NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 19 of 105

'To ki yanka mana albasar nan, Rabi slicing za ki yi rabi Kuma ki yanka kanana sai a saka a soup da fried egg.’ PAGE 42 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ta dauki albasar ta wanke ta zuba a chopping board ta fara yankawa. Ba su ji lokacin da Mustapha ya karaso bakin kofar kitchen din ba; a dai-dai lokacin nan wukar da Afaf take yanka albasa ta goce ta Yanke mata hannu. Ta dire albasar ta make murya tana cewa ‘Waiyo Anti na yake.’ Da sauri ta saki abinda yake hannunta ta nufi wajen Afaf din tana murmushi cike da kulawa tana cewa ‘Sorry, garin yaya Afaf. Ki…’ Da sauri ya karasa ya kama hannun Afaf din yana cewa ‘Garin Yaya kika yanke, me ya sa kika dauki wuka?’ Ya juya ya dubi Khadijan yana cewa ‘Na gaya miki sai kin san aikin da Zaki dinga sa yaran nan Amma ke gani kike kamar kawai bana son su taya ki aiki ne. Yaushe Afaf zata iya wani yanka albasa.’ Afaf ta zare hannunta daga nashi hannun ta juya ta wanke a sink, ta dubeshi tace ‘Ya ma daina jinin Abba bari naje na daure.’ Yana juyawa ya dubi Habib wanda yake ta ferayar dankali ya daka masa tsawa ‘Ka ajiye wukar nan ka tashi, namiji da kai kana wani feraye dankali. Tashi ka bani waje.’ Ya juya kan Khadeeja wadda ta riga ta cigaba da aikinta kamar ba da ita yake magana ba, yace ‘Na gaya miki ki daina sa yaran nan aikin da ya fi karfinsu, bana so. Shi Habib ma da yake namiji me ya hadashi da wani harkar girki? Bana so.’ Bai ga alamar zata bashi amsa ba don haka ya juya shima ya fice suka barta ita kadai a kitchen din. Ta rasa me ma zata yi, ta goge fuskarta ta cigaba da aikinta. Haka ta lallaba ta gama komai, zuwa magriba ta zubawa kowa aka sha ruwa. Ta gaji iya gajiya don haka bata ma da kuzarin da zata iya wani musu da shi, ta dai riga ta gama yankewa kanta hukunci da zarar an bude gari zata tafi gidansu ba zata dawo ba sai ta haihu kuma ya dauki mai aiki. ……. A haka aka cigaba da azumi, kullum cikin wannan yanayin Khadeeja take hadawa da hidimar gidan da ta yaran tayi ta fama. Kullum sai ta yiwa Shukra da Nasreen wanka, tsarkin kashi tsarkin fitsari duk ita take musu. Duk wata fitinarsu itace me kulawa. Ga shi tana fama da Shukra wadda sai yanzu ne da suka kwana biyu ta fara hanata kashin wando. PAGE 44 MIJIN MARIGAYIYA A HAUSA NOVEL by Sakina Yazid (Innar su Amal) 'Don Allah kiyi mata a hankali, komai lokaci ne ai zata daina ne a yi mata hakuri.’ Ya fada yana shirin komawa dakin ya yiwo alwala. Ta tsuguna zata dauketa taji kanta ya biyota kamar zai fado, ta dafe goshi ta koma ta tsaye tace ‘Kai! Ba zan iya ba fa.’ Ya juyo ya tsaya ‘Menene?’ ‘Ba zan iya tsugunawa ba fa, jiri kwasa ta yake.’ ta karasa kan kujera ta zauna ta dafe goshi. Ta dubi Afaf tace ‘Bani ruwa na Sha Afaf, ga kiran Sallah nan an fara.’ Nan da nan ta cika Kofi da ruwa ta mika mata, ta Sha kadan ta jingine kanta tana rike da ruwan. Kukan Yusra ne ya katsesu tana cewa ‘Anti na daina ba zan Kuma ba, manatwa nayi daman.' Ta yunkura zata mike Afaf tayi sauri ta dafeta. Abbansu ya dubi Khadija yace ‘Don Allah ki lallaba ki wanke mata kashin nan, Wannan wane irin abu ne? Yanzu wa kike so ya wanke mata kashin?’ Afaf ta aika Nasreen ta dauko fo a toilet ta cire wandon da yake cike da Kashi ta jefe a fo din sannan ta dauke Shukran ta nufi bandaki. Ta wanke mata sannan ta dawo ta gyara wajen, zuwa lokacin Abbansu ya fito daga alwala. Ya zauna ya sha ruwa sannan ya mike zai tafi masallaci. A daidai lokacin itama Khadeeja ta dago kanta ‘A dawo lafiya.’ Yana jinta yayi banza da ita saboda yanda yake jin haushinta, Kuma tabbas sai ya kora mata bayani in an Sha ruwa. Daga yau ma ba zata sake yin azumin ba tunda dama Mai ciki tana da damar ajiyewa. Ta mike tana gatsina fuska, kawai sai gani yayi ta sulale zata fadi. Ya zabura zai tareta yayi fatali da casserole din dankali, a lokaci guda Habib ya saki jug din zobon da ya fito dashi daga kitchen ya tarwatse a wajen ya karasa kanta. Duka su biyun kafin su karaso ta zube. Abbansu ya dago kanta yana jijjigawa ‘Khadeeja, Khadeeja, Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun, Khadeeja.' Ko motsawa bata yi. Ya sunkuceta ya kwantar da ita a kan three seater, ya kara gudun fanka sannan ya kunna AC. Ya cire mata dankwalin da yake kanta ya fara yi mata fifita. Yaran gaba daya suka jeru a kanta suka yi tsuru-tsuru; Afaf ta leka fuskarta ta kafadar Abbansu tace ‘Abban itama mutuwa zata yi ta barmu ko?’ 'Ke bana son rashin hankali, ba wanda zai mutu’ PAGE 45 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) A take yaran suka saka masa kuka mai ban tausayi. Afaf ta rungume Nasreen da Shukra suka hada Kai suna kuka. Habib ya taba shi yace ‘Abba ka Kai ta asibiti kada ta mutu ta barmu.’ 'Kai rufe mana baki.’ Gaba daya Shima ya rude, jikinsa har rawa yake yi. Ya janyo jug din ruwan sanyi ya jika hannunsa ya Shafa mata a fuska. Ta ja numfashi ta bude i
🏠