MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Bayan ya gama rufesu ya zo ficewa daga dakin doyin da yake ta ji ya sake dukan hancinsa; wannan doyin ai sai ya kymburawa mutum ciki. Kamar daga bandaki doyin yake fitowa don haka ya koma ya bude kofar bandakin ya shiga, ya karasa ya leka toilet din ya tarar babu komai a ciki duk da haka dai ya danna flushing ya juya zai fita. A daidai bakin kofa daga jikin bango ya ci karo da fo din Shukra wanda dazu Afaf ta cire wandon Shukra mai dauke da kashi ta jefa a ciki. Pant din yana nan da kashin a yanda ta ajiye har ya fara bushewa amma duk ya dumame bandaki da doyi.
Ya dan ja baya kamar a firgice, to wa Afaf ta ajiewa wannan kashin? Yanzu ya zai yi da shi gashi duk ya dumame gidan da wari. Ya daga hannuwansa ya zuba a aljihu, danshin da yaji ya tuna masa cewa wandon a jike yake da fitsrin Shukra ce ko Nasreen shima bai sani ba. Yayi tsaki ya fito daga bandakin ya wuce dakinsa yana tunanin yanda zai yi da kashin, gashi a jikin pant yake balle ya sa a toilet yayi flushing.
PAGE 53
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Saida yayi wanka ya canza kaya sannan ya fito daga dakin, yana fitowa yaji warin kashin nan har parlor din saboda ya bar kofar a bude. A fusace ya wuce kitchen ya dauko katuwar bakar leda ya zo ya dauki fo din ya kulle a ledar, ya sake dauko wata ledar ya kara kullewa sannan ya dauki mukulli ya bude kofa ya fice ya jefa a shara; gari yana wayewa zai sami yaro ya fitar masa da sharar. Ya san dai Shukra ta iya hawa toilet yanzu, duk da idan ta so rigima sai tace sai ta hau fo amma shi dai ya zubar don ba zai iya wankin kashi ba kuma ba zai iya bari Afaf tayi ba ta zo ta yi musu jagwalgwalo da kashi.
Yana dawowa cikin parlor din ya kalli agogon bango yaga karfe uku har ta wuce, abinda yayi masa saura bai fi awa daya da rabi ba ayi assalatu. Sai a lokacin ya tuna bashi ma da abincin sahur, gashi kuma ko a lokacin ma yunwa yake ji balle yace zai yi dore. Kai tsaye ya wuce kitchen ya dora indomie sannan ya tafasa ruwan shayi; nan da nana ya juye indomie din a plate ya dumama stew ya zuba sannan ya hada shayi, ya kwaso ya dawo dining table ya fara ci.
Tun kafin ya hadiye lomar farko ya fara jiyo hayaniyar Shukra a dakinsu, yana zuba loma ta biyu ta budo kofar dakin ta fito tana kuka tana ‘Antiiii..’
Ya ajiye cokalin yace ‘Menene Shukra?’
‘Shayi zan sha Abba’
Har cikin zuciyarsa takaicinta ya kamashi, to amma ya zai yi da ita? Haka ya kirawota ya zaunar da ita a kan kujera, tun kafin ya gama gyara mata zamanta zarni ya cika masa hanci; sannan ma ya tuna tayi fitsarin kwance. Ya gyara mata zama yace ‘Bari na gama sahur sai na hada miki shayin.’
Ya dauki cokali ya zuba loma a bakinsa yayinda ita kuma ta fara mutssike ido tana kuka.
‘Menene kuma?’ ya tambayeta
‘Yunwa nake ji, shaaayiii.’ Ya duba agogon wayarsa, saura bai fi minti goma sha biyar ba a yi assalatu ga shi baya jin zai kai azumin nan idan bai yi sahur ba, ya kalleta yanda take ta kuka kamar wadad aka ciza. Bai taba jin haushin Shukra kamar yau ba, amma babu yanda zai yi. Haka ya juye mata rabin shayin da ya hada zai sha ya saka mata madara da milo ya mika mata sannan ya cigaba da cin abincin.
PAGE 54
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Yana yi yana kallon lokaci saboda kar a akirawo assalatu. Haka ya ci abincinnan yayi sauri ya kwankwade shayinsa rabin kofa sannan ya dora da ruwan sanyi duk a loakci guda. Yana ajiye kofin aka fara kiran assalatu, ya kwantar da kansa a jikin kujerar yana mayar da numfashi.
Shukra da take kan kujera tana gyangyadi bayan ta shanye shayinta ta taboshi tana cewa ‘Abba kashi zan yi.’
A dan zabure ya dubeta yace ‘Kashi Shukra?’
Cikin halin ko in kula tana murje idonta tace ‘Um.’ Ta fara kokarin sauka daga kujerar da take zaune.
Ya jijjiga kai cike da takaici; su wai yara ba a hutawa da hidimarsu ne? tunda ya dawo daga asibiti ake abu daya gashi duk yana neman fita daga hayyacinsa amma babu alamar sauki. So yake ma ya sami natsuwa ya turawa Khadeeja message ta whatsapp yaga ko tana online amma basu bashi time ba, a halin yanzu ma kansa ciwo yake ga bacci duk kansa ya cushe bai ma san ta ina zai fara ba.
Haka ya bi bayanta har bandaki, Allah ya taimakeshi bata ma nemi fo ba ya taimaka mata ta hau toilet tayi kashinta. Yana zaune a gefen gadonsu yajiyota daga bandakin tana cewa ‘Abba na gama.’
Gaban shi ya fadi da ya tuna wai shi take sa rai yayi mata tsarki; ya juya ya kalli Afaf wadda take baccinta hankali kwance. Ya san idan ya tasheta zata yi mata tsarkin to amma fa itama bata kwanta da wuri ba. Ya jijjiga kai ya mike bayan da ta sake maimaita masa ta gama a karo na uku. Haka ya tashi ya shiga bandakin ya wanke mata kashin ya wanko hannunsa ya fito ya canza mata kaya ya mayar da ita ya kwantar da ita a kusa da Habib saboda katifar kan gadon ta jike; zuwa lokacin masallatai duk sun riga sun tayar da sallah.
Ya