NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 24 of 105

na fitowa daga dakin yayi alwala ya tada sallah a dakinsa, yana zaune a kan dadduma yana azkar Nasreen ta turo kofa ta shigo dakin, ta karaso ta fada jikinsa tana cewa ‘Abba na tashi, baka dawo mana da Anti Khadeeja ba?’ ‘Eh, sai an jima.’ Ya fada yana tureta. ‘Ki je kice Ant….’ Sai kuma ya tuna Antin bata nan don haka ya gyara zance yana kokarin mikewa ‘Muje na wanke miki jiki ki canza kaya sai kiyi sallah.” ‘Abba ni yunwa nake ji.’ PAGE 55 MIJIN MARIGAYIYA A HAUSA NOVEL BY SAKINA YAZID (INNAR SU AMAL) Ya bata rai yace ‘Sai an canza kaya kuma kinyi sallah.’ Haka yayi ta fama da yaran nan, gashi ita Afaf ma fushi take da shi saboda bai tasheta sahur ba tunda Anti tana tashinta tana yin azuminta. Sai wajen karfe takwas na safe sannan ya tashi ya koma ya roko Baban Ummi ta shigo ta karbi yaran don yana son ya tafi asibiti wajen Khadeeja. Yana shiga dakinsa ya zauna a gefen gado ya dannan mata kira. ------------ Haka Khadeeja ta kwana a asibitin karkashin kulawar Anti Iyami. Tun dare likita ya gama da ita aka bata duk wasu magungunanta, ya sanar da Anti Iyami za a iya tafiya da ita gida. Don haka gari yana wayewa karfe takwas na safe Anti Iyami ta gama aiki zata tafi gida ta shiga dakin da Khadeejan take. Bayan sun gaisa tace ‘Yanzu akwai inda yake miki ciwo Khadeeja.’ Ta jijjiga kai tace ‘A’a, ko ina ya warware, yanzu ma na gama breakfast din da kika aiko min da shi.’ ‘Ok, so ki kirawo Mustapha kice masa zan wuce dake gida sai mu tafi na kaiki gidan Mommy din.’ Bata son tayi magana da shi sai ta je gidansu don haka cikin sauri tace ‘Ai yanzu na kirawoshi bai dauka ba, ina jin yana bacci ko baya kusa da wayar amma na san da ya gani zai kira. Mu wuce kawai tunda tun jiya na gaya masa zamu wuce gidan.’ ‘Ohk, to tashi mu tattara kayan mu wuce. Nima tun dare na kirawo Mommyn naki na sanar da ita, da safe ma munyi waya. Na dai ce mata kada ta kirawoki ne don duk lokacin da na shigo sai na sameki kina bacci, shi yasa nace ta bari idan kin tashi zan kirawota kuyi magan. But ba komai idan mun je zata ganki tunda mun shirya.’ Nan suka hada kayan Khadeejan wadanda daman ba yawa ne da su ba suka shiga motar Anti Iyami suka kama hanya. PAGE 56 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Khadeeja tana zama a mota ta lalubo wayarta ta ska ta a silent ta jefa a jaka don bata so Mustapha ya kirawota a gaban Anti Iyami domin bata san me zai ce ba idan ya ji ta wuce gidan Mommy. Duk inda suka je checkpoint aka tsayar da su da anga uniform din Anti Iyami kuma ta nuna ID card sai a barsu su wuce, haka har suka isa gidan Mommy. Tun suna asibitin Anti Iyami ta snar da Mommy zasu taho don haka kafin su isa an dorawa Khadeeja ruwan wanka, suna shiga ta wuce dakin Mommy inda Azumi mai aikinsu ta sirka mata ruwan a bandaki. Ba tare da bata lokaci ba ta fada wanka. A parlor Mommy suka zauna da Anty Iyami; bayan sun gaisa sun jajantawa juna Mommy tace ‘Ina Mustaphan? Ai na zata tare kuke da shi.’ Ta gyara zama tace ‘Bai zo ba ma yau da safen duk da dai tace ta gaya masa nan zamu huto, amma don Allah kawata a duba yarinyar nan.’ Cike da kulawa Mommy tace ‘In sha Allahu kuwa, kema kin san ba zan barta haka ba ko akwai wata matsala ne da ta samu ko rashin lafiya.’ Ta jijjiga kai ‘Babu fa, kawai dai tace min tana son dawowa gida. Duk dai wasu tambayoyi da zan yi mata nayi ta nuna min babu komai, to amma kin ga akwai yaransa guda hudu. Watakila hidimar gida da ta yaran ce take mata yawa ga ciki shi yasa ta sume masa. Baccin da ta dinga yi kawai ya tabbatar min da cewa bata samun isasshen bacci wallahi, don shi yasa ma naki tashinta kuyi waya. Gaskiya ku bincika, ya nema mata mai aiki ko ya san yanda zai yi da yaransa.’ ‘Umm! To kinga dai idan ma da wata matsala bata fada ba, koda yake kwanaki tace mai aikinsu bata nana abata aron Nabila amma Baffansu yaki amincewa. Watakila saboda babu mai aikin ne abun yayi mata yawa ga laulayi.’ ‘Gaskiya dai ku duba, ko da zata koma ku barta ta huta ta sami natsuwa sannan kuma a daukar mata mai aiki.’ Suka karasa hirarrakinsu daga baya suka yi sallama Anti Iyami ta kama hanya. ....... Bayan ta fito daga wanka ta tarar da farfesun kaza mai rai da lafiya wanda Mommy ta dafa mata sannan ga shayi mai kauri Azumi ta hada mata da burodi a gefe, cikin sauri ta gyarajikinta ta sa kaya sannan ta shimfida dadduma a gaban gado ta mike kafafu ta zauna ta fara ci. PAGE 57 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) A nan Mommy ta shigo ta sameta itama ta zauna, sai da ta gama cin abinci sanna ta fara yi mata tambayoyi. Bata boyewa Mommy komai ba ta sanar da ita halin da ake ciki, ta tabbatar mata cewa idan dai da mai aiki musamman babba wadda ba zata sata surutu ba. Sai dai ta kasa gayawa Mommy cewa gaba daya ma ko da da mai aikin ita ji take kamar ma Mustaphan baya kaunarta, gani take kamar yanda take zama kullum cikin hidima ya
🏠