NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 21 of 105

miki, but in ana son wani abu kiyi min magana sai na saka miki kudi a account dinki ko transfer ne sai kiyi musu.’ Ya sa hannu a aljihunsa ya zaro wayarta ya mika mata yana cewa ‘Ga wayarki, ba zan kirawoki ba don kada na dameki ko na tashe daga bacci, but please da kin farka ki kirawo ni.’ Ta karba tana murmushi tana cewa ‘Ok, ka gaishe min da su Yaya Afaf.’ Ya fice ya barta a kwance. Yana fitowa ya sami Anti Iyami da abokan aikinta a station dinsu, yayi mata sallama bayan ta karbi lambar wayarsa sannan ya wuce. ……… Tun a daren Anti Iyami ta kirawo Mommy ta sanar da ita halin da ake ciki, sai dai bata gaya mata cewa Khadeejan tace gida zata taho ba. Ta dai sanar da ita cewa tana hannunta idan akwai wani abu zasu ji zuwa wayewar gari. Tana tsaye aka yiwa Khadeeja wankin ciki sannan aka bata daki, ta saka mata drip da alluranta sannan ta hada mata sahyi mai kauri. Ta sakata a gaba bayan ta shanye sannan ta zuba mata shayi da kwai ta cinye sannan ta ajiye mata saucer da kankana da lemon bawo tace ta shanye kafin a jima. Ta sha tambayoyi a wajen Anti Iyami wadda take kokarin gane dalilin da yasa Khadeejan take son tafiya gida; sai dai bata sami komai ba don da a tunaninta ko Mustaphan yana abusing dinta ne. PAGE 48 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) ita kuma ta sanar da ita kawai bata da lafiya ne sannan kuma ga aikin gida da raino wanda yayi mata yawa shi yasa take son ta je gida ta huta. _______ A gajiye ya shiga gidan wajen karfe tara na dare, yana shiga yaran suka taso da gudu gaba daya tun kafin ya gama rufe kofar motar suba cewa ‘Abba ina Anti Khadeeja?’ Ya dauki shukura ya kana hannun Nasreen yana cewa ‘Tana asibita, likita ya kwantar da ita, amma gobe in sha Allahu zan je na taho da ita.’ Ya tattara su suka shige cikin gidan. Yana shiga bayan Ummi tayi masa sannu da zuwa ya sallameta ya fito ya rakata sai da ta shiga gida ta kirawo masa babanta yayi godiya sannan ya koma gida. Sai da ya biya sallar Magriba da Isha’I duk da yunwar da yake ji sannan ya zo ya zauna a parlor a gajiya, ya dubi Afaf wadda take kwance tana yin game a tab dinta yace ‘Afaf dauko min flask da kayan shayi.’ Ta mike ta shiga kitchen din, jimawa kadan ta futo dauke da kayan shayin bayan ta ajiye tace Abba babu ruwan zafi a flask ka jira na dafa maka, wanda Anti ta zuba mun sha shayi dashi mu da Ummi.’ ‘No, barshi kawai. Dauko min zobo ki kawo min ragowar abincin da kuka ajiye na ci, yunwa nake ji.’ Kafin ta bashi amsa Habib yace ‘Abba ai tun kafin ku fita zobon ya bare a nan, ka manta? Kuma dama shi kenan wanda Anti ta zuba ragowar na jiya ne.’ Kafin yace wani abu Afaf tace ‘Abba babu fa abincin ma sai dai ragowar rice and stew, gaba daya dankalin muka cinye kuma da peppersoup din, amma akwai ragowar watermelon a fridge. Ko na dafa maka indomie?’ Ya kalleta yana shafa kai na dan lokaci, ya ma rasa me zai ce mata sabod yanda gaba daya ya jigata saboda yunwa, coke kawai ya samu a asibiti da wani guntun burodi ya ci. Ya zata zasu rage abincin amma wai duk sun ciye. Muryar Afaf ce ta katse shi tana cewa ‘Bari kawai na dafa maka indomie din Abba.’ ‘No, bari na shiga kitchen din na gani.’ Ya fada yana mikewa tsaye. Ya dan dauki lokaci yana kallon kitchen din bai ma san ta inda zai fara ba; har ya dauki tukunya zai dafa indomie sai kuma ya tuna ai akwai cereal, don haka ya mayar da tukunyar ya ajiyeta a muhallinta. Ya zuba ruwan zafi a kettle ya jona PAGE 49 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ya zuba ruwan zafi a kettle ya tafasa ya hada cereal, ya ajiye ya fiddo kankana daga fridge ya yanka sannan ya dauko ya dawo parlor din. Yana zama Shukra ta matso tana dariya ‘Abba zan sha golden morn din.’ Ya bita da kallo da cokali a hannunsa; bata taba bashi takaici ba kamar a wannan lokacin don ya tabbatar sun koshi tunda gashi sun cinye duk wannan uban abincin da Khadeeja ta dafa. Ya dubi Afaf yace ‘Tashi ki dauko cereal, ki hado min da tea flask da komai na hada mata.’ Kafin Afaf ta dawo Nasreen tace ‘Abba nima zan sha.’ Don haka tana kawowa ya sa ta koma ta karo kofi, ya hada musu cereal din su biyun. Babu wadda ta sha cokali uku a cikinsu, suka tashi suka bar masa a nan. Kafin ya gama cinye nasa abincin duk sun fara gyangyadi don haka ya sa Afaf ta dauko musu kayan baccinsu ya shiryasu bayan ya rakasu sunyi brush sun yi fitsari. Bayan sun kwanta sannan Afaf da Habib suma suka shirya, Afaf ta zauna a gefen gado tayi tsuru-tsuru shima Habib sai ya hau katifarsa ya kwanta yana zare ido. Yana tsaye daga bakin kofa yace ‘Yaya dai Afaf? Ki kwanta mana, ko akwai wata damuwa ne?’ Ta jijjiga kai tace ‘Kawai tunawa nayi da Mommy, itama muna bacci ta mutu.’ Ya gaji sosai ga kansa yana sarawa, babu abinda zai iya yi musu na lallashi, ya bude baki a gajiye yace ‘In sha Allahu babu abinda zai sami Anti, kuyi addu’a ku kwanta kuyi ba
🏠