NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 25 of 105

sa bata gane kulawarsa a gareta. Don haka ta bar wannan a ranta tana fatan idan an sami mai aiki ya zama suna samun lokaci a tare to zata fuskanceshi. Muryar Mommy ce ta katseta tana cewa ‘To yanzu yaushe zai zo ya daukeki?’ Ta kalleta suka hada ido ta sunkuyar da kai sanna cikin muryar shagwaba tace ‘Mommy kin ga yanzu mai aikin bata dawo ba, kuma na gaya miki shi ba zai tayani komai ba kuma ba zai bari yaransa su tayani ba. Kawai ki barni sai bayan sallah ko kuma duk lokacin da mai aikin ta dawo ko aka sami wata.’ Mommy ta jijjiga kai tace ‘Na fahimceki, amma me kike so na gaywa Baffanku? Shi kuma Mustaphan wane dalili za a bashi na rike ki a nan din. Tunda dai ciki ya fice an riga an wake; kuma gaki nan kowa yana ganinki ras.’ Ta karyar da kai kamar abin tausayi tace ‘Umma ni dai don Allah ki san yanda zaki yi a barni na huta.’ ‘To bari mu gani. Idan kuma akwai wani abun da Mustaphan yake yi miki wanda kike so a yi masa magan to kiyi gaya min.’ ‘Babu komai tunda ma bai hana a dauki mai aikin ba, in sha Allahu da ta dawo ko kika samo min wata zan koma., Ta gyara zama ta kafa tagumi ‘Hmma, bari muga yanda zamuyi da Baffan naki tukunna.’ ……… Sai da suka gama wannan hirar sanna ta tuna tunda suka shigo bata ma nemi wayarta ba, ta san yanzu haka Mustapha yana ta faman kiranta. Cikin sauri ta mike ta dauko wayarta daga jakarta, ai kuwa tana dubawa taga missed calls dinsa har guda goma sha daya. PAGE 58 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Tana gani danna masa kira, ko ringing bata yi ba ya dauka ‘Hello, wai ina kika shiga ne naje asibiti ina ta nemanki? Na rasa mai bani tsayayyiyar amsa, sai ce min kawai ake kin tafi da Anti Iyami, na zata gida zata kawo ki na dawo gidan kuma baku zo ba. Kin san ina neman haukacewa na rasa wanda zan kira don ban san me zan ce musu ba.’ ‘Subhanallah! Kayi hakuri Babe, wallahi ka ganni nan ai gidan Mommy ta kawo ni. Na kirawoka bata shiga ba kuma shine na jefe wayar a jaka na manta sai yanzu da na fito daga wanka na tuna.’ ‘Amma shine baki gaya min ba? Kin san wulakancin da aka dinga yi min a checkpoint kuwa?’ Ta tausasa murya ‘Sorry Babe, wallahi laifina ne don tun a asibitin Anti Iyami tace na kirawoka sai wayar ta ki shiga.’ Ya dan saki numfashi ‘To me yasa baku taho nan ba ko kuma a jirani na zo? Me ya sa za a kai ki gidan Mommy?’ Ta dan yi shiru, shima bai yi magana ba yana sauraronta; ta murgude baki kamar yana kallonta tace ‘Ai ka san dai idan an haihu ana zuwa wanka gida, may be shi yasa da suka yi waya Mommy tace a kawoni gida.’ ‘To kuma shine aka rasa wanda zai gaya min.’ Cikin kosawa tace ‘To ba gashi na gaya maka ba, kuma ai nace maka mantawa nayi.’ Ya dan ja numfashi ‘Uhm! To ya jikin naki? Shike nan an gama yi miki alluran?’ ‘Na sami sauki, ga ragowar magungunana na taho da su daman yawanci na kwana bakwai ne. amma na sami sauki.’ ‘To idan an bude gari sai na zo na daukeki, inaga ranar Saturday zasu dan bude mu, nan da kwana uku kenan.’ ‘Uhm, to ka dai zo amma gaskiya sai bayan sallah zan dawo kafin nan na dan huta na gama arba’in tunda ka san shima barin ai sai an yi wanka.’ ‘Barin, gaskiya ban taba ji ba. Ma’u ma fa su biyu tana yin barin amma na biyun babu wanda ma amuka gayawa a nan tayi zamanta ta cigaba da hidimarta. Hutawa kawai tayi na kwana biyu.’ ‘idan ka zo dai mayi maganar.’ Ta tamabye shi yaran ya bata su suka gaisa sannan suka yi sallama suka ajiye waya. ………. Tunda yake bai taba ganin son zuciya irin wannan ba, ya za ayi a dauke masa mata kuma ace sai bayan sallah zata dawo? Kawai saboda tayi bari. Asma’u ma ai tayi bari har sau biyu ma; PAGE 59 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Asma’u ma ai tayi bari har sau biyu ma; na farkon shine bayan haihuwar Habib, bayan anyi mata wankin ciki a ranar suka dawo gida. Ko maganar taje gidansu ma ba a yi ba kawai dai an kawo mata kanwarta tunda dama tana da mai aiki. Na biyun kuwa ma bayan haihuwar Nasreen babu wanda suka gayawa, suna zuwa asibiti aka ce musu ya fice gaba daya ba sai an yi wankin ciki ba aka basu magunguna suka dawo gida. Kawai dai ya san ba zata koma dakinsa ba sai bayan kwana arba’in, kuma bashi da matsala da wannan. Amma su iyayen Khadeeja saboda son zuciya sai akwai su dauke ‘yarsu? Kuma ko gaya masa ba za ayi ba. Haka ya gaji da sake-sakensa ya sake daga wayar ya kirawo Alhaji ya gaya masa, don bai gaya musu cewar a asibiti ma ta kwana ba yana so yaje da safen ya gani tukunna. Shima Abban ya nuna rashin jin dadinsa da aka tafi da ita, musamman da ya gaya masa basu ma tambaye shi ba suka tafi da ita. Bayan sun gama waya da Alhaji ya kirawo Ummansu itama ya sanar da ita. Suma su Afaf saida yayi musu bayani don tunda ya dawo basu ganshi tare da Khadeeja ba suke ta faman yi masa tambayoyi. Babu yanda za ayi ya iaya brin Khadeeja ta zauna a gidansu,
🏠