NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 22 of 105

cci kawai.’ Halifa shima ya tashi zaune yana share kwalla ‘Wallahi Abba ni ba zan ma iya baccin ba, Allah ya sa dai kada Anti Khadeejan ma ta mutu ta barmu. Har yanzu idan na tuna Mommynmu sai na yi kuka.’ Kafin yayi magana itama Afafa din hawaye ya fara bin fuskarta, ta sunkuyar da kai ta sa masa kuka harda shassheka. Ji yayi kamar ya dora hannu a ka ya sa ihu; ina ma yaran nana zasu barshi ya huta, yanzu ya zai yi da su? Manyan cikinsu da yake ganin sune ba zasu bashi matsala ba sune suke so su hanashi bacci. Ya karasa ya zauna a kusa da Afaf ya rungumota yana cewa ‘In sha Allahu babu abinda zai sameta, ku daina kuka kuyi mata addu’a Allah ya bata lafiya. Goben nan ma zaku ga an sallamota.’ PAGE 50 A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ta fara share hawayenta, Habib wanda shima ya taso ya dawo kusa da ita yace ‘Abba to ka kirawo mana ita a waya mu yi mata sannu.’ Ya zaro wayarsa daga aljihu yana cewa ‘To ai da bana son kiranta saboda kar na dameta don an yi mata allurai, ban sani ba ko harda ta bacci a ciki. Amma bari na kirawota sau daya idan ta daga shikenan idan kuma bata daga ba sai mu hakura da safe ma sake kira.’ Ya lalubo lambarta ya danna mata kira, sai da wayar ta kusa tsinkewa sannan ta daga. Murya kasa-kasa tace ‘Hello.’ Yace ‘Hello, Khadeeja ba kiyi bacci ba?’ ‘Na dan yi, farkawa dai nayi kuma naji wayar tana ringing. Ai tun dazu aka gama wankin cikin har na dan ci abinci.’ ‘Sannu. Wankin cikin ba wahala kenan?’ ‘Hmmm! Akwai wahala ba kadan ba, kawai dai da an gama aka bawa mutum maguguna sai ya sami relief.’ ‘Sannu. Afaf ce dama ita da Habibi wai ba zasu iya barci ba sai sun yi miki sannu.’ Tayi murmushi mai sauti domin ta ji dadi har cikin ranta, ta tabbatar cewa yaran nan suna kaunarta kuma da zai barta da su komai nasu zai zo da sauki amma shi komai gani yake kamar zata cuce su. Muryar Afaf ce ta katseta bayan da Abbanta ya bata wayar ‘Anti.’ ‘Na’am Afaf, ya aka yi ba kiyi bacci ba.’ ‘Babu komai Anti, ya jikin naki? Ke ya aka yi bakiyi baccin ba? Tayi ‘yar dariya tace ‘Yanzu zan yi Afaf, kuma na sami lafiya don likitan ma ya ce gobe za a sallame ni.’ Suka dan taba hira sannan tayi mata sallama ta mikawa Habib wayar. Bayan sun gama gaba daya ya karbi wayar ya katse yayi mata sai da safe. Ya yi musu sai da safe suka kwanta, har zai kashe fitilar Afaf tace ‘Abba kada ka kashe mana fitilar, in an jima ka zo ka kashe.’ Haka ya bar musu fitilar ya fice. Can bayan awa daya ya gama abinda yake yana so ya kwanta saboda ya gaji ya zo zai kashe musu fitilar, yana kashewa Afaf da Habib suka hada baki a lokaci guda suka ce ‘Abba kada ka kashe fitilar.’ Da mamaki yace ‘Kai! Me kuke baku yi barci ba?’ Afaf tace ‘Abba to ni dai na kasa bacci, da ma zaka taya mu kwana.’ Habib yace ‘Eh wallahi Abba don ni wallahi tsoro nake ji.’ Takaici ya kamashi, to yanzu ya zai yi? Taya su kwanan zai yi ko kuwa barinsu zai yi a haka su PAGE 51 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Takaici ya kamashi, to yanzu ya zai yi? Taya su kwanan zai yi ko kuwa barinsu zai yi a haka suna zare ido yaje ya kwanta? Wannan wacce irin fitna ce a daren nan gashi ya gaji. Baya son barinsu su kadai don haka ya wuce dakinsa yaje ya shirya ya rufo gidan sannan ya dawo nan dakin; katifar Habib karama ce ya san ba zata ishesu ba don haka kawai ya gyarawa Nasreen da Shukra kwanciya ya dan sami waje a gefen gadon ya kwanta bayan Khadeeja ta kwanta a daya gefen. Yayi addu’a ya tofa musu sannan yace kowa ya rufe idonsa kada ya sake jin motsinsu. Tunda ya kwanta yake jin wani dan doyi haka, idan iska ta busa sai ya ji kamar doyin ya buso cikin daki idan iskar ta wuce kuma sai ya daina ji. A haka bai san lokacin da bacci ya daukeshi ba. ‘Subhanallahi!’ ya fada bayan yayi firgigit ya tashi, ya kai hannunsa ya taba inda yake kwance daidai duwawunsa yaji shi a cikin ruwa sosai. Ya daga hannun yana kallo da tsananan mamaki ‘Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.’ Ya sake fada a fili. to fitsarin kwance yayi ko me? Gashi yaran duk sunyi bacci balle yace wni ne ya zuba masa ruwa; tunda shi dai ya san baya fitsarin kwance. Motsin Shukra da yaji a kusa da shi ne ya tabbatar masa da cewa itace tayi fitsarin, ya mika hannu ya tabata ya jita a jike amma tana ta baccinta hankali kwance. Ya kai hannu zai janye Nasreen daga kusa da ita ya jita itama a jike ‘Tab!’ ya fada a fili. Kenan duka su biyun suke fitsrin kwance ko kuwa yau suka fara? Don shi tunda Khadeeja ta tare a gidan nan sau daya ya taba ji an ce Shukra ta yi fitsari. Ya kalli Afaf wadda ita tana can ta takure a karshen gadon tana baccinta, ya danna wayarsa ya kalli lokaci yaga karfe biyun dare. Ba zai iya tashin yaran nan ba don haka ya lallaba ya sauka daga kan gadon ya fice ya shiga dakin Khadeeja ya samo zanin gado ya zo ya rufe su saboda kar sanyi ya dinga kadasu ga danshi. PAGE 52
🏠