
‘Na gama.’
PAGE 63
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Ya dauketa cak ya ajiyeta a wajen wanka, ya dauki sprayer din yin tsarki ya fesa mata ruwan da karfi ta yanda ruwan ya wanke kashin jikinta, sannan ya sabi sabulu ya wanke mata da hannunsa. Ya dauketa ya fitar da ita ya shiryata ya kwantar da ita sannan ya koma bandakin; ya tsaya daga bakin kofa ya karewa bandakin kallo. Ga guntun kashin da ta jefar a kasa sannan gashi duk ta shafe na jikinta a jikin toilet din bandakin har ya fara wari. Ya yi tsaki ya juya ya fice, jimaw kadan ya dawo dauke da tissue paper, ya warware kusan rabinta sannan yayi amfani da ita ya dauke guntun kashin jefe a toilet din. Sannan ya sake warwarowa ya goge toilet din yayi flushin sannan ya fito ya dawo parlor ya zauna cike da takaici da gajiya.
A nan a parlor din bacci ya kwasheshi, watakila saboda tsabar gajiya domin bacci yayi mai nauyi sosai. Maganar Shukra ce ta farkar da shi wadda taje tashinsa tana sanar da shi zata sha shayi. Ya tashi zaune yana mittsike ido, ya lalubi waya ya duba lokaci; karfe ukun dare saura. Haka ya tashi ya hado mata shayin ya zo ya bata ta shanye sannan ya ja hannunta suka koma dakin. A nan ya tarar ita da Nasreen duk sun riga sun yi fitsarinsu a kwance; ya canzawa Shukra kaya ya lallaba ya kwantar da ita a gefen da bai jike ba kusa da Afaf. Ya dan tsaya ya karewa dakin kallo, sai kuma ya juya ya fice.
Gaba daya kansa ya kulle; wai dama haka yaran nan suke ko kuwa don sun ga mahaifiyarsu bata nan ne kuma Khadeeja bata nan suka saka shi a gaba suka hanashi sakat, domin wasu abubuwan da suke yi ma kamar da gayya musamman Shukra.
Har zai zauna a parlor din kuma ya tuna sai ya dafa abinda zai yi sahur don haka y wuce kitchen, ya janyo indomie ya debo park uku sannan ya nemi tukunya ya dora; Afaf da Habib sun yita fushi a kan jiya bai tashe su sahur ba don haka yau idan ya gama dafa abincin sai ya tashesu. Nan da nan ya dafa idomie din ya zubawa kowa a plate ya dora a dining table sannan ya hadawa kansa shayi. Bayan ya gama ya wuce dakinsu, ya kunna fitila sannan ya karasa ya tashi Afaf, ta zauna a kan gadon tana mittsike ido sanna ya wuce ciki ya tashi Habib.
PAGE 64
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Yana juyawa ya bude ido yace ‘Abba asuba tayi ne?’
‘No da saura, sahur zamuyi tukunna ga indomie can na dafa.’ Ya bashi amsa.
Ya gyara kwanciya yana janyo abun rufarsa yana cewa ‘Ni ba zan yi azumi ba Abba, sai gobe.’ Ya rufe ido ya cigaba da baccinsa ba tare da ya sake bi ta kan Abban nasa ba.
Afaf wadda take zaune a bakin gadonsu ta juyo tace ‘Abba wai sahur zamu yi.’
‘Eh.’
‘To Abba ai jiya ne ya kamata muyi azumi kuma baka tashemu ba, nima dai gaskiya yau ba zan yi azumin ba sai gobe. Dama haka mukeyi da Anti; muyi daya mu sha daya.’ Ta fada cikin halin ko i